Cunha zai koma United, Liverpool ta ƙarfafa bayanta, an yi wa Wirtz farashi

Matheus Cunha

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan gaba na Wolves, Matheus Cunha zai koma taka leda a ƙungiyar Manchester United a ƙarshen kaka mai zuwa, inda ake sa ran darajar ɗan wasan na Brazil mai shekara 25 ta kai sama da fam miliyan 62. (Sky Sports)

Manchester United ta tattauna da ɗan wasan Ingila da ke taka leda a Ipswich Town Liam Delap, 22. (The Athletic)

A ranar Litinin ne ɗan wasan baya na Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong, 24, ya kammala gwajin lafiya da Liverpool, bayan nan ne mai tsaron gida na Netherlands zai koma Birtaniya a ranar Lahadi mai zuwa. (Sky Sports)

Aston Villa na son golan Ireland mai taka leda a Liverpool, Caoimhin Kelleher, 26, da ɗan wasan Argentina, Emiliano Martinez, 32, za su bar Villa a karshen kakar nan. (The Sun)

An gano Manchester United,da Barcelona da ƙungiyoyin Pro League na Saudiyya na bibiyar lamarin Martinez. (The Sun)

Bayer Leverkusen ta yi wa ɗan wasan tsakiya na Jamus Florian Wirtz, 22, darajar fam miliyan 126, daidai lokacin da ƙungiyoyin Bayern Munich da Liverpool ke zawarcinsa bayan janyewar da Manchester City ta yi daga son ɗaukar dan wasan. (The Times - subscription required)

Dan wasan tsakiya na Ingila, Angel Gomes, 24, ya sanar da zai bar ƙungiyar Lile da yake taka wa leda a ƙarshen kakar nan inda kwantirginsa ya kare, tuni ƙungiyoyin Tottenham, West Ham da Manchester United suka fara kyalla ido kan dan wasan (The Sun)

Marseille ta ce ba ta son saida dan wasan gaba na Manchester United, Mason Greenwood, 23, amma ƙarshenta dole ta yi hakan sakamakon rashin tabbas ɗin tattalin arzikinta. (RMC Sport)

Sunderland na son ɗaukar mai tsaron gida na Mali da ke taka leda a Montpellier, Modibo Sagnan, 26 ko da ba su kai bantensu a Premier League a wasan da ya rage musu na Championship. (Sunderland Echo)