Fari ya haifar da kaurar Zalɓe a Sifaniya

Asalin hoton, Reuters
Tsawon fari da aka dade ana fuskanta a wani yanki mai dausayi a kudanci kasar Sifaniya ya tilasta wa tsuntsayen zalɓe yin kaura zuwa wasu yankuna domin kyankyashe kwayakwayansu .
An ayyana yankin Fuente de Piedra mai dausayi da ke lardin Malaga a matsayin gandun namun daji a 1984.
Sai dai a ranar Asabar manyan tsuntsaye kalilan ne aka iya gani a bakin ruwa.
A tsakiyar watan Mayu, Sifaniya ta sami karancin ruwan sama da kashi 28 fiye da yadda ake tsammani, in ji jami'ai.
Yanayin da ke zuwa kafin bazara ya kasance mafi zafi tun 1961, kuma ana ganin yanayin zai ci gaba da hauhawa har bazara.
A baya 'yaƴan tsuntsaye zalɓe 200,000 ne aka kyankyashe a bakin ruwa a cewar ma'aikatar noma ta yankin Andalusia
Wani mazaunin yankin Alberto Gonzalez Sanchez ya ce hakan ya faru ne saboda sauyin yanayi.
"Wannan abin kunya ne saboda masu yawon bude ido na kai ziyara wannan wuri", in ji Mista Sanchez.










