An sayi tsohuwar wayar iPhone kusan naira miliyan 32

Karen Green ta fara mallakar IPhone a 2007, amma sai ta yi wani abu da mutane da dama ba su yi ba – ba ta buɗe ta ba kwata-kwata.

Wayar Iphone din ta farko a lokacinta, an yi gwanjonta kan dalar Amurka $63,356.40 a ranar Lahadi, kwatankwacin naira miliyan talatin da ɗaya a farashin hukuma.

Farashin ya wuce tunaninta, a zatonta ba za ta wuce $50,000. Ya ninka da kusan kashi 100 na ainihin farashin wayar mai ƙarfin ajiye bayanai 8GB na $599.

Amma kada ka zaci tsohuwar wayarka za ta yi wannan darajar, sai dai idan har yanzu tana cikin kwalinta na ainihi kamar yadda aka ƙriƙireta a kamfani.

“Samun irin wannan waya ta ainihi, kuma kashin farko na wayoyin da aka ƙera a 2007, tana maƙale a jikin ainihin kwalinta da tambarin kamfani, wannan ba ƙaramin abin birgewa ba ne, in ji Mark Montero na kamfanin LCG da suka yi bajakolin wayar.

Kamfanin LCG da ya yi gwanjon wayar, ya buɗe damar yin bajakolin ne da dalar Amurka 2,500 a ranar 2 ga watan Fabarairu, aka rufe a ranar Lahadi bayan mutum 27 sun taya ta.

Wani aboki ne ya bai wa Ms Green kyautar wayar a 2007, bayan ta samu sabon aiki, kamar yadda ta bayyana a wata tattaunawa da aka yi da ita a 2019. A lokacin ta riga ta sayi wata sabuwar waya da kuɗinta don haka ta ajiye wadda aka ba ta kyautar.

“Iphone ce, har yanzu ba ta tsufa ba”.

Masu amfani da IPhone an sansu da fidda kuɗi su sayi sabuwar wayar da ta fito duk tsadar ta. A bara, an sayar da wata kwamfuyutar Apple da aka ƙera tun ta 1970 kan $677,000.

An samu irin wannan wayar ta farko ita ma da aka sayar kan $35,414 a watan Agusta sai wata da aka sayar a watan Oktoba ita ma kan $39,339.

Ms Green ta shaida wa mujallar Business Insider cewa ya kamata ta ƙara riƙe wayar zuwa wani lokaci domin ta ƙara tsada, amma tana buƙatar wasu kuɗaɗe domin ta fara kasuwanci.