Dalilin da ya sa ba a kama shugaban EFCC da na 'yan sanda ba duk da umarnin kotu

Janar Faruk Yahaya da Abdulrasheed Bawa da IGP Usman Akali Baba

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Hafsan Sojan Ƙasa Janar Faruk Yahaya (hagu) da Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa (tsakiya) da Sufeto Janar na 'Yan Sanda IGP Usman Akali Baba

Tun da watan Nuwamba ya kama wasu alƙalan Najeriya suka soma bai wa 'yan kasar mamaki inda suka yanke hukuncin kamawa tare da garƙame shugabannin hukumomin da suka saba kama masu laifi.

A taƙaice dai kotunan sun umarci a kama masu kamawa.

Loƙacin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ba da umarnin kama shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da rashawa, Abdulrabsheed Bawa, 'yan Najeriya sun yi mamaki cewa ta yaya mai dokar barci zai ɓige da gyangyaɗi?

Kafin bakunan mutane su gama rufewa daga mamakin da suka sha, sai ga wani umarnin da kotu ta bayar na kama Sufeto Janar na 'Yan Sanda IGP Usman Alkali Baba.

Bugu da ƙari, shi ma Babban Hafsan Sojan Ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya na fuskantar ɗauri a gidan yari sakamakon umarnin da Babbar Kotun Jihar Neja ta bayar na kama shi.

Sai dai zuwa yanzu babu ɗaya daga cikin mutanen da aka gani cikin ankwa ko kuma a bayan kanta kamar dai yadda kotunan uku suka yi umarni.

Ko me ya sa hakan? Me doka ta tanada game da raina umarnin kotu, ganin cewa kotunan sun kama su ne da raina umarninsu?

Me ya sa aka ba da umarnin kama shugabannin?

Hukunce-hukuncen na zuwa ne a daidai lokacin da laifuka ke ƙaruwa a Najeriya, a gefe guda kuma su ma hukumomi ke cewa suna samun ci gaba a ayyukan daƙile su.

Kotun da ke unguwar Maitama a Abuja ta ba da umarnin kama Abdulrasheed Bawa ne saboda ƙin bin umarninta na farko game da ƙarar da tsohon sojan sama Adeniyi Ojuawo ya shigar da EFCC da kuma gwamnatin tarayya.

Mai Shari'a Chizoba Oji ya ce: "Shugaban EFCC ya raina wannan kotu saboda ƙin cika umarninta na ranar 21 ga watan Uwamban 2018, inda da ta umarci a mayar wa mai ƙara motarsa ƙirar Range Rover da kuɗi naira N40,000,000.00″.

Shi kuwa IGP Alkali Baba, zai sha ɗaurin wata uku ne sakamakon raina umarnin kotun da ta bayar na mayar da wani tsohon ɗan sanda bakin aikinsa.

Mista Patrick Okoli ya shigar da ƙarar ne yana ƙalubalantar IGP game da abin da ya ce an yi masa ritayar dole ba bisa ƙa'ida ba.

"Idan ya ci gaba da saɓa wa umarnin kotun a ƙarshen wata ukun, a ci gba da tsare shi wasu wata ukun har sai ya mutunta umarnin," a cewar Mai Shari'a M. O. Olajuwon.

Sai dai a sanarwar da rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar ta ce babban Sufeton nata bai raina umarnin kotu ba.

A shari'ar da ta umarci kama Janar Faruk Yahaya, Mai Shari'a Halima Abdulmalik ya haɗa da Manjo Janar Stevenson Olugbenga Olabanji a hukuncin.

Alƙalin ya ce ya ba da umarnin kama su ne saboda sun raina kotu game da ƙarar da aka shigar gabanta.

Me ya sa ba a kama su ba har yanzu?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Laifukan da kotunan suka kama shugaban 'yan sanda da na hukumar EFCC ba a ƙarƙashin IGP Usman Baba da Abdulrasheed Bawa aka aikata su ba. Yayin da aka aikata na 'yan sanda a 2011, an aikata na EFCC ne a 2018.

Masana shari'a a Najeriya na sun bayyana dalilai biyu da suke hana a kama mutum a irin wannan umarni da kotu kan bayar.

Ɗaya daga cikin waɗannan dalilai shi ne ɗaukaka ƙara.

"Kamar yadda shari'a ta tanada, duk hukuncin da kotu ta yi, ko da bisa kuskure ne, dole a yi biyayya gare shi amma wanda bai gamsu da shi ba yana da damar ɗaukaka ƙara kuma ya nemi a tsagaita aiwatar da hukuncin," a cewar babban lauyan Najeriya Ishaq Magaji mai muƙamin SAN.

Dalili na biyu kuma shi ne yadda wasu kotunan ke yanke hukunci bisa kuskure sakamakon rufa-rufa da wasu ke yi musu a shari'o'in da suka gabatar a gabansu.

"Idan muka ɗauki shari'ar Abdulrasheed Bawa misali, kotun da ta ba da umarnin a kama shi ita ce kuma ta jingine hukuncin saboda ta yi shi bisa kuskure," kamar yadda Ishaq Magaji SAN ya bayyana.

"Hakan ta faru ne saboda an yi mata rufa-rufa a shari'ar, abin da ba a faɗa mata shi ne cewa EFCC ta ɗaukaka ƙara. Daga baya an faɗa mata cewa ba ta da masaniya kan abin da ya wakana a baya."

'Ci gaba ne aka samu'

Babban lauyan ya ce irin waɗannan hukunce-hukunce da ake gani a yanzu ci gaba ne da aka samu a tsakanin al'umma ta yadda mutane ke ƙoƙarin neman haƙƙinsu.

"Misali, mutum ne ya kai ƙara an kore shi daga aiki, kotu ta ce a mayar da shi aikinsa amma aiwatar da hukuncin yana kan shugaban 'yan sandan, saboda rashin aiwatar da hukuncin sai ya koma kotu ya ce ba a mayar da shi ba," in ji Ishaq Magaji SAN.

"Wannan dalilin ne ya sa kotu ta hukunta IGP tun da alhakin mayar da shi yana kan sa.

"A fahimtata ci gaba ne da ake samu na mutane da suka fahimci bin kadinsu da kuma bibiya."