Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mulkin mallakan da ya hargitsa rayuwa a Gabas ta Tsakiya
- Marubuci, Tom Bateman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC na Gabas ta Tsakiya
Iyayen Eid Haddad suna matasa, lokacin da suka ga yadda Birtaniya ta yi amfani da cikakken ƙarfin da take da shi a Falasɗinu cikin 1938.
"Sun ga yadda sojoji ke shiga suna far wa mutane. Mahaifina ya faɗa mini cewa an fasa kan ɗaya daga cikin mutanen lokacin da aka doke shi da gudumar katako mai suna modaka da Larabci, ta kwankwatsa nama, inda ya riga mu gidan gaskiya," cewar Eid Haddad.
"Wani mutum da ɗansa suna shanya ganyen taba sigari don ya bushe. Su ma aka harbe su a gadon baya, suka mutu.."
"Duk lamari ya hargitse," in ji shi.
Mahaifansa na zaune ne a al-Bassa, wani ƙauyen Falasɗinawa da dakarun Birtaniya suka ɗauki matakin da a lokacin suka kira "ladabtarwa" a kan kowa da kowa.
Sojoji za su auka wa duk ƙauyukan yankin matuƙar dakarunsu suka fuskanci hare-hare daga 'yan tawaye masu gwagwarmaya da makamai a kan tuddai.
Eid Haddad na ba da labarin irin miyagun aika-aika da 'yan mulkin mallaka suka aikata ne ga wani sabon jerin shirye-shirye mai suna 'The Mandates' na BBC Radio 4 da ke Ingila, wanda aka fara gabatar da shi ranar Talata da karfe 4:00 na yamma agogon BST.
Yana tsokaci ne a kan yadda mulkin mallakar Birtaniya da Faransa a Gabas ta Tsakiya shekara 100 da ta wuce, ya yi tasiri a yankin cikin sigogin da har yau ana jin raɗaɗinsu.
A cikin jerin shirye-shiryen, mun ji daga masanan tarihi daban-daban; ƙwararru a kan lamurran da suka faru ƙarni guda da ya wuce a wurin da ya ƙunshi inda ake kira ƙasar Isra'ila a yanzu da Yankunan al'ummar Falasɗinawa da ke ƙarƙashin mamaya da Jordan da Lebanon da kuma Siriya.
Mun zanta da mata da maza kai tsaye waɗanda ruguntsumin tashin hankalin da ya taɓa nahiyar Turai da Gabas ta Tsakiya ya shafi rayuwarsu, har ma da ta 'ya'ya da jikokinsu a yau.
Na fara haɗuwa da Eid Haddad ne bara, lokacin da nake ɗauko rahotanni kan yunkurin da Falasɗinawa suke jagoranta na neman afuwa a kan zargin laifukan yaƙi da Birtaniya ta aikata.
Zamanin da take iko da yankin Falasɗin daga 1917 zuwa 1948.
Da nake zantawa da shi lokacin, a jerin tattaunawar wayar tarho daga gidansa a Denmark, ya riƙa labarta min yadda rayuwa ta kasance lokacin da yake yaro a Lebanon. Ana cikin fuskantar ƙarin zubar da jinin da danginsa suka tsallake rijiya da baya - har ma ya tilasta musu tserewa daga gidansu.
Kamar sauran mutane da dama, da na zanta da su saboda jerin shirye-shiryen, rayuwar mahaifansa lokacin da suke kan gaɓar ƙuruciyarsu. Zamanin mulkin mallakan Birtaniya da na Faransa da ya haddasa rikicin shekara da shekaru da tashin-tashinar ɓangaranci a Gabas ta Tsakiya.
Yarintarsa tana ƙunshe da rashin kwanciyar hankali mai cike da zubar da jinin da ya dabaibaye Gabas ta Tsakiya tsawon shekaru gommai, bayan manyan ƙasashen Turai sun yi watsi da ƙoƙarin shiga tsakaninsu, sun fice.
Wani masanin tarihi da muka zanta da shi ya faɗa mana cewa tarihin yankunan Gabas ta Tsakiya a zamanin mulkin mallaka, ya kasance ginshiƙi mai matuƙar tasiri ga "tarihin yanzu".
A lokacin Yaƙin Duniya na Daya, sa'ar da Birtaniya ta mamaye tare da ƙwace yankin daga Daular Usmaniyya da ta ɗauko durƙushewa, matakin da ya haifar da ƙaruwar mayaƙa masu gwagwarmayar ƙwatar 'yanci.
Ta ɗauki alƙawurra masu cin karo da juna game da makeken yankin ga Larabawa, da ke neman 'yancin kai, da kuma masu gwagwarmayar kafa ƙasar Isra'ila da ke neman samun ƙasar Yahudawa a yankin Falasɗin.
