Zamfara: Yadda hare-haren ƴan bindiga suka raba al'ummar garuruwa 40 da gidajensu

.

Asalin hoton, ABDULMALIK MAIBIREDI

Al'ummar Gundumar Rijiya wadda ta ƙunshi garuruwa da ƙauyuka fiye da 40 a yankin ƙaramar hukumar Gusau da ke Zamfara a arewacin Najeriya suna ta gudun hijira zuwa garin Gusau, babban birnin jihar.

Hakan ya faru ne sakamakon hare-haren ƴan bindiga da suka addabi yankin, tun daga makwanni biyu da suka gabata.

Hare-haren ƴan bindigan dai sun hana jama'ar gundumar ta Rajiya sakat a ɗan tsakanin nan har abin ya tilasta wa da dama yin gudun hijira, a cewar wani mutumin yankin, wanda ya nemi BBC ta sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro.

Ya ce halin da suke ciki a yanzu duk sun fice daga garuruwansu sama da 40, saboda yadda ƴan bindigar suka uzzura musu da hare-haren da suka jefa rayuwarsu cikin ƙunci, "mun koma cikin Gusau, ko masauki ba mu samu ba."

Ya bayyana cewa wasu daga cikin garuruwan sun haɗa da Gidan Doka, da Gidan Kada, da Tsakuwa, da Gabachawa, da Baya Wuri, da Ruwa Kusa, da A gama Lafiya.

Majiyar ta ƙara da cewa akwai gawarwaki da dama yashe cikin daji, "muna son ma'aikata su taimaka mana mu je mu binne su."

A cewarsa, ƴan bindigar suna shiga garuruwansu kan babura suna harbi tare da buge mutane.

"Bayan sun zo sun ɗaukar mana mata sati biyu da suka wuce, suka kawo mana hari na baya-baya ranar Laraba, sun kashe mana mutum ashirin ranar Laraba ɗin nan,"

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Alhamis suka sake shigowa suka kashe mana mutane da dama, ba mu san adadinsu ba, gawarwaki - wasu suna daji, mun ɗauko wasu mun yi musu jana'iza, amma wasu tsakani na da Allah suna daji ba mu ɗauko su ba, muna jin tsoron komawa wajen da aka yi abin, yanzu mun samu gawa 11 a hannunmu."

Ya kuma shaida wa BBC cewa ta'adin da ƴan bindigar suka yi wa garuruwansu ba zai misaltu ba, "saboda a taƙaice an basu kuɗi ya fi miliyan 100 kuma ba su bari ba."

Ya bayyana cewa ƴan bindigar sun kashe sama da mutum 40, "yanzu akwai mata namu 25 a hannunsu, kuma mun rasa inda suka kai su."

Mun tuntubi SP Muhammad Shehu, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar ta Zamfara, dangane da wannan lamari amma har ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoto ba mu ji daga gare shi ba.

Sai dai wata majiya ta shaida mana cewa, an tura sojoji da manya makamai wannan yanki da ke da iyaka da ƙungurmin daji da tsaunuka, inda bayanai suka ce ta nan ƴan bindiga ke shiga suna kai hare-hare wasu sassa na yankunan ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe a jihar ta Zamfara.