Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin juyin mulki Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin na fuskantar barazanar rasa ikonsa a wasu sassan ƙasar, bayan da ƙasar ta shiga cikin wani yanayi na firgici tun bayan da dakarun sojojin hayar kasar na 'Wagner' suka fara ƙwace iko da wasu yankunan ƙasar.
Mista Putin ya zargi shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin da 'cin amanar ƙasar' bayan da dakarunsa suka fara ƙwace iko da wasu garuruwan Rasha.
A nasa ɓangare Mista Prigozhin ya ce ba shi da burin yin juyin mulkin soji, inda ya ce ''gangamin neman adalci'' dakarun nasa ke yi.
Meke faruwa da kungiyar Wagner?
Jagoran Wagner Yevgeny Prigozhin ya taka muhimmiyar rawa a mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, inda ya shafe watanni masu yawa yana ɗaukar dubban mutane aiki a matsayin sojojin haya, musamman daga gidajen yarin Rasha.
A baya-bayan nan ya ɗauki dogon lokaci yana musayar yawu da jagororin sojin Rasha da ke jagorantar yaƙin, lamarin da a yanzu ake ganin ya koma tamkar tawaye.
Dakarun Wagner sun tsallaka daga yankunan gabashin Ukraine da suka mamaye zuwa birnin Rostov-on-Don da ke kudancin Rasha, inda suka ƙwace iko da sansanin sojin Rashan da ke birnin.
Shugaba Putin ya ce ana cikin mawuyacin hali, to amma ya alƙawarta yin duk abin da ya dace wajen kare Rasha.
Shin wannan juyin mulki ne?
Mista Prigozhin ya ce maganar juyin mulki da aka ce suna yunƙurin yi, zance ne marar tushe.
Ana ganin rashin samar wa dakarun Wagner wadatatun kayan aiki da makamai, shi ne ya haifar da abinda ke faruwa yanzu.
Lamarin da ke zama babban ƙalubale ga manyan ƙusoshin gwamnatin Rasha biyu da ke jagorantar yaƙin Ukraine, Ministan tsaro Sergei Shoigu da kuma babban hafsan sojin Rasha Valery Gerasimov.
Kawo yanzu ba juyin mulki ba ne, saboda babu wani yunkuri na ƙwace iko daga gwamnatin ƙasar.
Dakarun sojin hayar ƙarƙashin jagorancin Mista Prigozhin ba sojin gwamnatin Rasha ba ne, duk da cewa yana iƙirarin samun goyon baya daga ƙasashen duniya.
To sai dai wannan yunƙuri ka iya zama ƙalubale ga ƙarfin ikon da Mista Putin ke da shi a ƙasar.
Duk da cewa Putin ne ya bai wa mista Prigozhin dama ya tawagar dakarunsa mai ƙarfin gaske, a yansu a fili take Putin ba shi da wani iko a kansa.
Fadar gwamnatin Rasha na ɗaukar wannan mataki da matuƙa muhimmanci.
A yanzu birnin Moscow na cikin shirin ko-ta-kwana inda dakarun da ke yaƙi da ta'addanci ke sintiri a faɗin birnin, sannan an soke manyan ayyuka masu muhimmanci da aka shirya gudanarwa a yau.
Haka kuma an ɗauki makamancin waɗannan matakai a yankin Voronezh da ke kusa da kan iyakar Ukraine.
Jagoran dakarun sojin hayar na Wagner ya ce yana da mambobi 25,000, "Sannan ƙofa a buɗe take ga duk wanda ke son shigowa cikinmu''.
''Ba mu da niyyar yi wa shugaban ƙasa barazana, sai dai muna yi ne don mu ƙalubalanci shugabannin sojin ƙasar'',in ji shi.
Yayin da yake jagorantar dakarunsa zuwa kan iyakar Rostov, mista Prigozhin ya yi iƙirarin cewar ministan tsaron Rasha da babban hafsan sojin ƙasar sun gudu, bayan da dakarunsa suka mamaye shalkwatar sojin Rasha da ke yankin.
Shugaba Putin ya ce mista Prigozhin ya yi babban kuskure bisa wannan mataki.
Me Prigozhin ke buƙata?
Mista Prigozhin bai bayyana aniyarsa ta yin abin da ya kira ''gangamin neman adalci'' ba, to sai dai rashin jituwar da ke tsakaninsa da jagororin sojin Rasha a fili take, don haka yana son ya kore su.
A wani bidiyo da ke yawo, an ga mista Prigozhin na gaya wa mataimakin ministan tsaron ƙasar da wani babban janar a Rostov ranar Juma'a cewa matuƙar ministan tsaron da babban hafsan sojin ba su zo suka tattauna da shi ba, to dakarunsa za su kulle birnin daga nan kuma Moscow zai nufa.
Mista Prigozhin ya ce jayayyarsa ba da sojojin Rasha da ke yaƙi a Ukraine ba ne, yana faɗa ne da shugabaninsu.
Manyan sojojin ƙasar sun roƙe shi da ya yi haƙuri, to sai dai kamar bakin alƙalami ya bushe.
Yaya alaƙa take tsakanin Putin da Prigozhin?
Prigozhin ya kasance daɗaɗɗen aboki, kuma makusanci ga shugaba Putin, dan haka ya samu dama mai yawa sanadiyyar abotar tasu, da farko ya taso a matsayin hamshaƙin ɗan kasuwa, kafin ya zama shugaban sojojin hayar Rasha.
Ya yi asarar dakaru masu yawan gaske a ƙoƙarinsu na ƙwace iko da birnin Bakhmut da ke gabashin Ukraine da suka ƙwashe watanni suna fafatawa.
Mista Prigozhin bai taɓa fitowa ƙarara ya soki shugaba Putin ba, to amma ana ganin wasu kalamansu na baya-bayan nan a matsayin shaguɓe, ko hannunka-mai sanda ga shugaban.
A farkon wannan wata shugaba Putin ya goyi bayan wani ƙuduri da ministan tsaron ƙasar ya gabatar.
Kudurin ya buƙaci duka dakarun Wagner da ke yaƙi a Ukraine su sanya hannu a kwantiragin aiki da ma'aikatar tsaron ƙasar daga ranar 1 ga watan Yuli.
To sai dai Mista Prigozhin ya yi watsi da matakin, wanda a ganinsa wata ''maƙarƙashiya'' ce ta rage masa ƙarfin iko.
Lokaci mai tsanani ga Putin da Rasha
Prigozhin ya yi barazanar faɗaɗa kwace yankuna daga Rostov zuwa babban birnin ƙasar Moscow, matuƙar ba a biya masa buƙatunsa ba.
A baya dai buƙatun nasa ba su wuce batun ƙarin makamai, da kayan aiki a yaƙin da dakarunsa ke yi a Ukraine ba, to sai dai yanzu buƙatun nasa sun ƙaru, inda yake buƙatar sauke jagororin sojin ƙasar.
Mista Prigozhin ya na da goyon bayan al'umma a Rasha, kuma ko da fafutikar tasa ba ta yi nasara ba, hakan zai kawo rikici ga rundunar sojin ƙasar - wadda ta dogara da mayakansa a yaƙin da ƙasar ke yi a Ukraine.
Haka kuma wannan wani lokaci ne mai tsanani ga shugabancin mista Putin.
Kawo yanzu dai ba a san yaushe rikicin zai ƙare ba.