Ana damuwa kan yawaitar kisan ƴan jarida a rikicin Isra'ila da Falasɗinawa

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Layla Bashar Al-Kloub
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
Tun bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma hare-haren ramuwar-gayya da Isra'ila ke kai wa kan Zirin Gaza, an kashe 'yan jarida aƙalla 29 a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta ta kwamitin kare 'yan jarida (CPJ).
Adadin ƴan jaridar da aka kashe ya haɗa da Falasdinawa 24, da ƴan Isra'ila hudu da kuma ɗan jarida daya ɗan ƙasar Lebanon, daga lokacin harin farko har zuwa ranar 29 ga watan Oktoba. Mun wallafa wasu hotuna da labaransu a ƙasa.
Zirin Gaza

Asalin hoton, Facebook
Doaa Sharaf, 'yar jarida ce ta gidan rediyon Al-Aqsa mai alaƙa da Hamas, an kashe ta a ranar 26 ga watan Oktoba, tare da ɗanta, a wani harin da Isra'ila ta kai a gidanta da ke Yarmouk a birnin Gaza.
Ɗaya daga cikin abokan Doaa ta ce tana da "murmushi mai sanyaya zuciya".

Asalin hoton, Facebook
An kashe Salma Mkhaimer, 'yar jarida mai zaman kanta mai shekaru 31 a ranar 25 ga Oktoba, tare da jaririnta da mahaifinta da mahaifiyarta da kuma wasu 'yan uwa da dama, a wani harin da Isra'ila ta kai a kudancin birnin Rafah. Ta na zaune na a Jordan amma ta koma Gaza don ziyarar iyali ta ba-zata kafin ɓarkewar rikicin.
Muhammad Imad Lobbad, mai shekaru 27, ɗan jarida ne na shafin yaɗa labarai na Al-Resalah, kuma an kashe shi a ranar 23 ga watan Oktoba a wani harin da Isra'ila ta kai a unguwar Sheikh Radwan a birnin Gaza.

Asalin hoton, Facebook
Rushdi Siraj, mai shekara 31, shi ne ya kafa kamfanin Ain Media, wani kamfani na Falasdinwa da ya ƙware kan ayyukan yaɗa labarai.
An kashe shi ne a ranar 23 ga watan Oktoba a wani harin da Isra'ila ta kai a Gaza.
Ya bar mata ɗaya da ɗiya ƴar ƙasa da shekara ɗaya. Abokan aikinsa sun ce: "Mun yi rashin babban mutum amma Rushdi ya koya mana mu ci gaba gudanar da aiki a ko wane irin yanayi."
An kashe Mohammed Ali, ɗan jarida a gidan rediyon Al-Shabab (Youth) a ranar 20 ga watan Oktoba a wani harin da Isra'ila ta kai a arewacin Zirin Gaza.
Ɗaya daga cikin abokan aikin Muhammad ya yi jimami a shafinsa na Facebook: "Mohammed bai taɓa samun saɓani da kowa ba kuma ya kasance abokin aikin ƙwarai wanda kowa ke so."

Asalin hoton, Google
Khalil Abu Atherah wani mai ɗaukar hoto ne na gidan talabijin na Al-Aqsa mai alaƙa da Hamas. An kashe shi tare da ɗan uwansa a ranar 19 ga watan Oktoba a wani harin da Isra'ila ta kai a Rafah da ke kudancin Gaza. Ɗaya daga cikin abokansa ne ya yada hotonsa a Facebook ya ce: “A sauka lafiya Khalil, Allah Ya kiyaye... Ba mu kuma san wanda za mu yi jimami a cikin abokanka ba.”

Asalin hoton, Facebook
Sameeh al-Nadi, mai shekaru 55, ɗan jarida ne kuma darektan gidan talabijin na Al-Aqsa mai alaƙa da Hamas. An kashe shi ne a ranar 18 ga watan Oktoba a wani harin da Isra'ila ta kai a zirin Gaza. Ƴarsa ta ce: “Kawuna, da ma a ce zan iya sake jin muryarka, ina matukar kewar ka.”

Asalin hoton, Facebook
Muhammad Baalousha ɗan jarida ne kuma manajan kuɗi na gidan yaɗa labarai na Palestine Today. An kashe shi tare da iyalansa a ranar 17 ga watan Oktoba a wani harin da Isra'ila ta kai a arewacin Gaza.

