Ƙayyade sojoji da haramcin shiga Nato: cikin buƙatun da Trump ke son Ukraine ta amince da su

Asalin hoton, Reuters
An ganin cewa akwai abubuwa da dama da ke ƙunshe cikin shawarwarin da Amurka ta miƙa wa Ukraine game da yaƙinta da Rasha, kuma a cikinsu akwai batun miƙa yankin Donbas na gabacin ƙasar Ukraine mai yawan masana'antu, ga Rasha.
Haka nan shawarwarin sun ƙunshi rage yawan sojojin Ukraine zuwa 600,000.
To mene ne sauran buƙatun kuma wane ne zai fi amfana?

Asalin hoton, EPA / Shutterstock
Akwai manyan abubuwa guda 28 a cikin shawarwarin, kuma akwai da dama daga cikinsu da ake ganin Ukraine ba za ta amince da su ba. Wasu kuma babu ciakken bayani a kansu.
Za a samu "matsaya" game da ƴancin Ukraine sannan za a cimma "cikakkiyar yarjejeniyar haramta duk wata wata takalar faɗa tsakanin Rasha da Ukraine da Tarayyar Turai", da kuma cikkaken "tabbacin tsaro" ga Ukraine da kuma buƙatar a gudanar da zaɓe cikin kwana 100.
Idan har Rasha ta kai wa Ukraine hari a nan gaba za a samu "gagarumin martani na soji" tare da sake mayar mata da jerin takunkumi da kuma rushewar yarjejeniyar.
Amma a ɓangaren tabbacin tsaro, babu cikakken bayani game wanda zai bayar da tabbacin da kuma yadda zai kasance.
Wannan ya gaza a kan tsarin Nato na sashe na biyar wanda ya ce hari kan Ukraine tamkar hari ne kan dukkanin ƙasashen Nato. Ukraine za ta so a tabbatar mata da tsarin da za a aiwatar, ba kawai cewa za a bayar da tabbacin tsaro ba.
Miƙa yankin Ukraine ga Rasha da rage yawan dakaru
Ɗaya daga cikin batun da ake taƙaddama a kai shi ne shawarar miƙa wasu yankunan Ukraine ga Rasha, waɗanda ba sa cikin wuraraen da Rasha ta mamaye.
Sai kuma batun rage yawan dakarun Ukraine.
"Dakarun Ukraine za su janye daga wani ɓangare na yankin Donetsk Oblast wanda ke ƙarƙashin ikonsu a yanzu, kuma za a ɗauki wurin a matsayin yankin da ba na kowa ba, kuma yankin da ba za a jibge sojoji a cikinsa ba, wanda ƙasashen duniya za su amince da shi a ƙarƙashin ikon Rasha. Dakarun Rasha ba za su mamaye yankin ba."
Miƙa wani yanki wanda al'ummar Ukraine aƙalla 250,000 ke rayuwa a cikin shi – wato Donetsk mai ƙunshe da birane kamar Slovyansk, Kramatorsk da Druzhkivka – ba abu ne da ƴan Ukraine za su amince da shi ba.
Rasha ta kwashe sama da shekara ɗaya tana fafutikar ƙwace garin Pokrovsk – zai yi matuƙar wahala Ukraine ta miƙa wannan yanki maimatuƙar muhimmanci salun-alun.

Asalin hoton, Reuters
"Ƙayyade yawan sojojin Ukraine zuwa mutum 600,000."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan Janairun da ya gabata an ƙiyasta yawan sojojin Ukraine a mutum 880,000, daga mutum 250,000 a farkon samamen Rasha a watan Fabarairun 2022.
Duk da cewa ƙayyade yawan sojojin Ukraine a mutum 600,000 ba abin damuwa ba ne a lokaci na zaman lafiya, amma irin haka zai zama tauye hakkin Ukraine a matsayinta ta ƙasa mai ƴanci. Kuma zai iya yiwuwa Rasha ta ce sun yi yawa.
"Iyakokin da muka gindaya a bayyane suke kuma ba waɗanda za a sassauta ba ne," kamar yadda wakiliyar Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya Khrystyna Hayovyshyn ta shaida wa kwamitin tsaro: "Babu yadda za a yi a amince a hukumance ko ma ba a hukumance ba, cewa yankunan da Rasha ta mamaye sun zama nata. Ukraine ba za ta amince da duk wani yunƙuri na takure hakkokinta ba na kare kanta, musamman game da yawan ƙarfin sojinta."
Haka nan ƙunshin shawarwarin ya buƙaci "a amince da yankunan Crimea da Luhansk da Donetsk a matsayin ƙarƙashin Rasha, hatta Amurka ma za ta amine."
Wato ba dole ba ne sai Ukraine da wasu ƙasashen sun amince da hakan ba a hukumance. Zai iya yiwuwa Ukraine ta amince da hakan, saboda ba zai ci karo da tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar da ya ce "ba za a iya cire wani ɓangare na ƙasar ba".
A yankunan kusanci irin su Kherson da Zaporizhzia, za a amince da iyakokin da suke a yanzu, wanda hakan ke nufin Rasha za ta iya rasa wasu yankunan da ta mamaye a baya.

