Abin da muka sani kan maharin da ya kashe mutum 15 a Amurka ranar sabuwar shekara

Lokacin karatu: Minti 3

Mutane 15 sun mutu sannan aƙalla 35 sun jikkata bayan wani mutum ya bi ta kan gomman mutane da motarsa a safiyar ranar farko ta sabuwar shekara a birnin New Orleans, in ji hukumomi.

Ga abin da muka sani zuwa yanzu.

Wane ne Shamsud Din Jabbar?

An bayyana mutumin da ya kai harin a layin Bourbon a safiyar Laraba a matsayin Shamsud Din Jabbar, mai kimanin shekara 42 a duniya.

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta tabbatar da cewa tana binciken harin a matsayin ''harin ta'addanci'' kuma kafar watsa labaran CBS ta tabbatar da cewa ya mutu bayan harbin sa da ƴansanda suka yi.

Tun da farko ƴansanda sun ce wanda ake zargin ya harbi jami'an tsaron ƴansanda a lokacin da suka zo wurin da aka kai harin.

Jami'a ta musamman a Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI, Alethea Duncan ta ce hukumomin tsaro ba su yarda cewa wanda ake zargin ne kawai ke da hannu a kai harin ba.

Ta buƙaci duk wanda ke da wani bayani ko kuma wanda ya yi wata hulɗa da maharin a sa'o'i 17 da suka gabata ya tuntuɓi hukumar ta FBI.

''Wannan bincike ne da ke gudana kuma ana ƙoƙari wajen warware shi cikin sauri,'' in ji ta.

Duncan ta tabbatar da cewa wanda ya kai harin tsohon soja ne, inda ta ce suna ganin cewa yana hutu ne, sai dai ba su tabbatar da hakan ba.

Tawagar bincike ta BBC ta gano motar da yake ciki, fara ƙirar Ford F-150 Lightning, wadda gaban motar ya lalace, a gaban wani gidan rawa mai suna Rick's Carbet a titin Bourbon kusa da mahaɗar titin Conti.

A cewar hukumomi, motar hayar ta aka yi ba ta wanda ake zargi ba ne.

Masu bincike sun ce sun gano wasu abubuwa biyu da ake ganin masu fashewa ne a wurin da aka kai harin.

An kuma gano wata doguwar bindiga wadda aka maƙala wa salansar hana yin ƙara a wurin da lamarin ya faru, in ji rahoton CBS.

Su wane ne aka raunata?

Ƴansanda sun ce mutane 10 sun mutu kuma aƙalla mutane 35 sun samu raunuka.

Sai dai har yanzu ba a gano ko su waye ba.

Tuni aka kai waɗanda suka ji raunuka asibitocin da ke kusa domin karbar magani da samun kulawa.

Ƴan sanda na ganin cewa waɗanda harin ya rutsa da su ƴan birnin ne na New Orleans da ke jihar Louisiana.

A ina harin ya auku?

Titin Bourbon sanannen wuri ne da mutane ke zuwa yawon dare, kuma wuri ne da masu yawon buɗe ido ke yawan zuwa da ke cike da gidajen cin abinci, mashaya, da gidajen rawa da kuma waƙoki.

Yana wani wuri ne a birnin New Orleans da ke janyo masu yawon buɗe ido da ƴan gari, musamman lokacin bukukuwan sabuwar shekara.

Wani wuri ne da turawan Faransa suka kafa a shekarar 1718, kuma tsarin gina layukan da aka yi a baya shi ne ke janyo masu yawon bude ido zuwa birnin.

Duk shekara , mutane fiye da miliyan ɗaya ke zuwa wurin bikin mai farin jini, wanda ya yi fice saboda duwatsun kwaliyya masu launi daban daban da masu zuwa wurin ke sanyawa.

Me waɗanda suka shaida harin ke cewa?

Wani shaida, wanda ke kan titin Bourbon a lokacin da harin ya faru ya bayyana yadda lamarin ya faru.

Whit Davis, daga garin Shreveport da ke jihar Louisiana ya shaida wa BBC cewa: ''muna ta kai-komo a kan titin Bourbon tun da yammaci.

''A lokacin da muke cikin mashaya, ba mu ji ƙaran harbi ko hatsari ba saboda waƙar da aka kunna ta yi ƙara sosai,'' in ji Davis.

Ƴansanda sun riƙe Mista Davis da wasu mutanen da ke mashayar, a lokacin da aka sake su su tafi, ya ce ''muna ta wucewa ta gefen gawarwaki da mutanen da suka ji raunuka cike da titin''.