Abin da ya sa Rasha ke son yin ƙuri'ar raba-gardama a yankunan Ukraine da ta mamaye

Jami'an da Rasha ke goyon baya a yankuna huɗu da ta mamaye a Ukraine sun bukaci a yi kuri'ar raba gardama domin samun damar komawa ƙarƙashi ikonn Rashar.

A yayin da Rasha ke kai hare-hare tare da mamayar wasu yankuna a Ukraine, a yanzu wasu yankunan sun fara yanke shawarar komawa ƙarƙashin Rasha.

Mene ne ke faruwa, me ya sa kuma sai a yanzu?

A daidai lokacin da yaƙin ke shiga wata na bakwai, shugaban Rasha Vladimir Putin ya nuna goyon bayansa kan matakin wadannan yankuna.

To sai dai a baya-bayan nan Ukraine na ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya domin ƙwato yankunan da suka kwashe watanni suna ƙarƙashin ikon Rasha.

A yayin da Putin ke ci gaba da fuskantar matsin lamba game da batun, a yanzu kuma nuna goyon bayansa ga ƙuri'ar raba-gardama zai ƙara janyo masa suka daga kasashen duniya.

Kafafen watsa labaran Rasha sun fara yaɗa ra'ayoyin mazauna yankunan da ke nuna goyon bayansu ga komawa karkashin ikon kasar.

To sai dai wasu na kallon ƙuri'ar a matsayin haramtacciya, saboda za a gudanar da ita ne a yayin da kasar ke tsaka da yaki.

Kamar dai yadda kasashen duniya suka yi watsi da kuri'ar raba-gardama kan yankin Crimea a 2014, shi ma wannan tuni kasashen Jamus da Faransa suka yi Allah-wadai da shirin.

To amma ga Shugaba Putin, kasancewar yankunan a karkashin ikon kasarsa, hakan ka iya sauya fasalin yakin.

Kuma hakan zai sa ya samu damar nuna wa magoya bayan Ukraine cewa ya kamata su daina taimaka mata da makamai, saboda yin hakan ba shi da wani tasiri.

Alexander Baunov, wani mai sharhi ne a kasar Rasha ya kuma ce, abin da Rasha take fata shi ne kasashen Yamma su daina tunanin sanya baki a kan abin da Rasha take kallo a matsayin yankunanta.

Mene ne abin kunya game da ƙuri'ar?

A cikin kwana biyar, daga 23 zuwa 27 ga watan Satumba, yankuna hudu na Ukraine wadanda ke karkshin ikon Rasha za su gudanar da kuri'ar raba-gardamar, inda za a jefa kuri'a a zahiri ko kuma ta intanet a yankunan da ke makwabtaka da yankin Kherson.

Birnin na Kherson dai yanzu ya kasance wani wuri da ba shi da tabbas ta fuskar tsaro, inda dakarun Rasha ke kokarin turje wa hare-haren sojojin Ukraine.

Ko a makon da ya gabata ma dai sai da wani hari ya lalata ginin sakatariyar gwamanatin yankin, abin da ya sa ake tunanin yin ƙuri'ar a yankin ka iya zama abu mai matukar wahala.

Haka kuma ba abu ba ne mai sauki gudanar da ƙuri'ar raba-gardamar a babban birnin Zaporizhzhia.

Rasha ce ke rike da ikon kashi 60 cikin dari na yankin Donetsk a gabashi, sannan kuma ita ce ke riƙe da ikon mafi yawancin yankin Luhansk a arewa maso gabashi.

Mutane da dama ne dai suka ƙaurace wa yankunan.

Tuni dai dama shugaban gwamnatin yankin Donetsk da ke goyon bayan Rasha, Denis Pushilin ya bayar da umarnin kwashe mutane kafin mamayar.

Shugabannin wadannan yankuna dai sun dade suna son yin wannan ƙuri'a, to amma tasowar kiran a daidai wannan lokaci ka iya ƙara zafafa kiraye-kirayensu na yin ƙuri'ar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ''Rasha ta ƙaddamar da yaƙi, ta mamaye wadannan yankuna, ta kashe mutane da dama, ta tilasta wa al'ummomi da dama barin muhallansu, yanzu kuma suna kiran yin ƙuri'ar raba gardama a wadannan yankuna.''

Ma'aikatar tsaron Ukraine ta shaida wa BBC cewa ''mutanen yankunan na son komowa Ukraine, don haka ba za mu amince da wannan ƙuri'a ba, wannan abin kunya ne ga Rasha.''

Me ya faru bayan mamayar?

Shugaban Rasha ka iya daukar matakin mamaye duka yankunan hudu, to amma martanin da yanzu Ukraine ke mayarwa ka iya tayar da sabon hargitsi a yankin.

Rasha ta sha nanata kira ga kasashen kungiyar tsaro ta NATO da su daina bai wa Ukraine makamai, to amma kawo yanzu babu ko daya daga cikinsu da ta goyi bayan ƙuri'ar.

Shin Rasha za ta sake shiri ne?

A baya dai Shugaba Putin ba ya amfani da kalaman yaki kan rikicin, a maimakon haka yakan kira shi da ''Atisayen soji na musamman'' abin da kuma shi ne ya yi masa tarnaki wajen amfani da cikakken karfin soji a yakin, to amma yanzu tana dab da daukar wannan matakin.

Yayin da yankunan hudu ke yunkurin yin ƙuri'ar raba-gardama, majalisar wakilan Rasha na gaggawar yin dokar laifukan yaki na soji- wadda za ta bayar da damar shirya dakaru a ''lokacin yaki''.

Haka kuma dokar za ta kunshi hukunce-hukunce ga wadanda suka bijire, da wadanda suka miƙa wuya, ko kuma suka juya baya a fagen daga.

Mista Putin dai na nuna wa sauran abokansa cewa yana kokarin kawo karshen yakin.

Shugaban Turkiyya ya ce Putin ya shaida masa cewa yana kokarin kawo karshen yakin nan ba da jimawa ba.

To sai dai idan hakan bai samu ba Alexander Baunov ya yi amanna cewa Shugaba Putin zai fara amfani da ƙarfi kan Ukraine, tare da halasta yakin domin bayar da damar daukar matakan gaba.

Shin akwai hatsarin Nukiliya?

Masu yada farfagandar Rasha na yawan barazanar amfani da makamin nukiliyar kasar, musamman a yanzu da dakarunsu ke samun koma-baya a yakin.

Inda kuma suke ci gaba da nuna cewa Ukraine na samun goyon bayan kungiyar NATO, duk da cewa shugabannin Yamma na kokarin kauce wa yaki kai-tsaye da Rasha.

Margarita Simonyan wani mai yada farfagandar ne a gidan talabijin ya kuma ce ''hare-hare kan yankunan Rasha za su iya haddasa cikakken yaki tsakanin Rasha da Ukraine tare da kawayenta 'yan kungiyar NATO''.

Dan majalisar wakilan Birtaniya Bob Seely - wanda ya ziyarci Ukraine a baya-bayan nan, ya ce barazanar makamin nukiliya da ake yi wa Ukraine na matukar tasiri wajen razanarwa da tsoratar da kasashen Yamma wajen taimaka wa kasar da makamai.