Sana'o'i 10 da ke fuskantar barazanar ɓacewa saboda fasahar zamani

Asalin hoton, Getty Images
Fasahar zamani na sauya rayuwar mutane ta hanyoyi daban-daban.
A yayin da wasu sabbin abubuwan fasahar zamanin ke kawo sauƙi da inganci, a gefe guda kuma suna shafar wasu harkokin da aka saba da su.
Sana'o'i da kasuwanci na daga cikin ɓangarororin da suka fi fuskantar sauye-sauye sakamakon zuwan fasahar zamani.
Sana'o'i masu yawa da a baya mutane ke dogara da su domin samun rufin asiri da biyan buƙatun rayuwarsu ta yau-da-kullum na fuskantar ɓacewa, musamman ƙananan garuruwa da ƙauyuka.
Wasu daga cikin waɗannan sana'o'i sun fara raguwa ko ma kusan shuɗewa gaba ɗaya saboda zuwan fasahar zamani da sabbin hanyoyin sadarwa na zamani.
Dalilin haka ne BBC Hausa ta zaƙulo wasu sana'o'i 10 da ke fuskantar barazanar ɓacewa a Najeriya saboda ci gaban fasahar zamani.
Sayar da kaset

Asalin hoton, Getty Images
A baya kaset ne hanya mafi sauƙi wajen sauraron sauti, kama daga karatuttuka da waƙoƙai da ma hirarraki.
Mutane kan je kasuwa su sayi kaset domin su saurara a gida ko mota.
Haka kuma akan sayar da kaset ɗin da babu komai a cikinsa ga masu buƙatar naɗar sauti domin su nadi sauti ta hanyar amfani da rikoda.
Yanzu, an maye gurbin kaset da na'urar mp3 wajen sauraron sauti, musamman a awayoyin zamani ko sauran na'urorin sauraron sauti.
Lamarin da ya sa masu irin wannan sana'a a baya yanzu suka haƙura da ita, sakamakon rashin kasuwar da sana'ar ke da shi saboda zuwan fasahar zamani.
Sayar da DVD/CD

Asalin hoton, Getty Images
Sana'ar sayar da faya-fayen DVD da CD masu ɗauke da fina-finai da waƙoƙi a ciki ita ma na neman zama tarihi a Najeriya.
A baya wannan sana'a ta shahara tsakanin musamman dillalan fina-finai da ƴan kasuwar film.
A wasu lokutan da suka gabata akan samu masu buɗe shagunan bayar da hayar irin waɗannan kaset-kaset musamman ga masu gidajen kallo waɗanda ke karɓa domin haskawa masu kallo.
To sai dai da alama bayan zuwan sabbin fasahohin zamani irin su Youtube da Netflix, wannan sana'a ta ɓace a wurare da dama.
Gyara da sayar da rediyo

Asalin hoton, Getty Images
A baya rediyo na ɗaya daga cikin muhimman na'urorin da ake alfari da mallakarsu musamman don sauraren labaran duniya da jin gaishe-gaishe a shirye-shiryen zaɓi sonka da gidajen rediyo ke shiryawa.
Saboda yadda Hausawa suka shaƙu da rediyo har kirari suke yi mata da ''radiyo abokin hira''.
Saboda yawan amfani da radiyo ya sa kasuwar sayar da shi ta bunƙasa, inda mutane da dama ke cin abinci daga sana'ar sayarwa da kuma gyara ta da ma masu sayar da kayan gyaran.
To sai dai sannu a hankali bayan zuwan fasahar zamani inda ake samun radiyoyi a kan wayoyin hannu da kuma wasu manhajojin sauraron radiyo da ake da su a kan wayar hannu ya sa mutane suka rage amfani da radiyo.
Hakan ne kuma ya sa kasuwarta ta ja baya, haka ma masu gyarata suka fara rasa kwastomomi.
Gyara da Sayar da agogo

