Rashford zai rage albashi don komawa Barcelona, Sane zai bar Bayern

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rashford
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Manchester United, Marcus Rashford, 27, da ke zaman aro a Aston Villa, ya amince a rage ma sa albashi domin ya samu komawa taka leda kungiyar Barcelona a kaka mai zuwa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tun da fari Barcelona na son daukar Rashford a matsayin aro daga Manchester United, amma ta na fatan sayan dan wasan nan gaba kadan idan ciniki ya kaya. (Sport - in Spanish)

Mai tsaron baya na Poland kuma dan wasan Arsenal, Jakub Kiwior, 25, na samun zawarawa ciki har da Napoli, sai dai kulub din na Serie A na son Gunners su sassauta farashin fam miliyan 30 da suka sanya kan dan wasan. (Calciomercato - in Italian)

Manchester City na shirin kashe fam miliyan 180 kan kwantiragi biyu na dan wasan Jamus da ke taka leda Bayer Leverkusen, Florian Wirtz, 22, da dan wasan tsakiya na Netherlands mai taka leda a AC Milan Tijjani Reijnders, 26. (Mirror)

Manchester United ba za ta kori manaja Ruben Amorim, ko da kuwa ba su kai bantensu a wasan karshe na cin kofin Nahiyar Turai da za su kara da kungiyar Tottenham. (Mirror)

AC Milan ta yi watsi da tayin sama da fam miliyan 50 da Manchester City kan dan wasanta Reijnders. (Teamtalk)

Dan wasan Netherlands mai taka leda a Bayer Leverkusen, Jeremie Frimpong, 24, inda suka amince da kwantiragin shekara 5 da Liverpool. (Talksport)

Dan wasan Jamus Leroy Sane, 29, ya yi watsi da tayin kwantiragin da Bayern Munich daidai lokacin da ake rade-radin kungiyoyin Premier League da La Liga, na zawarcinsa. ( Sky Germany - in German)

Da alama mai tsaron ragar Aston Villa, Emiliano Martinez, zai bar kulub din sakamakon yadda dan wasan na Argentina mai shekara 32 ke samun goron gayyata daga kungiyoyi da dama ciki har da kulub din Saudiyya da kuma wasu biyu na Turai. (Mundo Albiceleste - in Spanish)

Martinez da iyalansa sun samu matsuguni a Birmingham, amma ya na bukatar yin gaba idan har ya na son daukar karin kofuna.(Ole - in Spanish)