'Sai da iyayena suka biya dubban daloli kafin ceto ni daga matattu'

Mohammad ya kawashe shekaru biyar a tsare kafin daga bisani aka biya kudi aka sako shi.
Bayanan hoto, Mohammad ya kwashe shekara biyar a tsare kafin daga bisani aka biya kudi aka sako shi.
    • Marubuci, Lina Sinjab
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent

Dubban fursononi ne da ke gidajen yari a Siriya suka ɓace tun bayan da aka fara yaƙin basasa a ƙasar.

Ƴan'uwansu sun shiga tashin hankali, yayin da suka riƙa bayar da maƙudan kuɗaɗe ga jami'an tsaro da masu shiga tsakani da kuma gwamnati domin samun bayanan inda ƴan'uwan nasu suke, sai dai babu wani ci gaba da ake samu kan hakan.

A wani layi da ke kan wani tudu a arewacin birnin Istanbul, wata mata ce ƴar Siriya mai suna Malak, na tuna lokacin da aka kama yaranta maza biyu a shekarar 2012.

Babban cikinsu, Muhammad, yana da shekaru 19 kuma sojan Siriya ne, sai dai an ba shi umarnin harbe wasu masu zanga-zanga a kusa da unguwarsu.

Amma ya tsere saboda kasa aiwatar da umarnin da aka ba shi, yayin da jami'an tsaro suka kama shi kan haka.

Sai yaron nata na biyu Maher shi ma an tsare shi, kawai saboda yayansa ya aikata wancan laifin, kuma an yi awon gaba da shi ne lokacin da yake karatu a makaranta.

Daga wannan lokacin Malak, ba ta sake ganin Mohammad da Maher ba, sai dai ta yi iyakar bakin ƙoƙarinta domin ganin ta gano su amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba.

Saboda haka hanya ɗaya da ta rage mata, ita ce ta rika bayar da maƙudan kuɗaɗe don neman bayanan inda suke.

Malak ba ta sake samun wani bayani kan yaranta ba tun 2014
Bayanan hoto, Malak ba ta sake samun wani bayani kan yaranta ba tun 2014

Ɓatan mutane a Siriya

..

Asalin hoton, ADAM BROOMBERG/THE SYRIA CAMPAIGN

Akwai hasashen da ake cewa hanya ɗaya da ake amfani da ita wajen samun komai a Siriya ita ce ta hanyar bayar da cin hanci, koda kuwa bayanai ake nema na mutanen da suka ɓace ko kuma neman hukumomi su sake su.

Sai dai inda matsalar ta ke, shi ne hakan ba koda yaushe yake aiki ba.

'Na mutu na dawo'

An fara yaƙin basasa a Siriya ne a shekarar 2011, lokacin da ƴan ƙasar da dama suka shiga zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin shugaba Assad, sai dai an far wa masu zanga-zangar lumana tare da kashe su da kuma tsare wasu dubbai.

Mohammad Abdulsalam na ɗaya daga cikin waɗannan masu zanga-zangar da aka tsare lokacin. Jami'in tsaron da ya kama shi ya shaida masa cewa za a yi masa tambayoyi ne na minti biyar kafin a sake shi.

Sai dai an tsare shi a gidan yarin Seydnaya mai nisan kilomita 30 daga arewacin babban birnin ƙasar Damascus.

"An azabtar da ni ta hanya mafi muni da tashin hankali" in ji shi.

Hotunan ƴan Siriya a wajen taron baje kolin waɗanda suka ɓace a Berlin

Asalin hoton, ADAM BROOMBERG/THE SYRIA CAMPAIGN

Bayanan hoto, Hotunan ƴan Siriya a wajen taron baje-kolin waɗanda suka ɓace a Berlin
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai wani lokaci da waɗanda ke tsare da shi suka yi tunanin ya mutu saboda raunukan da ya ji, saboda haka suka ɗauke shi zuwa "ɗakin gishiri", inda ake ajiye waɗanda suka mutu (ana baɗa musu gishiri ne domin kada su yi wari).

Ya ce "A lokacin da na farka, na duba dama da hagu, na fara lalube sai na fara lalubo gawawwaki."

A lokacin da masu gadin gidan yarin suka gane cewa Mohammad bai mutu ba, sai suka fitar da shi daga ɗakin gishiri, inda suka mayar da shi wurin da ake tsare da shi tun farko.

An bai wa iyalan Mohammad takardar shaidar mutuwarsa a 2014, wadda aka rubuta cewa ya mutu saboda bugawar zuciya.

Sai dai mahaifinsa ya ƙi amincewa da hakan, kuma ya ci gaba da neman sa, ta hanyar masu shiga tsakani da ke irin wannan aikin. Ya samu wasu iyalai da ke da alaƙa da shugaba Assad suka kuma amince za su yi aikin.

Ya ce mahaifinsa ya biya dalar Amurka sama da dubu arba'in kafin ya samu a sake shi.

