Riƙaƙƙun fursunonin da ba a iya yin ido biyu da su

Fursunoni uku wadanda suka zane jikinsu da tatu, a gidan yarin Cecot da ke El Salvador

Asalin hoton, Lissette Lemus/BBC

    • Marubuci, Leire Ventas
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, El Salvador

Ɗaruruwan mutane suka zuro mana ido. Kawunansu duk a aske, suna sanye da fararen tufafi, kuma duk sun zane jikkunansu, fursunonin sun san ana sanya musu ido kuma su ma suna mazurai daga cikin ɗaukunan su.

Muna cikin Cecot - Centro de Confinamiento del Terrorismo - wani gidan yari mafi tsaurin tsaro wanda gwamnatin Shugaba Nayib Bukele ta gina shekara guda da ta gabata saboda "manya-manyan" mambobin ƙungiyoyi masu aikata miyagun laifuka a El Salvador.

Wani gagarumin aiki da aka kaddamar a tsakiyar daji, wani lamari da ke nuni da manufofin tsaro na Bukele wadanda ke janyo cece-ku-ce.

Masu sukar sa sun bayyana gidan yarin a matsayin "bakin ramin take hakkin dan’adam", "ramin kankare da karfe inda ake jefar da mutane ba tare da aiwatar da hukuncin kisa a hukumance ba", in ji Miguel Sarre, wani tsohon ɗan kwamitin Majalisar Dinkin Duniya da ke yaƙi da azabtarwa.

Amma hakan ma babban dalili ne na farin jinin Bukele a cikin al'ummar ƙasar da suka dade suna fuskantar annobar ƙugiyoyi masu aikaita miyagun laifuka, kamar su- Mara Salvatrucha da Barrio 18, da Los Revolucionarios da kuma Los Sureños.

"A nan ne ake kawo miyagun mutane, 'yan ta'adda, masu kisan kai da suka sanya ƙasarmu cikin makoki," in ji shugaban gidan yarin, wanda ba ya son a ambaci sunansa amma ya ba da damar a ɗauki hotonsa.

Zai yi mana jagora yayin da muke wannan ziyarar da aka tsara zuwa makwancin fursunonin.

“Kada ku kalli idanunsu,” ya gargaɗe mu.

Shugaban gidan yarin Cecot shi ne ya jagiranci ƴanjarida na ƙasashen waje

Asalin hoton, Lissette Lemus/BBC

Bayanan hoto, Shugaban gidan yarin Cecot shi ne ya jagiranci ƴanjarida na ƙasashen waje

Tsakar dare ne amma wannan ba matsala ba ce, fitilun da ke kunne ba sa mutuwa.

Wata iska tana ɗan kaɗawa daga saman rufin, tana ɗan samar da sauki daga tsannin zafi na wani ɗan lokaci.

Zafin da ke cikin dakunan na iya kai wa digiri 35 kuma ba su da wata hanyar samun iska.

An kira gidan yarin "Alcatraz na Amurka ta Tsakiya", amma babu alamun lalacewa a tare da ita - komai sabo ne, yana kyalli da sabon fenti.

Masu gadi da suka rufe fuskokinsu suna kallo daga sama, riƙe da bindigogi.

A ƙasa, fursunonin suna hawa kan gadaje masu hawa huɗu waɗanda suke kwana a kai; ba tare da wata katifa ko shimfiɗa ba, suna kwance a kan zallan ƙarfe, suna cin shinkafa da wake da dafaffen kwai ko taliya da hannuwansu.

"Komai na iya kasancewa mummunan makami idan ya je hannusu," in ji daraktan.

Prisoners in a cell sitting on bunk beds four-storeys high

Asalin hoton, Lissette Lemus/BBC

Bayanan hoto, A cikin ɗakunan, fursunonin suna kwana a kan gadaje masu hawa huɗu

Babu wani abu a ɗakunan, sai dai wurin wanke jiki guda biyu da kuma masai guda biyu da ake amfani da su a gaban kowa.

Kuma babu wani abu da za a yi sai kallon lokaci yana wucewa.

Fursunonin suna barin waɗannan dakunan ne na minti 30 kacal a kowace rana, don motsa jiki - a tsakiyar harabar gini ma lamba ‘Block 3’, wanda mu 'yan jarida muke zagayawa.

Akwai wasu rukunnai guda bakwai irin wannan, gidajen yari masu zaman kansu a cikin katafaren filin da ya kai kwatankwacin filayen wasan ƙwallon ƙafa guda bakwai, kewaye da katangar lantarki guda biyu da katangar siminti guda biyu, da hasumiyan gadi guda 19.

Hoton gidan yarin Cecot da ke El Salvador
Bayanan hoto, Gidan yarin Cecot na yankin Tecoluca, kilomita 74 daga kudu maso gabashin babban birnin ƙasar, San Salvador.

Ba a fayyace ko fursunonin Cecot sabbin tsarewa ne ko kuma dauko su aka yi daga wasu gidajen yari ba, ba a kuma san ainihin dalilin da ya sa aka kawo su wannan wurin ba.

