'Ina jin raɗaɗi idan na ga maza kawai suna zuwa makaranta ban da mu'

"Kowacce rana ina tashi ne da burin ganin na koma makaranta. Taliban sun yi ta faɗin cewa za su buɗe makarantu. Amma yanzu ga shi har shekara biyu babu wani labari.
Ban yarda da su ba. Ina jin takacin hakan,'' in ji Habiba ƴar shekara 17
Ta kasance tana cizon yatsunta saboda da takaici.
Habiba tare da ƙawayenta Mahtab da Tamana na cikn dubban yara mata da Taliban ta haramta musu zuwa makaranta - ƙasa ɗaya tilo da ta ɗauki irin wannan mataki.
Shekara ɗaya da rabi bayan faruwar lamarin, an katse musu rayuwa, inda har yanzu suke ci gaba da nuna takaici.
Fara zangon karatu
Ƴan matan na fargabar cewa damuwar da duniya ta nuna a kansu na raguwa, duk da cewa kullum suna rayuwa cikin takaicin abin da ya faru - lamarin ya ƙara yi musu ciwo a makon nan ganin an shiga sabon zangon karatu ba tare da su.
"Idan na ga maza na tafiya makaranta da kuma yin duk abin da suke so, hakan yana min zafi. Bana jin daɗi. Idan na ga ɗan uwana na tafiya makaranta, sai na rasa mai yake min dadi,'' in ji Tamana.
Hawaye ne ke zuba a idonta yayin da take magana.
"Tun da farko, ɗan'uwana ya sha cewa ba zai tafi makaranta, ba tare da ni ba. Na faɗa masa cewa ya yi hakuri ya tafi zan zo daga baya.
"Mutane sun faɗa wa iyayena cewa kada su damu, suna da ɗa namiji. Ina ma a ce muna da damammaki iri ɗaya."

Duk wani fata da suke da shi na ganin an sake buɗe makarantu yana ƙara dusashewa saboda ƙarin takunkumai da gwamnatin Taliban ke saka wa mata.
"Akwai ɗan walwala da farko, amma sannu a hankali hakan na sauyawa,'' in ji Habiba.
Takunkumin farko da aka sanya kan makarantun sakandire, ya zo ne a watan Disamban 2021, lokacin da Taliban ta ba da umarnin cewa idan mata za su yi tafiyar da ta kai nisan kilomita 72, to sai sun samu muharrami.
A watan Maris ɗin 2022, gwamnatin Taliban ta sanar da cewa za a sake buɗe makarantun sakandire na mata, amma za a rufe su bayan ƴan sa'o'i.
Dokar sanya tufafi
Kasa da watanni biyu baya, an zartar da wata doka da ta bayyana cewa mata za su sanya tufafin da zai rufe musu jiki gaba-ɗaya, ciki har da ƙaramin himar.
A watan Nuwamba, an haramta wa mata da ƴan mata zuwa wuraren shaƙatawa da motsa jiki da kuma wuraren ninƙaya. An kuma daina bai wa ƴan mata damar zaɓar darussan tattalin arziki da fannin injiniya da kuma jarida a jami'o'i.
Wata ɗaya bayan nan, an shiga ruɗani lokacin da aka dakatar da mata daga zuwa jami'o'i da haramta musu yin aikatau da kuma aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasashen waje ban da ɓangaren lafiya.