Asalin hoton, Instagram
Youssef Dawwas, marubucin jaridar Palastine Chronicle da shirin samari mai zaman kansa We Are Not Numbers (WANN) ne, an kashe shi ne a ranar 14 ga Oktoba a wani farmaki da Isra’ila ta kai a gidan danginsa a garin Beit Lahia a arewacin zirin Gaza. Wani abokinsa ya rubuta a dandalin sada zumunta: “Wani saurayi da kowa ke ƙauna ɗan shekara ashirin. Kowa ya yi tsammanin makoma mai albarka a gare shi nan gaba. Ya na da burin kammala karatunsa na digiri a wajen ƙasar ya kuma dawo."

Asalin hoton, Facebook
An tsinci gawar 'yar jarida mai zaman kanta Salam Mima a ranar 13 ga watan Oktoba, kwanaki uku bayan wani harin da Isra'ila ta kai a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin zirin Gaza, wanda ya kashe dukkan iyalanta. Ta kasance shugabar kwamitin mata 'yan jarida a majalisar 'yan jaridan Falasdinawa. Ta taɓa wallafa hoton ‘ya’yanta guda uku a sakonta na ƙarshe a Facebook. "Su ne tallafi, gida, mafaka, kwanciyar hankali da jin daɗin rayuwa," ta rubuta. "Don haka Ubangiji, Ka kiyaye mun su da idanunka waɗanda ba sa barci."
Isra'ila
Roee Idan, mai shekaru 45, mai ɗaukar hoto na jaridar Isra'ila Ynet, Hamas ta kashe shi a harin da suka kai ranar 7 ga Oktoba, tare da matarsa da 'yarsa. Ɗaya daga cikin abokan aikinsa ya shaida wa kafofin yaɗa labaran Isra'ila cewa Roee "yana ɗaya daga cikin waɗancan 'yan jaridun da ke son kasancewa a fagengudanar da aiki… kuma ya yi nasarar taɓa rayukan mutane da yawa."

Asalin hoton, Facebook
Ayelet Arnin, mai shekaru 22, editan labarai na gidan yaɗa labarai na Isra'ila Kan, Hamas ta kashe ta a ranar 7 ga Oktoba yayin da ta ke halartar bikin kiɗa na Supernova kusa da kan iyaka da Gaza.
Shai Regev, mai shekaru 25, edita ce na TMI, sashen labaran nishaɗi na jaridar Ma’ariv, it ma Hamas ta kashe shi a bikin kiɗa na Supernova. Kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun ce labarinta na karshe ya shafi Bruno Mars, mawakin da ya yi waƙa a Isra’ila kwanaki kaɗan kafin harin Hamas.

Asalin hoton, Facebook
Yaniv Zohar, mai shekaru 54 mai ɗaukar hoto ne na jaridar Isra'ila, Hayom, an kashe shi a ranar 7 ga Oktoba, tare da matarsa da 'ya'yansa mata guda biyu, yayin harin Hamas kan Kibbutz Nahal Oz a kudancin Isra'ila. Wani mai ɗaukar hoto ya ce: "Shi babban mutum ne mai kyakkyawar zuciya."
Lebanon

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An kashe Issam Abdallah, ɗan jaridan bidiyo na kamfanin dillancin labarai na Reuters mazaunin birnin Beirut a kudancin ƙasar Lebanon lokacin da makamai masu linzami da aka harba daga ɓangaren Isra'ila suka tashi da shi tare da jikkata wasu mutane shida. Wasu gungun 'yan jarida na aiki a kusa da Alma al-Shaab, kusa da kan iyakar Isra'ila, inda sojojin Isra'ila da dakarun sa-kai na Hizbullah suka yi musayar wuta a kan iyakar ƙasar. Isra'ila ta ce ana gudanar da bincike kan lamarin.
Haka kuma CPJ tana bin diddigin adadin ‘yan jarida da suka ɓace ko suka jikkata. Ya jaddada cewa 'yan jarida "fararen hula ne da ke yin ayyuka masu mahimmanci" kuma " dole ba ne bangarorin da ke rikici su guji kai masu hari".
"'Yan jarida a duk faɗin yankin suna yin sadaukarwa sosai don kawo rahotanni kan wannan rikici mai ratsa zuciya," in ji Sherif Mansour, mai kula da shirin na CPJ na Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
“Wadanda ke Gaza, musamman, sun sadaukar, kuma suna ci gaba da sadaukarwa, adadin da ba a taɓa gani ba kuma suna fuskantar barazana. Mutane da yawa sun rasa abokan aiki, iyalai, da na'urorin watsa labarai, kuma sun gudu don neman mafaka lokacin da babu mafita ko mafaka."