Kuma ba a san fursunoni nawa ne ke cikin wannan gidan yarin ba, wanda a cewar gwamnati, zai iya ɗaukan har mutane 40,000. Kuma ko guda nawa ne suke sa ran sauya wa wuri?

Duk da binciken da aka yi na tsawon watanni, BBC ba ta samu sahihan amsoshin waɗannan tambayoyin ba.

Mun tambayi shugaban gidan yarin kai tsaye, inda ya amsa mana: "Ba za mu iya bayar da wannan bayanin ba."

Mun kara tambayar sa: "Mutane nawa ne ke iya zama a kowane ɗaki?"

"Inda za ku iya ajiye mutane 10, za ku iya ajiye 20," in ji shugaban, yana murmushi sanye da takunkumin da ke fuskarsa.

Wani nau'in darasi

Journalists and prison guards inside Cecot

Asalin hoton, Lissette Lemus/BBC

Bayanan hoto, BBC da sauran kafofin watsa labarai sun sami damar zuwa Cecot yayin ziyarar da aka tsara a hankali
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun lokacin da aka buɗe shi a ranar 31 ga Janairu, 2023, BBC ta sha neman izinin shiga gidan yarin.

A ƙarshe gayyatar ta zo ne a ranar 6 ga watan Fabarairu ta hanyar sakon WhatsApp daga jami’in yaɗa labarai na fadar shugaban kasa: “Za mu je Cecot yau da dare.” An shaida mana wurin da za a haɗu minti 30 kafin lokacin tafiyar.

Kwanaki biyu ke nan bayan da Bukele ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓe da kashi 85 cikin ɗari na ƙuri’un da aka kaɗa, yana mai cewa jam’iyyarsa ta lashe kusan dukkanin kujerun majalisar dokoki kafin ma rumfunan zaɓe su kammala kirga ƙuri’un.

“Zai kasance karo na farko da jam’iyya ɗaya tilo ta kasance a ƙasar mai cikakken tsarin dimokraɗiyya.

Duk ƴan adawa sun sha kaye. El Salvador ta sake kafa tarihi a wannan rana, "ya yi iƙirari daga barandar fadar shugaban ƙasa da yammacin ranar zaɓen.

Amma yayin da nake rubuta wannan rahoton (kwana biyar bayan zaɓen), El Salvador ba ta san sakamakonta na karshe ba saboda ƙalubale da dama a tsarin ƙidayar ƙuri'u da kuma shakku kan yadda aka tafiyar da al’amuran zaɓe.

Babu wanda ke jayayya kan nasarar da Bukele ya samu a zaɓen shugaban ƙasa; An mayar da hankali ne kan yaƙin neman kujeru 60 da ake takaddama a kai a Majalisar Dokokin, wanda ikonsa ke da matukar muhimmanci ga tsarin Shugaba Bukele.

Nayib Bukele, El Salvador's president, left, speaks following the presidential election in San Salvador, El Salvador, on Sunday, 4 February 2024

Asalin hoton, Bloomberg via Getty

Bayanan hoto, Shugaba Bukele ya yi magana da magoya bayansa daga barandar fadar shugaban ƙasa a ranar zaɓen

Kamar yadda ya yi iƙirarin samun nasara, Bukele ya jinjina wa kansa kan nasarorin da aka samu a ɓangaren tsaro a wa'adinsa na farko, mayar wa masu sukarsa martani a gaban taron jama'a da suka yi gangami tsakiyar dandalin San Salvador, babban birnin ƙasar.

"Mun tashi daga kasancewa ƙasa mafi hatsari a duniya zuwa zama ƙasa mafi aminci a duk Yammacin Duniya, ƙasa mafi aminci a duk nahiyar Amurka, kuma me suka ce? 'Yana take hakkin ɗan’adam," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, "wane hakkin dan’adam? Ba dai na mutanen kirki ba. Watakila mun fifita hakkin mutanen kirki a kan haƙƙin miyagun mutane, abin da muka yi ke nan”.

Ziyarar da 'yan jaridar ƙasa da ƙasa daban-daban da na masu zaman kansu a ciki bayan kwanaki biyu na iya kasancewa a matsayin ci gaban wannan muhawarar.

Wurin da muka nufa shi ne gidan yarin da ya kasance babbar alamar manufofin tsaro na shugaba Bukele da kuma babban matakinsa na gaggawa wanda ke ba da ikon kama-karya ga 'yan sanda da sojoji - wanda aka kwashe shekara biyu ana aiki da ita.

Kimanin mutane 70,000 ne aka tsare a ƙarƙashin wannan matakin, kuma El Salvador yanzu ta kasance ƙasa mai mafi yawan fursunoni a duniya.

Ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama na cikin gida da na duniya sun yi iƙirarin cewa dubun dubatarsu ba su da wata alaƙa da ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Wasu kuma an tilasta musu haɗa kai da ƙungiyoyin, ko dai a matsayin masu leƙe ko kuma su boye musu bindigogi ko kwayoyi, saboda tsoro.

