Tomahawk: Makamin da Rasha ke fargabar Amurka za ta iya bai wa Ukraine

A missile in flight with flame coming out of its jet exhaust

Asalin hoton, Mark Wilson/Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Lokacin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky zai gana da shugaban Amurka Donald Trump a ranar Juma'ar, akwai yiwuwar cewa batun makamai masu linzami zai zamo ɗaya daga cikin manyan batutuwan da za a tattauna.

A baya-bayan nan shugaba Trump ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya amince da buƙatar Zelensky na ganin an bai wa Ukraine miyagun makamai.

Shugaban na Ukraine ya sha nanata buƙatar samun tallafin soji mai ƙarfi ta yadda ƙasar za ta iya mayar wa Rasha martani, kuma yana sa ran jin labari mai daɗi a lokacin wannan ganawa, a ziyara ta uku da zai kai Amurka tun daga watan Janairu.

Akwai rahotannin da ke cewa a baya-bayan nan Ukraine ta yi amfani da makamanta masu cin dogon zango, wadanda ake kira 'Flamingo', to amma tana ganin har yanzu tana buƙatar makamin 'Tomahawk' domin samun nasara kan Rahsa.

Me ya sa wannan makami mallakin Amurka ke da muhimmanci haka kuma me ya sa Amurka ta ƙi bai wa Ukraine tuntuni?

Me ya sa ake son makamin Tomahawks?

Tun bayan samamen da Rasha ta ƙaddamar kan Ukraine a 2022, Ukraine ta riƙa miƙa ƙoƙon bararta na samun makamai masu cin dogon zango, yayin da take tunanin yanke shawarar kai hare-hare a biranen da ke da nisa a cikin Rasha.

Tun a baya Rasha ta gargaɗi Amurka daga bai wa Ukraine makamai masu cin dogon zango, inda ta ce bai wa Ukraine makamin zai haifar da ƙazancewar yaƙin da kuma lalata alƙar da ke tsakanin Amurka da Rasha.

Wasu daga cikin makamai masu linzami samfurin Tomahawk da Amurka ta taɓa harbawa a baya kan iya cin zangon kilomita 2,500, wanda hakan ke nufin za su iya kaiwa birnin Moscow cikin sauƙi daga cikin Ukraine.

Duk da cewa makamin Tomahawk ba ya gudu kamar walƙiya, to amma suna tafiya ne a ƙasa-ƙasa, lamarin da ke sanyawa suke da wahalar ganowa da kuma kakkaɓowa.

Kuma suna da saiti sosai, ta yadda za su iya faɗawa daidai inda aka tura su, in ji wakilin BBC a harkar tsaro Pavel Aksenov.

Sai dai wani ƙalubale game da bai wa Ukraine makaman Tomahawk shi ne hanyar da ake bi wajen harba su.

Bisa tsari Tomahawk makami ne da ake harbawa daga teku, kuma jiragen ruwa da jirage masu tafiya ƙarƙashin ruwa ne ke dakon shi. A halin yanzu Ukraine ba ta da irin jiragen ruwan da za su iya harba makamin.

A baya-bayan nan Amurka ta tura wa Ukraine gudumawar turakun harba makamai asu linzami, to amma dakarun Ukraine na buƙatar samun horo sosai kafin su iya amfani da su.

Trump puts his arm around Zelensky while they stand in front of flags of their respective countries.

Asalin hoton, Alex Wong/Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Ukraine na ta sintiri zuwa Amurka domin neman ƙarin tallafin makamai

Abin da Amurka za ta iya bayarwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yin amfani da irin wannan makami mai cin dogon zango ba tare da kuskure ba na buƙatar bayanan sirri masu inganci daga Amurka.

Dogaron da Ukraine take yi da Amurka wajen samun bayanan da take buƙata domin kai hare-hare ya fito fili ne a watan Maris, lokacin da Amurka ta ɗan dakatar da samar wa Ukraine bayanai.

Sai dai jaridar Financial Times ta ruwaito cewa tun daga wancan lokacin Amurka ta ƙara ƙaimi wajen samar wa Ukraine bayanai, inda bayanan da take samarwa suka taimaka wa Ukraine wajen kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi na Rasha, har da matatun man fetur.

