Me ya sa Thailand da Cambodia ke faɗa?

Sojan Thailand.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojan Thailand tsaye kusa da wani wurin bauta mai muhimmanci, a kan iyakar ƙasar da Cambodia da ake taƙaddama a kai
    • Marubuci, Jonathan Head
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News in Bangkok
    • Marubuci, Kelly Ng
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Artabu tsakanin sojojin Thailand da Cambodia a kan iyakar ƙasashen da ake rikici a kai, ya janyo mutuwar mutum 12, a cewar hukumomin Thailand.

Faɗan ya janyo bazuwar rikici tsakanin ƙasashen biyu da ke gabashin Asiya, wand aya samo asali sama da shekara 100 da suka wuce.

Yawancin waɗanda suka jikkata sun kasance fararen hula kuma dukkansu sun fito daga lardunan Thailand, a cewar sojojin Thailand - waɗanda kuma suka ruwaito cewa mutane da dama sun jikkata.

Cambodia dai ba ta kai ga tabbatar da cewa ko ta samu waɗanda suka mutu ba.

Ɓangarorin biyu sun yi bata-kashi a sanyin safiyar ranar Alhamis. Faɗan ya bazu cikin sauri, inda Thailand ta zargi Cambodia da harba mata rokoki zuwa cikin wani ƙauye da kuma far wa asibiti.

Ita ma Bangkok ta kai hare-hare ta sama kan wuraren sojin Cambodia.

Thailand a rufe iyakarta da Cambodia bayan da ta buƙaci dukkan ƴan ƙasarta su fice.

A ɗaya gefe, ita Cambodia ta rage alaƙarta da Thailand wadda suka zarga da amfani da "ƙarfi fiye da ƙima".

Dukkan ƙasashen sun buƙaci mutanensu da ke kusa da kan iyaƙar da su tashi daga yankin, inda shaidun gani da ido suka bayar da rahoton cewa ana tsananin faɗa.

"Abin tayar da hankali ne. Muna haɗa kayanmu don ficewa," kamar yadda Sutian Phiwchan, wani mazaunin lardin Buriram na Thailand kusa da iyaƙa da Cambodia ya shaida wa BBC.

Me ya sa Thailand da Cambodia ke faɗa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rikicin ya samo asali ne sama da shekaru 100 da suka wuce, lokacin da iyaƙar ƙasashen biyu suka haɗu bayan mamayar da Faransa ta yi wa Cambodia.

Abubuwa sun yi tsamari a 2008, lokacin da Cambodia ta yi ƙoƙarin yin rajistar wani wurin bauta wanda shi ne na 11 da aka kafa a yankin da ake yin taƙaddama a kai - wanda Unesco ta ayyana a matsayin wuri mai muhimmanci - lamari da ya janyo gagarumar zanga-zanga a Thailand.

An samu artabu a tsawon shekaru, abin da ya janyo kashe sojoji da kuma fararen hula daga dukkan ɓangarori.

Sabon rikici ya ƙaru ne a watan Mayu bayan da aka kashe sojan Cambodia a wani artabu. Wannan ya janyo raguwar hulɗa tsakanin ƙasashen na sama da shekara goma.

A cikin watanni biyu da suka wuce, dukkan ƙasashen sun sanya takunkumi na kan iyaƙa ga juna. Cambodia ta haramta shigo da kayayyki daga Thailand kamar ganyayyaki da kayan lemu, da kuma dakatar da shigo da makamashi da layukan intanet.

Dukkan ƙasashen sun ƙara girke dakaru a kan iyaƙar a makonnin baya-bayan nan.

Ina rikicin ya nufa?

Muƙaddashin Firimiya na Thailand Phumtham Wechayachai, ya ce rikicinsu da Cambodia ya "lalace" kuma ya kamata a yi taka tsantsan, kuma karkashin tsarin dokar ƙasa da ƙasa.

Firaministan Cambodia Hun Manet ya ce ƙasarsa na son warware rikicin dake tsakanin ƙasashen cikin sauki kuma ba su da "zaɓi" illa "mayar da martanin soji kan farmakin da aka yi musu".

Yayin da ake samun bata-kashi mai tsanani a baya, sai dai an rage ruwan wuta cikin sauri.

Yayin da ake fargabar cewa faɗan zai iya rikiɗe wa zuwa babban yaƙi, a halin yanzu akwai rashin shugabanci daga dukkan ƙasashen wajen ganin sun saduda daga rikicin.

A Thailand, akwai haɗakar gwamnati da ba ta da ƙarfi, wadda ke samun goyon bayan tsohon ɗansiyasa Thaksin Shinawatra.

An yi imanin cewa Thaksin yana da alaƙa da Hun Sen da iyalansa, kuma yana jin an yaudare shi da matakin da Hun Sen ya ɗauka na ƙwarmata wata tattauna da suka yi - da ta janyo aka dakatar da ƴarsa, Paetongtarn Shinawatra a matsayin Firaminista.