Asalin hoton, Getty Images
Kamar sauran sana'o'in da muka ambata a baya, ita ma sana'ar sayar da agogo na fuskantar wannan barazana.
A baya wasu mutane kan ɗaura agogo saboda duba lokaci ko kwalliya, amma kasancewa a yanzu kowa na da wayar hannu kuma tana ɗauke da agogo ya sa mutane da dama masu damu da ɗaura agogon hannu ba.
Haka ma agogon bango da ake ajiye cikin ɗakuna ta fara zama tsohon yayi, inda a yanzu sai a masallataiu kawai ake samun agogon bango.
Wannan ya sa tsohuwar sana'ar gyaran agogo da aka sani a baya, ke fuskantar barazana.
Kodayake har yanzu ana ɗaura agogon zamani da ake yi wa kirari da komai da ruwanka, saboda ana iya haɗa shi da waya domin amsa kira ko auna lafiya da nisan tazara, ba kowa ba ne ya iya gyaransa.
Sayar da fitila da gyara ta
A baya fitila, wadda ake saka wa kalanzir ko kuma cocila da ake saka wa batir a hannu ana haskawa sun kasance abubuwan da ake amfani da su lokacin da wutar lantarki ta ɗauke.
Don haka ne ake samun masu sana'o'in sayar da su da kuma gyara su idan sun lalace
A yanzu mutane na amfani da fitilun caji (rechargeable lamps) da wutar solar da wayoyi masu haske.
Hakan ya rage buƙatar fitila sosai wanda ya saka sana'ar kananzir ma yayi ƙasa.
Sayar da katin waya

Asalin hoton, MTN
A baya jama'a na cika shagunan sayar da kati domin siyan katin kiran waya ko aika saƙo.
Amma a yanzu ta dalilin fasahar zamani, ana sayen kati ta manhajojin bankuna da na'uarar cirar kuɗi ta POS.
Waɗannan abubuwan sun janye yawancin masu siye daga shagunan katin waya, wani abu da ke barazana da sana'ar.
Sana'ar ɗaukar hoto

Asalin hoton, Getty Images
Shagunan ɗaukar hoto na daya daga cikin sana'o'in da ke da dimbin masu shiga.
A da, ana zuwa studio domin daukar hoto na fasfo ko na biki ko na wani taro.
Amma kuma yanzu, wayoyin zamani da kamara masu ƙarfi da manhajojin gyaran hoto sun rage buƙatar zuwa studio.
Har wayar hannu na iya ɗaukar hoton fasfo cikin sauƙi.
Sayar da littattafai

Asalin hoton, Getty Images
A bayan, shagunan littattafai suna da albarka musamman a kusa da makarantu.
Ɗalibai da malamai da sauran mutane na siyan littattafan karatu, na addini da na karatu.
Yanzu, litattafai na intanet wato e-books da PDF da manhajojin karatu kamar OkadaBooks da Scribd sun sauya yanayin.
Mutane na saukar da littafi cikin waya ko kwamfuta, ba tare da zuwa siye ba.
Sana'ar aika saƙo/kiran waya

Asalin hoton, Getty Images
Shagunan kiran waya sun kasance tushen sadarwa a shekarun baya.
Idan mutum baya da waya ko ba shi da kati, sai ya je ya biya a yi masa kira ko a aika masa saƙo.
Amma yanzu, yawancin mutane na da waya, da manhajojin aikawa da saƙonni ta WhatsApp, da Facebook da intagram da twitter da sauran hanyoyin da ke bai wa mutum damar yin kira ko aika saƙo ba tare da fito zuwa wani shago ba.
Sayar da waƙoƙi ta bluetooth ko turawa a kaset

Asalin hoton, Getty Images
A shekarun da suka gabata, matasa na tura waƙoƙi da bidiyo daga waya zuwa waya ta hanyar Bluetooth ko memory card ko kuma ma a tura musu a kaset kuma suna karɓan kuɗi.
Yanzu da zuwan intanet da manhajoji kamar Boomplay da spotify da Telegram sun maye gurbin wannan hanya.
Yawanci mutane su kan sauke duk abin da suke so kai tsaye cikin waya.
Waya ta gaje komai

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da wasu sana'o'i ke fuskantar barazanar ɓacewa, waya ta gaje komai a zamanin yanzu.
Tare da zuwan wayoyin zamani da fasahohin intanet, ayyuka da dama da ake buƙatar mutane su je waje a yi musu, yanzu ana iya yi daga gida ko daga ko ina.
Mutane na amfani da waya wajen yin banki da siyayya da karatu da tura saƙonni da shirya tafiye-tafiye da kallon fina-finai da dai sauransu.
Wannan sauyi ya rage dogaro da sana'o'in da ke buƙatar hulɗa kai tsaye kuma yana barazana ga ci gaba da wanzuwarsu.
A haka ne fasahar zamani ke ci gaba da sauya tsarin rayuwa da sana'o'in mutane, inda waya ke zama cibiyar rayuwar yau da kullum.