Asalin hoton, Reuters
Makomar Ukraine – za ta iya shiga Tarayyar Turai amma ba Nato ba
Shawarwarin sun samar da matsaya kan makomar Ukraine:
"Ukraine ta amince a kudindin tsarin mulkinta cewa ba za ta taɓa shiga Nato ba, kuma Nato, a cikin tanade-tanadenta za ta amince cewa ba za ta karɓi Ukraine a cikinta ba a nan gaba."
"Ukraine za ta iya shiga Tarayyar Turai da kuma samun shiga kasuwannin Turai na wani lokaci yayin da ake ci gaba da nazari kan batun.
Babu wata alamar yiwuwar shigar Ukraine cikin Nato a wani lokaci nan kusa, kuma a baya-bayan nan Rasha ta sassauta ra'ayinta game da yunƙurin Ukraine na shiga Tarayyar Turai.
Ƙoƙarin shiga Tarayyar Turai da kuma ƙungiyar Nato na cikin kundin tsarin mulkinta, kuma wani abu da Khrystyna Hayovyshyn ta nanata a jawabinta a Majalisar Dinkin Duniya shi ne "Ba za mu lamunci duk wani katsalandan a ƴancinmu ba, ciki har da ƴancinmu na zaɓen wadanda muke son mu ƙulla ƙawance da su."
Wata shawarar kuma it ace Nato za ta yarda cewa ba za ta jibge dakarunta a Ukraine ba. Kuma Kyiv za ta Sanya hannu kan zama "wadda ba za ta mallaki makamin nukiliya ba".
Wannan ya ci karo da matsayar ƙasashen yamma ƙarƙashin jagorancin Birtaniya da Faransa.

Asalin hoton, Reuters
Dawo da Rasha cikin tsara
Wasu ɓangarori da dama na yarjejeniyar sun ambaci daina mayar da Rasha saniyar ware inda "za a mayar da Rasha cikin tsarin tattalin arziƙi na duniya" tare da mayar da ita cikin jerin ƙasashe takwas masu ƙarfin tattalin arziƙi na duniya, wato G8.
Wannan abu ne da zai iya ɗaukar dogon lokaci kasancewar akwai takardar sammace na kotun manyan laifuka na duniya a kan shugaba Putin. An fitar da Rasha daga cikin ƙungiyar G8 ne bayan ta ƙwace yankin Crimea a shekarar 2014, said ai Trump ya so mayar da Rasha cikin ƙungiyar shekaru 6 da suka gabata.
Ko daftarin zai iya aiki?

Asalin hoton, Reuters / EPA / Shutterstock
Ya za a yi da kadarorin Rasha da aka ƙwace?
Shawarwarin sun ƙunshi amfani da kadarorin Rasha waɗanda suka kai darajar kuɗi dala biliyan 100 "a yunƙurin Amurka na sake ginawa da zuba jari a Ukraine"
Wannan kuɗi da aka ambata ba za su isa gudanar da aikin ba: A farkon wannan shekara an yi ƙiyasin kuɗin sake gina Ukraine zai kai dala biliyan 524.
Mene ne ba a ambata ba a shawarwarin?
Masu Nazari da dama sun gano cewa shawarwarin bas u ƙunshi ƙayyade yawan makamai ga sojojin Ukraine ba da kuma kamfanoninta na haɗa makamai, duk da akwai wani ɓangare da ya ce: Idan Ukraine ta harba makami a kan biranen Moscow ko St. Petersburg, wannan zai wargaza batun ba ta tabbacin tsaro.
Shin wannan ce matsaya ta ƙarshe?
Mun gano cewa Amurka na son matsa lamba domin aamincewa da shawarwarin, inda wasu rahotanni ke cewa wajibi ne Ukraine ta amince da shawarwarin kafin ƙarshen mako mai shigowa.
Haka nan kuma, sakataren harkokin waje na Amurka Marco Rubio, wanda ke cikin wadanda suka tsara shawarwarin ya bayyana su a matsayin"wasu shawarwari da za su iya kawo ƙarshen yaƙin'.
Shin shawarwashin muradun Rasha ne kawai?
Jakadan Rasha na musamman, Kirill Dmitriev ya kwashe kimanin kwana uku yana tattaunawa kan shawarwarin da jakadan Amurka Witkof, lamarin da ya sa ake raɗe-raɗin cewa shawarwarin sun fito ne daga gwamnatin Rasha.
Rasha na taka tsantsan wajen mayar da martini kan batun amma an ce za su "iya zama tsuhen hanyar nemo zaman lafiya.
Batun miƙa yankunan Ukraine ga Rasha shi ne babban abin da ke nuna cewa shawarwarin sun fi karkata ne ga ra'ayin Rasha. To amma yin amfani da iyakokin da suke a yanzu a wasu yankuna abu ne mai wuya ga Rasha, wadda ta ƙwace Kherson da Zaporizhzhia.










