Birtaniya za ta mayar wa Zimbabwe ƙoƙon kawunan waɗanda suka bijire mata a ƙarni na 19

Gidan tarihin Jami'ar Cambridge na Natural History Museum da ke London ya ce a shirye yake ya haɗa hannu da Zimbabwe domin mayar da rage-ragen mutanen da aka dauka zuwa kasar a lokacin mulkin mallaka.

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan wani wakilci daga Zimbabwe ya tattauna da jami'ai daga ɓangarorin biyu.

Zimbabwe na so a ba ta ƙoƙon kan jaruman da suka yi yaƙi da mulkin mallaka a ƙarni na 19, wanda suka yi amannar suna Birtaniya.

Amma har yanzu ba a kai ga gano su ba.

Hukumomin Zimbabwe sun dade suna zargin cewa akwai sauran jikkunan shugabannin da suka nuna adawa da mulkin mallakar Birtaniya a shekarun 1890 - waɗanda ake kira ( First Chimurenga) - waɗanda turawan Birtaniya suka kwashe a matsayin alamun nasarar da suka samu.

Mafi mahimmanci a cikinsu ita ce wata mata wadda aka fi sani da Mbuya Nehanda. An kashe ta ne a Harare babban birnin ƙasar, ana dai yi mata kallon gwarzuwa a ƙasar.

Lokacin da aka duba wasu daga cikin kayan tarihinta, gidan tarihin Natural History Museum ya gano wasu abubuwa 11 "da bincike ya nuna asalinsu daga Zimbabwe suke" - sai dai kuma ba su da alaƙa da Nehanda.

Ciki har da ƙoƙunan kai uku da aka ɗauka a 1893, daga birnin na biyu a Zimbabwe, Bulawayo, da kuma wasu sauran abubuwa da ba a kai ga ganowa ba a wani wagegen rami da aka yi wanda daga baya shi ma aka kai su Birtaniyan.

Ɗakin gwaji na Jami'ar Cambridge da ake kira Duckworth ya ce "akwai wani ƙaramin abu na mutane daga Zimbabwe", amma cikin sanarwar da ta aike wa BBC ta ce ba ta kai ga tantance ko ɗaya daga ciki ba, kan cewa na mutanen da suka yi adawa ne da mulkin mallaka.

Gidan tarihin ya gano sassan jikin ɗan adam 25,000, kuma ɗakin gwaji na Duckworth na da 18,000, cikinsu har da manyan kayan tarihi na duniya.

An tattaro wannan bayani ne daga majoyoyi daban-daban ciki har da wani shafi na bankaɗo ababen tarihin mutanen farko, amma a wurin wasu ana boye asalin irin waɗannan abubuwa cikin lokaci.

A zamanin shugabancin turawan mulkin mallaka, a lokuta da dama akan kwashe sassan mutane daga filin yaƙi a matsayin alamar nasara ko kuma a ajiye su domin binciken fasaha.

A ƙarnin na 19, ƙwararru a fannin sanin girma da kuma girman ƙwaƙwalwar ɗan adam waɗanda suka yi binciken kan halayyar mutane na da alaƙa da yanayin girman ƙoƙon kan shi, abu ne da yake sananne a Birtaniya da wasu ɓangarori na turai.

Masanan na karɓar kokon kai domin taimakawa wajen samun bayanai, wanda a gaba yake ƙarewa wajen banbance launin mutane.

Wasu masu bincike sun nuna yadda girman ƙoƙon kai ke nuna banbancin mutane da kuma ta wanne ɓangaren duniya suka fito.

Wasu daga cikin kayayyakin tarihin da ake da su a Birtaniya gamayya ce da abin da masana daga hukumomi suka samu da kuma waɗanda cibiyoyi masu zaman kansu suka samu.

Gwamnatin Zimbabwe ta yi amannar cewa ko ta yaya ne ƙoƙon kawunan jarumansu na cikin kayayyakin tarihin da ke Birtaniya.

Manyan cikinsu sune shugabanin addinai, ciki har da Charwe Nyakasikana, wadda ake kira Mbuya (kakar Nehanda) wadda ake ganin ta jininta Nehanda ta gaji gwagwarmaya.

An kama ta tare da zargin cewa ta kashe wani jami'in Birtaniya.

Daga nan aka rataye Nehanda aka kuma naɗe jikinta da sarka, abin kuma da ya faru daga nan babu wanda ya sani, amma a ƴan shekarun nan, Jami'an Zimbabwe sun ta fitar da sanarwa cewa gidan tarihin nan aka kai ta.

Da kukan mutuwa "za a ƙara tashin jikina", Nehanda ta zama wata alama ta masu yaki da mulkin farar fata wanda ake kira da (Rhodesia) a ƙarshen shekarun 1960. A shekarar 1980 e Zimbabwe ta samu 'yan cin kanta.

Wani mutumin Nehanda da aka yi, mai tsayin mita uku an kafa shi a tsakiyar babban titin da ke tsakiyar Harare.

A lokacin ƙaddamar da shi a 2021, Shugaba Emmerson Mnangagwa ya nemi a ci gaba da kiraye-kirayen dawo da ƙoƙon kan nata da na sauran waɗanda ke gidan tarihin.

A wurin mutanen Zimbabwe idan aka cire wa mutum kai "na nufin ka hukunta mutum sama da yadda ake yi a kabari", in ji Godfrey Mahaci, wanda ya jagoranci wakilcin mutanen Zimbabwe zuwa Burtaniya ya shaida wa BBC a 2020. "Idan aka raba kan da jikin yana nufin ruhin zai ci gaba da gararamba ba zai taba samun salama ba".