Ana nuna mana wariya a Najeriya - Masu addinin gargajiya

- Marubuci, Tunde Ososanya
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
Masu addinin gargajiya a Afirka sun nuna ɓacin ransu kan nuna masu banbanci da suka ce gwamnati ke yi wajen rashin nuna an san da su musamman a wajen ware ranakun hutu a ƙasar.
Wani daga cikin masu bautar addinin gargajiyar, Oluwo Olawole Olakunle, ya shaida wa BBC cewa mutane na nuna musu wariya a duk lokacin da aka san abin da suke bauta wa.
"Yanayin kallon da mutane ke yi mana idan mun ce mu ƴan gargajiya ne, sai ka ce mun kashe mutum, ko kuma kana ƙoƙarin kashe wani,"in ji Olawole.
Oluwo Olawole ya ce mutane suna kiransu da matsafa, su ma kuma sun yarda suna tsafin, amman sun ce irin tsafin da suke shi ne na neman biyan wata buƙata.
"Idan manya suka ce suna son hutu, to za su samu ba tare da ɓata lokaci ba, amman ban da mu saboda ba a ɗauke mu bakin komai ba," In ji Oluwo.
Sun ce suna fuskantar ƙalubale da wariya da ake nuna musu har wajen aikin gwamnati.
Ƴan gargajiyar sun ce, ko a asibitoci idan sun je jikin kati da ake bayarwa akwai bayanin addinin marar lafiya, amman daga Musulunci sai kuma Kiristanci.
"Waye ya isa ya ce Ifa ba za su iya fitar da yadda tsarin tattalin arziƙin Najeriya zai kasance ba?
"Waye ya gaya muku ba za mu iya faɗin abin da zai faru nan da shekaru hamsin masu zuwa ba? In ji ɗan gargajiyar.
Wani shi ma ɗan gargajiyar, Oluwo Jogbodo Orunmila, ya ce akwai wuraren da ba zai iya shiga ba a garin da yake saboda kawai yana addinin gargajiya.


Ya shaida wa BBC cewa ana nuna wa 'ya'yansu banbanci a makarantu.
"Duk lokacin da 'ya'yanmu suka rataya duwatsun da muke sakawa na addini sai a tilasta su su cire, amma Musulmai suna saka hijabi kuma Kiristoci na saka alamar gicciye, duk ba a hana su."
"A makarantu ana sanya 'ya'yanmu suna addu'a ta Kiristoci ko a ce sai sun ce Allahu Akbar, amma idan za su yi waƙar addininmu ba a ba su dama. Kuma muna ƙasar da babu ruwanta da addini," in ji Oluwo Jogbodo.
Masu addinin gargajiyar sun ce ko bankuna suka je ana yin biris da su kuma a gabansu ake kula wasu mutanen har sai sun jima suna jira.
"Mutane suna iya yin da'awarsu tsawon kwana 17 ko 21. Musulmai suna zuwa masallacin Juma'a kuma suna sallah sau biyar a rana, amma idan boka ya ce zai yi addininsa na gargajiya sai a lakaɗa masa duka, ko kuma su riƙa tambayarka lafiya?" in ji Oluwo Jogbodo.
Shin me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce game da addini?

Wata lauya a Najeriya ta ce sashi na 38 ƙaramin sashe na huɗu na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi bai wa kowa ne ɗan ƙasa damar yin tunani da kuma yin addinin da duk yake so.
Barista Gladys Eyongndi ta ce hakan yana nufin kowa ne ɗan Najeriya na da damar zaɓen addinin da duk yake so ya yi.
"Babu wata doka da ta ce dole sai ka kasance Musulmi ko Kirista," in ji Barista Gladys Eyongndi.














