Arsenal na son Rodrygo, Liverpool na zawarcin Fofana, akwai yiwuwar Diaz ya koma Barca

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na neman dan wasan gaba na Real Madrid Rodrygo, Barcelona na zawarcin dan wasan gefe na Liverpool Luis Diaz, Chelsea ta kuduri aniyar ci gaba da rike Enzo Fernandez duk da alakanta shi da Real Madrid.
Arsenal na zawarcin dan wasan gaban Brazil Rodrygo, mai shekara 24, wanda zai iya barin Real Madrid a bana. (Sky Germany)
Ana sa ran dan wasan Bayer Leverkusen Florian Wirtz zai zabi tsakanin komawa Bayern Munich da Liverpool nan da kwanaki 10 masu zuwa, inda kungiyoyin biyu ke zawarcin dan wasan na Jamus mai shekaru 22. (Kicker)
Barcelona na son dauko dan wasan Liverpool dan kasar Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, wanda sauran shekaru biyu ya rage a kwantaraginsa a Anfield. (ESPN)
Liverpool na son dan wasan gaban Lyon da Belgium Malick Fofana mai shekaru 20 a matsayin wanda zai maye gurbin Diaz idan ya tashi (Mundo Deportivo)
Napoli da Chicago Fire ne ke kan gaba wajen zawarcin dan wasan tsakiyar Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33, wanda zai bar Manchester City a kyauta a bana. (Talksport)
Dan wasan tsakiya na Manchester City James McAtee zai iya komawa Bayer Leverkusen, kana akwai kungiyoyin Premier da dama da ke neman dan kasar Ingilan mai shekaru 22. (Sky Germany)
Chelsea ta kuduri aniyar rike dan wasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez, duk da cewa dan wasan mai shekaru 24 yana cikin jerin sunayen wadanda Real Madrid ke zawarci a bana. (Guardian)
Shugaban Fiorentina Rocco Commisso na shirin ganawa da dan wasan gaban kungiyar dan Italiya Moise Kean domin kokarin shawo kansa ya ci gaba da zama a kungiyar, duk da neman da kungiyoyi da dama ke masa. (Football Italia)
Viktor Gyokeres ya shaida wa takwarorinsa na Sporting cewa ba shi da tabbacin inda zai taka leda a badi, inda ake alakanta dan wasan gaban dan Sweden mai shekara 26 da Arsenal da Manchester United. (KCanal 11)











