Celtic ta ɗauki Premier na Scotland karo na 12 cikin shekara 13

Asalin hoton, PA
Celtic ta lashe kofin Premier na ƙasar Scotland karo na 12 cikin shekara 13 bayan nasarar caskara Kilmarnock 5-0 ranar Laraba.
Kociya Brendan Rodgers da tawagarsa sun je filin wasa na Rugby Park ne da sanin cewa maki ɗaya ya ishe su su ci gaba da mamaye gasar.
Karo na uku kenan da Celtic ta lashe kofin na Scotish Premier League.
Ƙwallo biyun da Celtic ta ci cikin minti 12 da take wasa ne suka kwantar wa da magoya bayanta hankali.
Zaƙaƙurin ɗan wasa Matt O'Riley, wanda shi ne ɗan wasan Celtic mafi hazaƙa a kakar bana - shi ne ya bugo ƙwallo daga gefen turke kafin Adam Idah ya cilla ta raga, sai kuma Daizen Maeda da ya ƙara wata.
Zuwa minti na 35 ta zama 3-0 bayan Maeda ya bai wa James Forrest ƙwallo kuma ya jefa ta raga.
O'Riley ya ci wata ƙayatacciyar ƙwallo daga wajen yadi na 18 kafin ya ci ta biyar kuma ta 18 da ya ci a kakar bana.






