Abin da ya kamata ku sani bayan wasan mako na biyu a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Litinin aka karkare karawar mako na biyu wasa na 10 a gasar Premier League, shi ne wanda Liverpool da Crystal Palace suka tashi 1-1 a Anfield.
Wasa na biyu kenan da Liverpool ta raba maki a bana, bayan da ta tashi 2-2 a makon farko a gidan Fulham, ita kuwa Palace ta sha kashi a hannun Arsenal da ci 2-0 a Selhust Park.
Jumulla an buga wasa 20 kenan a babbar gasar tamaula ta Ingila, an kuma ci kwallo 56.
Wanda ke kan gaba a cin kwallaye shi ne Rodrigo na Leeds United mai uku a raga kawo yanzu.
Jerin 'yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League
- Rodrigo Leeds United 3
- Pascal Gross Brighton & Hove Albion 2
- Gabriel Jesus Arsenal 2
- Erling Haaland Manchester City 2
- Pelenda Joshua Da silva Brentford 2
- Aleksandar Mitrovic Fulham 2
- Gabriel Martinelli Arsenal 2
Wasan da aka ci kwallaye da yawa a gida
Manchester City 4–0 Bournemouth ranar 13 ga watan Agustan 2022
Brentford 4–0 Manchester United ranar 13 ga watan Agustan 2022

Asalin hoton, Getty Images
Wasan da kungiyar gida ta sha kashi kwallaye da yawa
Crystal Palace 0–2 Arsenal ranar 5 ga watan Agustan 2022
West Ham United 0–2 Manchester City ranar 7 ga watan Agustan 2022
Wasan da aka ci kwallaye da yawa a raga
Arsenal 4–2 Leicester City ranar 13 ga watan Agustan 2022

Asalin hoton, Getty Images
Yadda teburin Premier yake bayan wasan mako na biyu
- Manchester City
- Arsenal
- Brentford
- Tottenham
- Newcastle United
- Leeds United
- Chelsea
- Brighton
- Aston Villa
- Nottingham Forest
- AFC Bournemouth
- Liverpool
- FC Fulham
- Wolverhampton
- Leicester City
- Crystal Palace
- Southampton
- FC Everton
- West Ham United
- Manchester United










