Man City ta shiga cikin masu neman Kerkez, Barca ta cimma matsaya kan Raphinha

Raphinha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Raphinha
Lokacin karatu: Minti 2

Newcastle na cikin kungiyoyin da ke shirin tattaunawa da Liam Delap, amma Manchester United ce ke kan gaba wajen sayen dan wasan Ipswich, Manchester City za ta fafata da Liverpool don neman dan wasan baya na Bournemouth Milos Kerkez.

Newcastle United na cikin kungiyoyin da ke shirin tattaunawa da dan wasan Ipswich Town dan kasar Ingila Liam Deap mai shekaru 22 a wannan makon. (Talksport)

Manchester United ce ke jagorantar fafatukar sayen Deap amma rashin nasara a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai da kuma rashin ba shi damar buga wasan Turai a kakar wasa mai zuwa zai baiwa Chelsea dama fiye da kowa. (ESPN)

Manchester City za ta fafata da Liverpool don siyan dan wasan Bournemouth mai shekara 21 da kuma dan bayan Hungary Milos Kerkez. (i paper)

Brighton ta amince da yarjejeniyar daukar dan wasan bayan Faransa Olivier Boscagli mai shekaru 27a kyauta daga PSV Eindhoven. (Sky Sports)

Liverpool ta karbi tayi daga kungiyoyin Saudiyya kan dan wasan gaban Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 25, dan wasan Portugal Diogo Jota da dan wasan Colombia Luis Diaz, dukkansu 28. (Sky Germany)

Manchester United tana fatan za su iya zawarcin dan wasan Sporting da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26 a bazara. (L'Equipe )

Aston Villa ba za ta tursasa wa golanta dan Argentina Emiliano Martinez, mai shekara 32, idan har ta tabbata yana son barin Villa Park. (Givemesport)

An fahimci cewa Chelsea ta fara tattaunawa da Ajax kan yuwuwar cinikin dan wasan bayan Netherlands Jorrel Hato, mai shekara 19, wanda Liverpool da Arsenal ke zawarcinsa. (Caughtoffside)

Barcelona ta cimma yarjejeniya da dan wasan Brazil Raphinha kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da zama a kulob din har zuwa watan Yunin 2028. (Fabrizio Romano)

Kocin Nottingham Forest Nuno Espirito Santo na iya barin kungiyar a karshen kakar wasa ta bana saboda rikicin cikin gida a kungiyar. (Footmercato)

Leicester City na shirin korar kocinta Ruud van Nistelrooy kuma tana ci gaba da tattaunawa domin nada tsohon kocin Southampton Russell Martin. (Football Insider)