Ko zai yiwu a koyar da 'yan firamare da harshen uwa a Najeriya duk da ƙabilu 600 na ƙasar?

Hukumomi a Najeriya na son harsunan uwa su maye gurbin Ingilishi wanda ake koyar da 'yan firamare da shi a yanzu. Amma ta yaya za a iya yin hakan a ƙasar da ake magana da harsuna fiye da 600?

Kareem Abiodun Habeebullah, wanda Bayerabe ne, an taɓa zane shi lokacin da yake ɗalibin sakandare saboda ya yi magana da Yarabanci maimakon turancin Ingilishi.

"Na sha fama da Ingilishi lokacin da nake ƙarami," kamar yadda ya faɗa wa BBC. A cewarsa game da abin da ya faru a 2010, akwai wani lokaci da wata malama ta kira sunansa don ya ba da amsa amma sai ya kakare.

"Na san amsar amma da Yarabanci kawai zan iya faɗa," in ji shi. Sai malamar ta ce ba zai yiwu ba, ya zo inda yake kuma ya fara tsula masa bulala.

"Ta tsula min bulala ɗaya," kuma ta yi wa Habeebullah tsawa cewa yin magana da harshen uwa ba na Ingilishi haramun ne, a cewarsa.

Ba shi kaɗai ya shafa ba, sauran ɗalibai a makarantu sun fuskanci wannan matsalar saboda sun yi magana da Yarabanci a madadin Ingilishi.

Fiye da shekara 60 da Najeriya ta samu 'yancin kanta daga Turawan Mulkin Mallakar Birtaniya, har yanzu Ingilishi ne harshen hukuma inda ake amfani da shi a al'amuran yau da kullum da makarantu da harkokin gwamnati da ma wuraren aiki da yawa.

Sai dai a watan Nuwamba lamari ya fara sauyawa, inda Ministan Ilimi Adamu Adamu ya sanar da Tsarin Harshe na Ƙasa da ya sharɗanta cewa a koyar da 'yan firamare da harshensu na uwa, maimakon Ingilishi.

Ya ce sauyin ya zama dole saboda yara sun fi saurin fahimta idan aka koyar da su da harshen uwa.

Akasari akan koyar da yara da Ingilishi a Najeriya, inda a wasu lokutan ake haɗa turancin da harsunan uwa don a sauƙaƙa wa ɗalibai.

Sai dai kuma ba a san yadda za a iya aiwatar da sabon tsarin ba saboda - a ƙasar da gwamnati ta yi ƙiyasin ana amfani da harshe 625 da kuma yadda mutane ke sauya wuraren zama a ƙasar - yara da yawa na zaune a wuraren da harshensu na uwa ba shi da rinjaye.

Hasali ma, sai a shekarun 1970 aka fara gabatar da ƙudirin koyar da yara a harshen uwa, amma saboda wahalar aiwatarwa a ƙasar ba a iya fara aiki da shi ba kamar yadda gwamnati ke son yi a yanzu.

Tuni aka fara nuna adawa da tsarin. Duk da abin da ya fuskanta, Habeebullah wanda yanzu malamin makaranta ne, yana ganin ba wani abu ne mai kyau ba koyar da yara cikin harshen uwa.

"Idan ka duba Najeriya a matsayin ƙasa, muna da harshe fiye da 500, abin da zai sa a sha wuya" wajen aiwatar da tsarin.

A ajin da yake koyarwa da ke Sabongidda-Ora a kudancin Jihar Edo, ana magana da harshe biyar daban-daban, in ji shi - akwai Hausa, da Ibo, da Yorubam, da Ora, da kuma Esan.

Duk da cewa da turanci yake koyarwa, wani zubin dole sai ya haɗa da turancin buroka (Pidgin English) don kowa da kowa ya gane.

"Babu wani amfani a koyar da su abin da ba za su iya ganewa ba, kuskure ne babba."

'An makara'

Akasarin masu rufin asiri a Najeriya, musamman a kudancin ƙasar, Ingilishi ya zama harshensu na uwa kuma da yawa ba sa ma yin magana da kowane harshe na cikin gida.

Tayo Adeyemo mai shekara 46 kuma mazaunin Legas, na ganin koyar da 'yan firamare cikin harshen uwa ba zai yiwu ba.

Harshen mutanen Legas shi ne Yarabanci, amma saboda shi ne birnin kasuwancin ƙasar mutane da yawada ke magana da wasu harsunan sun koma can da zama.

"Ba na jin abu ne mai kyau," kamar yadda uban ɗaliba mai shekara tara ya faɗa wa BBC.

"An daɗe ana magana da Ingilishi tsawon shekaru. Na yi amfani da shi a firamare shekaru da yawa da suka wuce. Saboda haka, kawo wannan tsarin ba zai yiwu ba a yanzu."

A yanzu abin kamar yana da amfani saboda yadda gwamnnatin Najeriya "ke ƙoƙarin daow da ɗabi'ar" magana da harsunan uwa, in ji Mista Adeyemo.

Duk da cewa yana son 'yarsa ta dinga magana da Yarabanci, yana ganin "an makara" a yanzu.

'Daƙile yaran'

Duk da haka, a wurin yaran da ba su iya Ingilishi ba a gida, idan aka koyar da su da harshen da ba su iya ba tun suna ƙanana zai lalata rayuwar koyon karatunsu.

Wani ƙwararre kan harsunan uwa a Bankin Duniya, Dr Olatunde Adekola, ya faɗa wa BBC cewa tsarin koyarwar na yanzu "yana daƙile yara".

A cewarsa, wasu iyaye na ƙorafin cewa 'ya'yansu ba sa koyo cikin sauri a makarantu, kuma hakan na da alaƙa da tsarin da ake bi na amfani da Ingilishi wajen koyar da su.

"Idan harshen da yara ke amfani da shi a gida ya sha bamban da na makaranta, zai jawo ruɗani da kuma nesanta yaro da karatu."

Shi ma Minista Adamu Adamu ya faɗa yayin sanarwar cewa akwai ƙalubale wajen aiwatar da tsarin. Ya ce "za a buƙaci jajircewa mai yawa wajen samar da kayan aiki da kuma ɗaukar malamai" da ke da ƙwarewa a harsunan.

Ya ce duk harshen da za a yi amfani da shi a kowace makaranta sai ya zama na mutanen da ke zaune a wurin da makarantar take.

"Muna da harshe 625 a ƙididdigar da aka yi ta ƙarshe kuma muradin wannan tsari shi ne ingantawa da ƙarfafa gwiwar amfani da harsunan Najeriya," a cewarsa.

Ba iya manyan harsunan Najeriya uku za a yi amfani da su ba (Hausa, Yarabanci, Ibo), da zarar an fara amfani da tsarin za a koyar cikin ɗaruruwan harsunan da ake magana da su a ƙasar.

Ƙarin bayani daga Olivia Ndubuisi da ke Legas