Sai dai, wani abin tashin hankali da tausayi shi ne mahaifinsa ya mutu sakamakon wani hari da aka kai ta sama kafin ganin ɗan nasa, Mohammad.

Gidan yarin Seydnaya.

Babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da kafa cibiya mai zaman kanta da za ta riƙa bibiyar makomar waɗanda suka ɓace a Siriya.

Har ila yau akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu da dama da ke taimaka wa waɗanda iyalansu suka ɓace a Siriya, kamar irin su ƙungiyar waɗanda aka tsare ko suka ɓace a gidan yarin Seydnaya wato Association of Detainees and Missing in Seydnaya Prison (ADMSP).

Riyad Avlar tsohon fursona ne wanda a yanzu yake taimaka wa iyalan da ke neman ƴan uwansu a Siriya.
Bayanan hoto, Riyad Avlar tsohon fursona ne wanda a yanzu yake taimaka wa iyalan da ke neman ƴan uwansu a Siriya.

An kama shi a shekarar 1996, a lokacin yana da shekara 19 da haihuwa, lokacin yana karatu a Siriya. Laifinsa shi ne ya soki gwamnati a cikin wata wasiƙa da ya rubuta wa abokinsa.

Kamar sauran mutanen, shi ma Riyad an neme shi an rasa kuma iyalansa ba su samu labarin inda yake ko halin da yake ciki ba har tsawon shekara 15.

Yanzu shekara shida da sako shi, bayan da ya kwashe shekara 21 a gidan yari.

Ƙungiyar ADMSP ce ta taimaka wa iyalansa wajen samun ƴancinsa daga gidan yarin Sedyana.

"Muna tambayar tsoffin fursunoni, su waye suka tsare su? kuma waɗanne mutane ne suka zauna tare da su? In ji Riyad.

Riyad da abokinsa na amfani da bayanan da suka samu wajen waɗanda aka taɓa tsarewa domin samun bayanan mutanen da ake nema.

Hoton gidan yarin Seydyana wanda ya yi ƙaurin suna a Siriya wanda aka ɗauka daga sama.

Asalin hoton, US DEFENSE DEPARTMENT

Bayanan hoto, Hoton gidan yarin Seydyana wanda ya yi ƙaurin suna a Siriya wanda aka ɗauka daga sama.

Riyad ya yi matuƙar kaɗuwa da yawan kuɗin da iyalai suke kashewa a wajen neman ƴan uwansu. Ya ce wasunsu suna sayar da gidajensu domin biyan kuɗin.

Ƙungiyar ADMSP ta gudanar da wani bincike da kiddigar adadin kuɗin da iyalai ke kashewa wajen neman ƴan uwansu.

Daga shekarar 2011 zuwa 2020 an yi ƙiyasin an kashe dalar Amurka miliyan 900 wajen neman iyalai a Siriya.

Riyad ya haɗa mu da Kadri Ahmad Badle, wanda yanzu haka ke rayuwa a Idlib kuma yake ƙoƙarin neman ɗan'uwansa da aka kama 2013.

Kadri da iyalansa sun bi hanyoyi da dama sun kuma kashe kuɗaɗe da dama wajen neman ɗan uwansu.
Bayanan hoto, Kadri da iyalansa sun bi hanyoyi da dama sun kuma kashe kuɗaɗe da dama wajen neman ɗan uwansu.

Kadri ya ce makwannin da suka gabata, wani ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya fito daga gidan yarin Seydnaya, kuma zai taimaka wajen tantance waɗanda ake tsare da su wajen.

"Mun tuntuɓe shi kuma ya ba mu bayanai masu mahimmanci game da ɗan'uwana, hatta zanen da ke jikinsa sai da ya zayyana mana yadda yake," in ji Kadri.

Tsohon Fursunan ya kuma haɗa su da wani lauya da ya yi musu alkawarin fitar da ɗan uwansu kan dalar Amurka 1,100.

Sai dai bayan sun soma biyan dala 700 sai suka nemi lauyan da tsohon fursunan suka rasa sun kuma rufe wayoyinsu.

Bayan kwana goma, an aika masu da takardar shaidar mutuwar ɗan uwan Kadri, inda aka ce ya mutu tun shekarar 2014 a gidan yarin Seydnaya.

Masu shiga tsakani

Riyad ya ce yawancin masu shiga tsakani da ke nuna za su taimaka, suna aiki da jami'an tsaro ne da hukumomi.

"Kotu za ta iya yanke wa mutum hukunci a Siriya kan wanda ya so wani hoto ko bayanai da aka wallafa a shafukan sada zumunta,"in ji shi.

"Cin hanci da rashawa sun yiwa gwamnatin Siriya dabaibayi don haka kowane mataki na gwamnatin ana iya basu cin hanci."

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin gwamantin Siriya kan wannan labarin, sai dai haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.