An shiga rana ta biyu ana neman wanda ya kashe mutane 18 a Amurka

Asalin hoton, REUTERS
An shiga rana ta biyu ta neman kama wani mutum da ake zargi da kisan mutum 18 da raunata wasu 13 yayin wani harbi da ya yi a Maine
Ƴan sanda sun ce Robert Card yana ɗauke da makami kuma sun buƙaci mutane su yi zaman su a gida don kaucewa fito na fito da shi.
A cikin daren Alhamis ne ƴan sanda suka taru a wani gida da ke Bowdon, mai nisan tafiyar minti 20 zuwa Lewiston, wajen da aka yi harbe-harben.
Ƴan sandan sun ce suna bincike don gano wajen da ya boye, kuma suna da izinin shiga gidaje don bincike a hannun su.
An riƙa jiyo ƙara da kuma ihun ƴan sandan na neman mutumin ya miƙa wuya.
Jami’an hukumar tsaron tarayya ta FBI da sauran jami’an tsaro na jiha ne ke gudanar da aikin haɗin gwiwa, inda suke bin gida-gida suna bincike.
Wani jami’i a ofishin ma’aikatar tabbatar da tsaron jama’a ya ce "ina zaton jami’an suna aikin da ya dace don ganin cewa sun bincika kowanne lungu da saƙo da kuma tabbatar da ganin sun kama Card".
An fara jin harbin ne a wani yanki na Lewiston, inda aka kashe wata mata da kuma maza shida.
Cikin minti 10 kuma harbin ya canza waje zuwa gidan abinci na Schemengees Bar & Grille, inda aka jikkata wasu mutanen fiye da takwas.
Daga cikin mutum 16 da aka fara garzayawa da su asibiti da farko, uku sun mutu.
A halin yanzu dai an rufe makarantu da kasuwanni a Lewiston da garuruwan da ke makwabtaka da shi.
Da alama mutanen yankin sun yi biyayya ga umarnin zama a gidajen su, yayin da ƴan sanda ke cigaba da sintiri.
Ƴan sanda sun ce wanda ake zargin ya yi fama da matsalar ƙwaƙwalwa a kwannan nan, inda ya riƙa jin muryoyi masu tunzura shi don kai farmaki a kan wata cibiyar soji da ke kudancin Maine.
Akwai kuma rahoton cewa an kai shi wani gidan kula da masu taɓin hankali, bayan da ya fara wasu abubuwa da suka saɓa tunani a lokacin da yake ɗaukar horo a kwalejin horar da dakarun Amurka.

Asalin hoton, REUTERS
FBI da sauran hukumomin tsaron tarayya na tallafawa jami’an tsaron yankin don zaƙulo wanda ake zargin. Haka nan kuma an sanar da jihohin da suka yi iyaka da su halin da ake ciki don ganin sun taimaka.
An kuma fargar da jami’an tsaron kan iyakar Canada don ɗaukar mataki.
Maine ce jihar da tafi kowacce ƙarancin samun aikata kisa a Amurka baki ɗaya.
Shugaba Joe Biden ya bayar da umarnin yin ƙasa da tutar ƙasar a fadar White House da kuma sauran gine-ginen gwamnatin tarayya, don karrama mutanen da suka mutu.











