Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan bukukuwan Gasar Kamun Kifin Argungu ta 2026
Dubban mutane ne suka halarci bukukuwan gasar kamun kifin Argungu ta 2026 da aka shirya a jihar Kebbi.
Gasar wadda ake yi shekara-shekara an jima ba a yi ba saboda dalilai na tsaro.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne babban baƙon da ga buɗe gasar kamun kifin da aka gudanar a yau Asabar.
Ministar al'adu da yawon buɗe idanu, Hannatu Musawa tare da ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu
Gwamonin Gombe da Jigawa na daga cikin gwamnonin ƙasar da dama da suka halarci bikin
Gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu ne ya ƙaddamar da gasar tseren motoci a lokacin bukukuwan
Gasar tseren motoci na daga cikin wasannin da ake gudanarwa a lokacin bukukuwan gasar
Manyan sarakuna da dama ne suka halarci gasar
Kafin gasar kamun kifin ta yau an shafe tsawon kwanaki ana gudanar da wasanni daban-daban.
Daga cikin wasannin da aka gudanar har da tseren jakuna da dawaki da kuma raƙuma
Masunta masu yawa ne suka fafata a gasar kamun kifin da aka gudanar ranar Asabar
Dubban asunta ne suka fafata gasar kamun kifin ta bana
Abubakar Usman daga ƙaramar hukumar Maiyama na jihar Kebbi ne ya lashe gasar kamun kfin ta bana
Kifin da ya kama na da nauyin kilogiram 59, kamar yadda alƙalan gasar suka bayyana
Ya samu kyautar motoci biyu da kuɗi naira miliyan ɗaya, daga masu shirya gasar.