Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon dan-sanda ya kashe kananan yara da yawa a makarantar nazare a Thailand
Wani tsohon jami'in 'yan-sanda a Thailand ya kashe mutum akalla 38, galibi kananan yara a wata makarantar rainon yara da ke arewa maso gabashin kasar.
'Yan-sanda sun ce maharin ya yi harbi da bindiga tare da amfani da wuka wajen ta'asar, sannan ya tsere.
'Yan sanda sun ce daga bisani maharin ya kashe kansa, tare da iyalansa, bayan da jami'an tsaro suka fara farautarsa a lardin Nong Bua Lamphu.
Harin ya rutsa da kananan yara masu yawa.
'Yan-sanda sun ce maharin ya yi amfani da harbi da bindiga tare da suka da wuka domin aiwatar da kashe-kashen inda daga bisani ya tsere daga yankin.
A watan Yunin da ya gabata ne aka kori mutumin, mai shekara 34, daga aiki a rundunar 'yan-sandan kasar sakamakon ta'ammali da miyagun kwayoyi.
Kawo yanzu dai ba a san dalilinsa na yin wannan danyen-aiki ba.
Wani malami da ya tsallake rijiya da baya ya shaida wa gidan talbijin na kasar Thairath TV, cewa maharin yakan kawo dansa makarantar a kullum, kuma ana yi masa kallon mutumin kirki.
Akalla yara 22 ne suka mutu a harin, inda kuma aka kai gomman mutane da suka jikkata asibitin gundumar Nong Bua Lamphu.
Wani jami'i a lardin, wanda ke aiki a kusa da makarantar, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ''Maharin ya zo ne da tsakar rana, kuma nan take ya harbe jami'ai hudu zuwa biyar da ke lura da makarantar ciki har da wata mace mai tsohon ciki.
Ya kara da cewa: "Da farko mutane sun dauka masu wasan wuta ne daga nan kuma sai maharin ya zarce zuwa dakin da yaran suke ya bude musu wuta."
Bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna yadda iyaye da 'yan uwan mamatan ke cikin dimuwa da kaduwa, inda wasunsu ke zubar da hawaye, sakamakon bakin cikin da suke ciki.
Jami'an 'yan-sandan da suka hallara a makarantar bayan harin, sun ce sun yi arba da gawarwarkin yara da ma'aikatan makarantar da aka kashe, kwance face-face cikin jini a ciki da wajen ginin makarantar.
Firaministan kasar Prayuth Chan-ocha ya bayyana lamarin da cewa ''abu ne mai tayar da hankali''.