Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kamfanin AstraZeneca ya janye allurar rigakafinsa ta Corona
- Marubuci, James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
Bayan yin amfani da fiye da biliyan uku na allurar rigakafin, kamfanin Oxford-AstraZeneca ya janye allurar daga kasuwa.
Kamfanin na AstraZeneca ya ce "yana matuƙar alfahari" da allurar rigakafin amma kuma dole ce ta sa ta ɗauki matakin.
Ta ce ƙarin nau'ikan cutukan Corona na nufin yanzu ana buƙatar sabbin nau'ikan allurar.
An ƙididdige cewar allurar ta taiamaka wajen kare rayukan mutane miliyoyi a lokacin annobar duk da cewa ta haddasa wasu 'yan ƙanana kuma taƙaitattun cutukan toshewar kafofin jini da suka yi sanadiyyar rasa rayuka.
An samar da allurar rigakafin ne a daidai lokacin da duniya ta fuskanci annobar Corona wani abu da ya tilasta masana kimiyya a jami'ar Oxford suka ƙirƙiri rigakafin a ƙanƙanen lokaci. Sun cimma samar da allurar a watanni 10 maimakon yadda aka saba samar da ita a tsawon shekaru 10.
A watan Nuwamban 2020, rigakafin "ta zama ta duniya baki ɗaya" kasancewar ta fi sauƙin farashi da kuma ajiya fiye da sauran rigakafin na Corona. Kamfanin magaungunan na AstraZeneca ya amince ya samar da mai yawa.
Tunda farko dai, yana cikin tsarin Burtaniya yi wa jama'ar ƙasar rigakafin a tsawon lokacin da annobar ta kwashe.
"Gaskiyar batu dai shi ne ta allurar ta AstraZeneca tare da ta Pfizer ta matuƙar samar da banbanci, kuma ita ce wadda ta fitar da mu daga annobar da ke bazuwa a wannan lokaci." In ji Farfesa Adam Finn daga jami'ar University of Bristol.
To sai dai ƙimar allurar rigakafin ta AstraZeneca ta samu tawaya saboda matsalolin toshewar ƙofofin jini da ka ɗan rinƙa samu wani abu da ya sa Burtaniya ta koma wa wasu nau'ikan na allurar rigakafin daban daga AstraZeneca.
A wata sanarwa, AstraZeneca ya ce "bisa ƙididdiga mai zaman kanta, allurar ta tseratar da rayukan fiye da mutum miliyan 6.5 a shekarar farko ta amfani da allurar.
"Gwamnatoci a duniya sun yaba da ƙoƙarinmu kuma an alaƙanta allurar tamu da ɗaya daga cikin dalilan da suka sa duniya ta shawo kan annobar Corona."
Sanarwar ta ƙara da cewa cigaba da ake samu na ƙirƙiro sabbin allurar rigakafi domin dacewa da ƙarin nau'ikan cutar ta Corona, da ke yawo shi ne "babban dalilin" da ya sa "buƙatar ta yi ƙasa" ta allurar ta AstraZeneca wadda ba a yin sabuwa".
Farfesa Finn ya ƙara da cewa "Ina tunanin janye allurar na nufin ba a buƙatar allurar.
"Abin da ke faruwa shi ne wannan ƙwayar cutar na saurin yaɗuwa kuma tana bujire wa allurar rigakafin saboda haka allurar ta zama marar amfani kuma abin da hakan ke nufi shi ne sabuwar nau'in allurar ce kawai za ta kasance a kasuwa."