Ƙasar Musulmi da ke son shiga jerin mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a duniya

    • Marubuci, Hanna Samosir da Nicky Widadio
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen BBC Indonesia, Jakarta da Nusantara

Mafi yawan ma'auratan da suke masu ƙananan shekaru na son yin ritaya lokacin da ya dace, amma Musmulyadi mai shekara 55 da Nurmis matarsa mai shekara 50 na son saɓa wannan al’ada.

Sun shafe tafiyar kilomita sama da dubu domin gudun hijira a sabon babban birnin Indonesia, wanda ke haɓɓaka cikin gaggawa.

"A nan ana saurin samun aikin yi, saboda yanzu ake gina garin," in ji Musmulyadi, kamar yadda ya shaida wa BBC.

Yanzu yake gini a yankin Nusantra, kamar yadda ake kiran yankin Borneo mai cike da tsuburi da yaran Javan.

Nurmis na cakuɗa ciminti yayin da Musmulyadi na sanya tayel.

Burinsu shi ne burin Indonesia - Musmulyadi na fatan kama ƙasa a aikinsa sannan ya zama babban ɗan kwangila a wannan gagarumin aikin.

Tun bayan lokacin da Shugaban kasar Joko Widodo wanda ake kira da Jokowi ya sanar da gina Nusantra shekaru biyu da suka gabata, al'amuran kasuwanci ke ci gaba da haskakawa.

Wani aiki da gwamnati ke yi a birnin da ake sa ran mutum miliyan biyu su zauna cikin shi nan da shekara 2029.

Amma gwamman kilomita nesa da nan, Pandi mai shekara 51 da matarsa Symsiah na cikin damuwar kada a kore su daga inda suke.

Sun fito ne daga ɗaya daga cikin kaɓilu 20,000 da ke yankin, kuma ba su da shaidar mallakar ƙasar, inda danginsa suke zaune na gwamman shekaru.

Pandi ya tashi wata rana da safe ya ga an cefanar da ƙauyensu, ba tare da an ba su wani wa'adin tashi ba.

Gwamnati ta so rushe ƙauyensu domin kare ambaliyar ruwa, sai dai a watan Fabarairu Pandi ya dakatar da hakan sanadiyyar ƙarar da ya shigar a kotu.

"Wannan yaƙi ne nake yi domin 'ya'yanmu da jikokinmu masu zuwa," ya shaida wa BBC.

"Idan na gaza yin komai, ‘yayana da jikokina za su zama ba su da wata daraja a wajen gwamnati. Don haka muke yaƙi da rashin adalci."

Wannan wani ɗan wurin zama ne ga mutanen ƙauyenmu na wani ɗan lokaci, domin tuni aka tashi wasu ƙauyukan da suke gabanmu, bayan gwamnati ta biya su kudaden fansa, amma ba su kai sun kawo ba.

Labarin Pandi da na Mulyadi ya nuna yadda aikin na Shugaba Widodo ke da fuska biyu mai dadi da mara dadi, matsa wa wasu, da kuma samar da aiki ga wasu.

Shiga jerin ƙasashe biyar masu karfin tattalin arziƙi

A cewar alƙaluman Asusun Bayar da Lamani na Duniya IMF, Indonesia ce ƙasa ta 10 da 'yan ƙasar ke da ikon sayan abubuwan da suke so a duniya, lokacin da ya ci mulki a karon farko a 2014.

Shekara 10 bayan nan, matsayin Indonesia ya koma na bakwai, tana bayan China da Amurka da India da Japan d Jamus da kuma Rasha.

Nan da 2027, ƙasar da ta fi yawan Musulmai a cikinta a duniya, tana neman zarce Rasha ta ƙarfin tattalin arziki.

Ƙasar da ke Kudu maso Gabashin Asia ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 14 ga watan Fabarairu, inda alƙaluman da ba na gwamnati ba suka nuna ministan tsaro Prabowo Subianto na kan nasarar lashe zaɓen a zagayen farko.

Ya yi alƙawarin ci gaba da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar kamar yadda shugaban yanzu yake yi, kuma ɗan gidan Shugaba Widodo, Gibran Rakabuming Raka, ne ɗaya ɗan takarar.

Kasar na da gagarumin buri na son ta zama cikin ƙasashe biyar masu ƙarfin tattalin arziƙi nan da 2045, lokacin da za ta cika shekara 100 da samun 'yancin kai.

Domin cimma wannan buri sai tattalin arziƙin ƙasar ya rika bunkasa da kashi 6 zuwa 7 kowace shekara.

An dauki hanyar haka domin a yanzu yana ƙaruwa ne da kashi 5.

‘Dutsen Nickel’

Indonesia ta yi suna da tsibirinta na Bali da ake zuwa hutu, amma bayan haka tana da ma'adanin wani ƙarfe mai matuƙar yawa, wanda ake haɗa batiran mota da shi.

Lokacin da shugaba Widodo ya sanar da haramta fitar da dutsen Nickel a 2019, sai da Tarayyar Turai ta kai Indonesia ƙara gaban Cibiyar Kasuwanci ta Duniya.

Shugaban ya ce yana so ya habbaka yadda ake samar da dutsen a Indonesia.

Wata takarda da wata ƙungiya da ke bincike mai zaman kanta ta fitar, Cibiyar da ke Nazari kan Ci gaban tattalin arziki ta ce sabon tsarin da ya fito da shi kan Nickel ya samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arziki.

Idonesia ta dogara kacokan kan masu zuba jari daga China domin gina wajen aikin Neckel ɗin.

Shugaba Widodo ya sha suka kan yadda ya bai wa China dama domin zuba jari, yayin da ya manta da abin da zai iya faruwa na lalata ƙasar da kuma matsalar lafiya da za a iya fuskanta da kuma matsalar muhalli da aikin zai haifar.

Fatan gina tsuburi?

An tayar da hankali lokacin da shugaba Widodo ya sanya hannu kan sabuwar dokar mayar da babban birnin wani wuri a 2022, yayin da ƙasar take ta fama da Korona.

Kasashe da dama irin su China sun nuna muradin zuba jari a sabon birnin, sai dai babu wani abu mai kwari da aka fara tattaunawa yanzu.

Shugaban ƙasar ya jarraba hanyoyi da dama wajen ganin burin ƙasar ya cika, ciki har da wata doka domin taimaka wa masu zuba jari, wadda ƙungiyoyin masu kare dan’adam suka cewa hakan take haƙƙin ɗan’adam ne.

A cewar rahotanni zai miƙa iko ne a watan Oktoba, kuma za a riƙa kallon wannan katafaren aiki na Nusantara a matsayin bajintarsa.