Cristosal, babbar ƙungiyar kare hakkin bil'adama a ƙasar, ta yi kididdgar laifukan azabtarwa da kuma mutuwar mutane sama da 150 a gidan yarin gwamnati.

A cikin wani rahoto da ta fitar a watan Disamba, Amnesty International ta soki gwamnati, wadda ta ce ta karɓe ragamar gudanar da miyagun ayyuka daga ƙungiyoyin.

Babu wasu cibiyoyi ko ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke ziyartar gidan yarin, Daraktan ya shaida mana, amma ya tabbatar mana da cewa gidan yarin na bin ka’idojin dokokin ƙasa da ƙasa.

Tsaro ta kowane hali

An x-ray machine shows the internal organs of a subject

Asalin hoton, Lissette Lemus/BBC

Bayanan hoto, Matakan tsaro a gidan yarin sun haɗa da na'urar x-ray don gano wasu boyayyun abubuwa har da kayan cikin ɗan'adam

Bayan mun wuce shingen bincike, an caje mu, an yi mana tambayoyi game da zanen jiki da na’urar X-ray wanda ke ɗaukar hoto har hanji – sai aka kai mu mu gana da wasu fursunonin.

Bukele ya ƙaddamar da yaƙi da ƙungiyoyin da ke aikata munanan laifuka ta hanyoyin da suka kawo masa farin jini da ba a taɓa ganin irin sa ba, amma kuma ya jawo tambayoyi masu tsanani kan take hakkin ɗan’adam, kuma daraktan ya bukaci mu yi gaba da gaba da mutanen da gwamnatin ke yaƙa.

Masu gadin sun fito da mutane biyar da aka zaɓa daga ɗakunansu, amma sai da suka ɗaure su da ankwa a wuyan hannu da idon sawunsu. Sun durkusar da su, kuma an sa suna fuskantar bango.

Ba a ba su damar yin magana ba.

"Zo nan, ka juyo, cire rigarka." Ya gabatar da mu ga fursuna na farko: Miguel Antonio Díaz Saravia, wanda aka fi sani da "Castor", aka kuma shaida mana cewa ɗan ƙungiyar Mara Salvatrucha ne.

A cikin 2022, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 269 a gidan yari saboda yin garkuwa da mutane da azabtarwa da kuma kisa (tare da wasu 'yan kungiyar) wasu sojoji huɗu a watan Oktoban 2016.

A prisoner shows his back tattooed with symbols of the Mara Salvatrucha gang

Asalin hoton, Lissette Lemus/BBC

Bayanan hoto, Zanen jikin wannan fursunan ya nuna cewa shi mamba ne na ƙungiyar Mara Salvatrucha

Marvin Mario Parada, da aka samu da laifin kisan Alison Renderos, ƴar makaranta ƴar shekara 16 da ke wasan kokawa a shekarar 2012, shi ma ya nuna mana zane-zanen da ke fatar jikinsa.

Wani ɗan El-salvador mai ɗaukar hoto da ya zauna kusa da ni lokacin da muke dawowa babban birnin ƙasar ya shaida mun cewa:

“Na tuna yadda suka je suka gano gawar ta a wani magudanar ruwa da ke San Vicente''.

"Na yi rahoto kan lamarin kuma na ga yadda mai binciken ya jera ɓangarorin jikinta a kan tebur,"

Muka ci gaba tattaunawar da wani mai daukar hoto.

Sa'a ɗaya da muka yi kan hanya ya kasance tamkar bitar ayyukan ta'addanci da manyan laifuka na kungiyoyin, kamar wasu fasinjoji 17 na wata ƙaramar bas da suka banka wa wuta da ransu a shekarar 2010.

Prisoners in a cell at Cecot

Asalin hoton, Lissette Lemus/BBC

Bayanan hoto, Fursunonin a Cecot suna fita daga dakunansu na tsawon minti 30 ne kowace rana

"Na kuma shafe shekaru da yawa ba tare da na iya ziyartar kawuna ba, wanda ke zaune a wannan unguwar," in ji mai ɗaukar hoton, yayin da yake magana kan iyakokin da ba a iya gani da suka raba yankunan da ƙungiyoyin da ke adawa da juna ke da iko da su.

"Idan ka shiga wannan yankin, ba za ka fito ba."

Na taɓa jin irin waɗannan labarai a kasuwannin tituna da unguwannin talakawa, da otal-otal na birni da bakin teku, a kwanakin da suka rage kafin zaɓen 4 ga watan Fabrairu.

Har ila yau akwai kuma waɗanda ke nuna goyon bayan dokar ta-baci, wadanda ke jaddada duk hasashen da aka yi na nasarar Bukele a zaɓen.

Bayan kwashe shekaru suna fama da barazanar rashin tsaro da tashe-tashen hankula, da alamar yawancin ƴan El-salvador na niyyar jure mulkin Bukele in dai har tsaro zai tabbata.