"Idan aka ci gaba da sa irin waɗannan takunkumai, ba na ganin rayuwa tana da wani muhimmanci ga mata. Ba mu da damar samun haƙƙoƙinmu kamar sauran mutane.
Rayuwa ba ta da muhimmanci idan babu ilimi. Ina ganin mutuwa tafiye min da irin wannan rayuwa da muke ciki,'' in ji Mahtab.
Mahtab ta ji rauni a wani harin bam da aka kai kan wata makaranta mai suna Sayed UI-Shuhada a watan Mayun 2021, lokacin da Taliban ke faɗa da dakarun gwamnatin da ta gabata a Afghanistan.
"Na samu raunuka a wuyana da fuskata da kuma tafin kafa. Suna yi min zafi. Amma ina da zimmar ci gaba da karatu,'' in ji Mahtab. "Na kuma samu damar rubuta jarrabawa ta tsakiyar zango, amma bayan zuwan Taliban, sai komai ya taɓarɓare."
'Muhalli mai kyau'
Taliban ta ce ta rufe makarantu da jami'o'i ne ga mata da ƴan mata na ɗan wani lokaci har sai an samu "yanayi mai kyau".
Akwai hujjoji da ke nuna an samu rarrabuwar kai a tsakanin gwamnatin Taliban kan wannan lamari, sai dai duk wani ƙoƙari da wasu masu ganin ƴan matan sun cancanci a bar su, su je makaranta, suka yi, abin ya ci tura.
Dangane da wasu takunkumai, Taliban ta ce ta ƙaƙaba su ne saboda mata ba sa sanya hijabi da ke rufe duk sassan jikinsu ko kuma bin dokokin musulunci.
Mutane ƙalilan ne ke bin dokokin Taliban a wasu larduna, sai dai dokokin sun janyo fargaba da kuma ruɗani tsakanin mutane.
"Muna sa hijabi a kodayaushe. Amma hakan bai kawo wani sauyi ba. Me suke nufi? Ban gane ba," in ji Tamana.
Can a baya, kafin da kuma bayan karɓe iko da Taliban ta yi, ba mu taɓa samun wata ƴar Afghanistan da ba ta sanya hijabi ba.
Ɗakin karatu na mata
Domin shawo kan matsalar ƙarancin wurare ga mata a cikin jama'a, Laila Basim ta buɗe wani ɗakin karatu na mata a Kabul wanda muka ziyarta a watan Nuwamban bara.
An tanadi dubban takardu da ke zagaye da ɗakin karatun. Mata na zuwa su yi karatu, inda a wasu lokuta kuma don ganin junansu - saboda ci gaba da zama a gidajensu da suke yi.
A yanzu, an rufe ɗakin karatun.
"Har sau biyu Taliban na rufe ɗakin karatun, amma muna ƙoƙari muna sake buɗe shi. Sai dai barazanar da suke yi na ƙaruwa a kowace rana.
Ina samun kiraye-kiraye ta waya cewa kada na kuskura na buɗe ɗakin karatu na mata. Duk lokacin da suka zo ɗakin karatun, suna faɗa wa mata cewa ba su da damar karanta takardu," in ji Laila. "Yana da haɗari wajen buɗe ɗakin karatu na mata a yanzu, don haka na ɗauki matakin rufe shi kwata-kwata."

Ta ce za ta ci gaba da laluɓo wasu hanyoyi na yaƙi da tsare-tsaren Taliban.
"Gaskiya, Ina cikin fargaba, amma rufe ɗakin karatun ba shi ne ƙarshen al'amuri ba. Akwai wasu hanyoyi da za mu bi don jin muryoyin matan Afghanistan. Yana da matukar wahala da kuma sadaukarwa, sai dai mun fara yunkurin kuma ba za mu fasa ba,'' in ji Laila.
Ga mata waɗanda alhakin ɗawainiyarsu ta yau da kullum ya rataya a wuyansu, suna shiga wahala wajen samun abin da za su dogara da shi.
Meera (wadda aka sauya wa suna) ba ta da aure kuma shekarun ta su haura 40. Ta kasance tana aikin goge-goge a wata makarantar ƴan mata, inda take taimaka wa iyalanta da suka kai mutum 10. Ta rasa aikinta lokacin da aka rufe makarantu.
Har yanzu, ba ta samu wani aikin yi ba a daidai lokaci kuma da ƙasar ke fuskantar matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki.
Roko
A yanzu roko take yi a titunan birnin Kabul.
"Ina ji kamar ba na raye. Mutane sun sa ba ni da komai, don haka suke kokarin taimakona. Na gwammaci mutuwa kan wannan rayuwa da babu inganci,'' in ji Meera yayin da hawaye ke zuba daga idanunta. "Idan na samu dankali, ina fere wa sannan na dafa su. Washegari kuma ina ɗaukar abin da na fere domin bai wa iyalina."
Duk da irin wahalhalu da take ciki, Meera na fatan ƴa'ƴanta mata za su iya zuwa makaranta.
"Idan za su samu ilimi, za su iya samun aiki. Ɗaya daga cikin ƴa'ƴa na mata, na son ta karanci aikin lauya, ɗayar kuma fannin likitanci. a faɗa musu cewa zan nemi kuɗi don ganin sun y karatu, ko da ya kasance roko zan yi, amma ba za su iya zuwa jami'a ba saboda Taliban ta hana hakan." in ji Meera.
"Babu wani abu a yanzu face raɗaɗi da takaici da kuma tsoro a kowane gida a Afghanistan,'' in ji ta.