Jami'an da suke da masaniya kan yadda abin ke faruwa sun ce, bayanan siriin Amurka na taimaka wa Ukraine wajen sanin hanya da nisa da lokaci da kuma dabarar da za a yi amfani da ita wajen kai harin.

Hakan ya taimaka wa jirage marasa matuƙa na Ukraine zulle wa shingen kariya daga hare-hare na Rasha.

Masana na ganin cewa idan har aka bai wa Ukraine makaman Tomahawk, to za a yi amfani da ƙwararrun sojojin Amurka wajen shiryawa da kuma tsara hanyoyin kai harin.

A yanzu haka Amurka na da tarin makaman Tomahawk, amma yaƙin Ukraine ya nuna cewa rikici da ƙasa mai ƙarfin soji sosai na buƙatar makamai masu ɗimbin yawa.

Ganin yadda Amurka ke fargabar ɓarkewar rikici tsakaninta da China, zai yi wahala Amurkar ta bai wa Ukraine tarin makaman da take bukata da za su sauya akalar rikicinta da Rasha ta hanyar lalata cibiyoyin sojinta.

Vladimir Putin da Volodimyr Zelensky

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai masana sun ce, makamai masu linzami da aka tura wa Ukraine waɗanda aka yi amfani da su tare da wasu makaman, za su iya taimakawa wajen sauya akalar yakin.

Dabarar da Rasha ta yi amfani da ita ta nuna hakan, ta hanyar amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare kan Ukraine.

Hare-haren da Ukraine ta kai kan matatun man fetur na Rasha a baya-bayan nan sun haifar da damuwa ga tattalin arziƙin Rasha, amfani da makaman Tomahawk za su iya taimakawa wajen ƙara matsi kan Rashar.

Yadda abubuwa ke sauyawa

A Tomahawk Land Attack Missile is launched from a US missile cruiser

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, MakamanTomahawk za su ƙara wa Ukraine ƙarfin kai hari zuwa wurare masu nisa a cikin Rasha

Ran shugaban Amurka Donald Trump ya ɓaci a watannin baya-bayan nan bayan nuna gajiya kan rashin hadin kan Vladimir Putin wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Ukraine.

"Akwai yiwuwar zan faɗa musu (Rasha) cewa idan ba a tsayar da yaƙin ba, za mu iya (tura wa Ukraine makamin Tomahawk), kila kuma ba za mu tura ba, ƙila kuma mu tura," kamar yadda ya faɗa a ranar Lahadi.

"Za su (Rasha) so a harba musu Tomahawk? Ba na tunanin za su so hakan," in ji shugaban na Amurka.

Rasha ta mayar da martani da kakkausan kalamai.

Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar Rasha Dmitry Peskov ya ce magana kan makamin Tomahawk "abu ne mai tsanani."

"Yanzu lokaci ne mai ban mamaki ganin yadda kowane ɓangare ke ƙara ɗaukar zafi," in ji shi.

A watan Satumba Peskov ya yi watsi da batun amfani da makaman Tomahawk, inda ya ce ba za su "iya sauya akalar" yakin ba.

Hoton da ke bayani kan tsarin makami mai linzami na Tomahawk da yadda yake aiki
Bayanan hoto, Hoton da ke bayani kan tsarin makami mai linzami na Tomahawk da yadda yake aiki

A wayar da suka yi ta baya-bayan nan, Zelensky da Trump sun tattauna yunkurin Ukraine na ƙarfafa sojinta, ciki har da ƙarfafa garkuwarta daga hare-hare ta sama da kuma amfani da makamai masu cin dogon zango.

Manyan biranen Ukraine kamar Kyiv na ci gaba da shan luguden wuta daga Rasha ta hanyar amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa.

Musamman ma yadda Rasha ke kai hari kan cibiyoyin makamashi na Ukraine yayin da yanayin tsananin sanyi ke matsowa, lamarin da ke haifar da katsewar lantarki.

A watan da ya gabata, jakadan shugaba Trump na musamman a Amurka, Keith Kellog ya yi bayanin da ke alamta cewa shugaban Amurka ya amince da kai hari kan wurare masu nisa a cikin Rasha.

Ƙarin bayani daga Harry Sekulich, Laura Gozzi, Sashen labaran BBC na Rasha da kuma sashen BBC Global Journalism.