Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Donald Trump ke ɗasawa da Kim Jong Un?
- Marubuci, Sangmi Han
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Korean
- Aiko rahoto daga, Seoul
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ba zai gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ba a lokacin ziyarar da yake yi a yankin Asia, inda ya kafa hujja da "rashin tsayar da lokaci".
Kwana daya kafin isar Donald Trump ƙasar Koriya ta Kudu domin taron ƙasashen duniya na Apec, Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani makaminta mai linzami a gaɓar yammacin ƙasar.
A farkon wannan mako Trump ya ce zai "so ya hadu" da Kim, inda ya yi tayin sake zuwa ƙasar Koriya ta Arewar.
Yau kimanin shekara shida tun bayan da Donald Trump ya kafa tarihin zama shugaban Amurka na farko da ya shiga Koriya ta Arewa.
Tsakanin shekarun 2018 da 2019, a lokacin wa'adinsa na farko, ya gana da Shugaba Kim Jong Un har sau uku.
To sai dai yanzu ba a sani ba, ko har yanzu shugabannin biyu na zantawa da juna kan batun ƙasashensu.
Amurka ta ci gaba da jaddada matsayinta kan hana bazuwar makaman nukiliya a yankin Koriya, amma Shugaba Kim, wanda ya ƙi amincewa ƙasarsa ta dakatar da ƙera makaman nukiliyar - ya yi watsi da matakin Amurkan a matsayin ''matakin'' da ya kamata ƙasashen Yamma su yi watsi da su.
Sannan shi kansa Trump ya yarda cewa abu ne mawuyaci ci gaba da alaƙa da ƙasar da ke sirrinta ala'muranta.
"Tabbas, ina ganin za su iya shiga ƙasashe masu karfin nukiliya,'' kamar yadda ya bayana ranar 24 ga watan Oktoba, ''Suna da makaman nukiliya masu yawa, amma kuma ba su da sabis din waya mai yawa'', in ji Shugaba Trump.
Alkwai dai ƙaruwar raɗe-raɗin yiwuwar ganawa tsakanin shugabannin biyu.
Akwai yiwuwar cewa Amurka za ta ci gaba da alaƙa da Koriya ta Arewa duk da cewa Trump da Kim ba za su gana ba a wannan karo, in ji wasu masharhanta.
Abu ne ƙarara cewa Donald Trump, wanda ke kallon kansa a matsayin jakadan zaman lafiya na duniya, burinsa shi ne ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel.
A farkon wannan mako Donald Trump ya ziyarci Malaysia, domin ganin yadda za a sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Thailand da Cambodia, inda nan ne zangonsa na farko a ziyarar da yake yi a nahiyar Asiya.
A watan Yuli ƙasashen biyu sun gwabza faɗa mafi muni cikin shekaru 10, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.
Bayan haka ne Trump ya yi iƙirarin cewa ya kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe takwas.
"Akwai buƙatar ganin an samu zaman lafiya a yankin Korea, inda nan ne abubuwa suka fi zafi a arewa maso gabashin Asia, daidaita dangantaka tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa da kuma warware taƙaddamar makaman nukiliyar ƙasar," in ji Kim Jae-chun, wani farfesan harkokin ƙasashen duniya a Jami'ar Sogang.
Koriya ta Arewa ta ƙara ƙarfi tun bayan ganawar Trump da Kim a 2019
"Gwamnatin Koriya ta Arewa ta shiga yanayin daidaito," in ji farfesa Kang In-deok na Jami'ar Kyungnam, wanda ya riƙa muƙamin ministan hadin kai na Koriya ta Arewa a shekarun 1990.
A watan Satumban 2025 an ga hoton Kim na ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin da na China Xi Jingping a lokacin bikin baje kolin makaman yaƙin China a wani ɓangare na bikin tunawa da cika shekara 80 na cin galaba a kan Japan a yaƙin duniya na biyu.
Wannan ne karo na farko da aka ga shugabannin uku a tare.
Koriya ta Arewa ta ƙarfafa hulɗar tsaronta da Rasha. A bara ƙasashen biyu waɗanda ƙasashen yamma suka ƙaƙaba wa takunkumai sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa, inda suka amince "nan take su samar wa juna tallafin soji ta kowace hanya."
A watan Janairun 2025, jami'an ƙasashen Yamma sun shaida wa BBC cewa Koriya ta Arewa ta tura kimanin sojoji 11,000 domin taya Rasha yaƙi a Ukraine, ita kuma Koriya ta Arewa za ta samu tallafi na fasaha da kuma kuɗaɗe.
Haka nan kuma alaƙar tattalin arziƙi da ke tsakanin Koriya ta Arewa da China na ƙara ƙarfi, inda kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ya ƙaru da kashi 33%, ya kai dala biliyan 1.05 a rubu'i na farko na 2025, kamar yadda alƙaluman hukumar shige da fice na China suka nuna.
To amma wasu masanan na ganin ba lallai ne ganawar shugabanin biyu ta samu ba, saboda zai yi wahala Kim ya samu abin da yake so.
"Gwamnatin Koriya ta Arewa ta shiga lokacin daidaituwar al'amura,'' a cewar Farfesa Kang In-deok, na Jami'ar Kyungnam , wanda ya kasance tsohon ministan haɗewar Koriya a shekarun 1990
Baya ga ganawa da Putin da Xi Jinping a China - bayyanarsu ta farko a bainar jama'a tare da kuma matakin diflomasiyya na farko da Kim ya ɗauka tun bayan da ya hau mulki, a shekarar 2011 - shugaban na Koriya ta Arewa ya ƙulla kawancen soja da Rasha.
Ƙasashen biyu da ke fuskantar takunkuman ƙasashen duniya na ƙulla ƙawance mai karfi a 2024, ciki har da amincewa da ''samar da taimakon soji tsakaninsu idan buƙatar hakan ta taso''.
A Janairun 2025, wasu jami'an ƙasashen Yamma sun faɗa wa BBC cewa Koriya ta Arewa ta aike da sojoji aƙalla 11,000 domin taimaka wa Rasha yaƙi a Ukraine.
Yayin da ita kuma Rasha za ta samar mata da taimakon kuɗi da fasahar zamani.
Haka kuma alaƙar tattalin arzikinta da China na ƙara ƙarfafa, yayain da ƙiyasin kasuwancin da ke tsakaninsu ya kai dala biliyan 1.05 a farkon wata shidan shekarar 2025, kamar yadda alƙaluman kasuwancin China suka nuna.