Birtaniya da Faransa sun yi ƙoƙarin ƙarfafa ikonsu a kan abin da ake kira "yankunan da suke iko ko Mandates" don tafiyar da su kamar yadda sabuwar ƙungiyar ƙasashen duniya - League of Nations - wadda manyan ƙasashen duniya biyu masu ra'ayin faɗaɗa iko suka mamaye.
Yankuna ikon Birtaniya da Faransa
A Falasɗinu, manufofin Birtaniya daga ƙarshen ƙarshe sun sanya ƙungiyoyin ƙwatar 'yancin kai arangama da juna, kafin ɓullo da wani mataki mai tsauri na yin dirar mikiya a kan juyin-juya-halin Larabawa a ƙarshen shekarun 1930.
Dakarun Birtaniya daga baya sun fuskanci tawaye daga mayaƙan sa-kai masu rajin kafa ƙasar Yahudawa zalla.
A lokacin da hukumomi suka mayar da hannun agogo baya ga jerin manufofin hargitsi, da suka kai Birtaniya ta ƙi cika alƙawurran da ta ɗauka a kan batun shigi da fice da kuma komar da wasu jiragen ruwa na mutanen da suka kuɓuta daga kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa, bayan tun farko sun tsere daga ƙasashen Turai da ke ƙarƙashin ikon Nazi.
"'Yan Birtaniya ba su san yadda za su tafi da lamuran ba," kamar yadda masanin tarihin Isra'ila Tom Segev ya faɗa min. "[Suna] lallaɓa Falasɗinawa tamkar mutumin da ke lallaɓa kyanwar da yake so. Abin jin daɗi ne ta samu yankin, amma bai kamata su zame mata matsananciyar rigima ba," ya ƙara da cewa.
A lokaci guda kuma Yankin ikon Faransa ya raba Lebanon daga Siriya don kafa wata muhimmiyar gaɓar teku da kuma ƙaƙaba wasu sabbin iyakoki a kan illahirin yankin a farkon shekarun 1920.
Kafin wani faɗan tawayen Larabawa wanda cikin matakai na rashin imani suka murƙushe shi.
Sun raba yankunan a kan tsarin ƙabilanci da addini, a abin da masanin tarihi James Barr ya faɗa mana cewa wani yunƙuri ne "kai tsaye kuma mai cike da son rai" na raba kan al'ummomi don a mulke su.
'Yan shekaru bayan Yaƙin Duniya na Biyu, Birtaniya da Faransa sun fice.
A Falasdinu, hukumomin London sun kwan da sanin cewa janyewarsu za ta mayar da rikicin kan iyakoki da ya ta'azzara zuwa cikakken yaƙi a yankin, don kuwa yayin da aka ayyana kafa ƙasar Isra'ila, sai sojojin Larabawa suka mamaye.
Mahaifan Eid Haddad sun tsere daga al-Bassa, ƙauyen da mayaƙan Yahudawa masu kayan sarki suka lalata.
A lokacin rikice-rikicen 1947-8, Falasɗinawa aƙalla 750,000 ne ko dai suka tsere ko kuma aka tilasta musu tserewa daga gidajensu, a abin da Falasɗinawa suke kira da 'Nakba' ko kuma 'bala'i'.
An haifi Eid kuma ya girma a wani sansanin 'yan gudun hijira na Falasɗinawa da ke Lebanon mai maƙwabtaka.
Yanayin jalli-joga na ɓangaranci tsakanin Kiristoci da Musulmai da aka bari sanadin mulkin Faransa a Lebanon ya ƙarasa tarwatsewa saboda ƙarin Falasɗinawa 'yan gudun hijira da suka kwarara.
Lamari ya sake ƙazancewa ne a lokacin tasowar rajin Kwatar 'Yancin Kan Falasɗinawa (PLO), ƙungiya mai gwagwarmaya da makamai da ta ƙaddamar da hare-hare a kan Isra'ila.
Kasar da ke da jami'ai masu ƙarfi waɗanda har a lokacin suke fifita ƙawance da Siriya da Masar a yankin mai rajin tabbatar da haɗin kan Larabawa - wannan wani gangami ne da ya samo asali daga yankunan da suka samu kansu a ƙarƙashin ikon Birtaniyda da Faransa.
Daga bisani Lebanon ta auka cikin yaƙin basasa na ɓangaranci.
Eid Haddad, wanda iyayensa Falasdinawa ne, Kiristoci, ya bayyana yadda Kiristocin Lebanon masu tsattsauran ra'ayin kishin ƙasa suka harbe ɗan'uwansa mai shekara 16.
Mayaƙan sa-kai na Phalangi sun riƙa far wa Falasdinawa, kuma suna kai hari a kan sansaninsu da ke arewa da birnin Beirut a 1975.
Bayan shekara guda kuma, da ƙyar ya tsallake rijiya da baya a wani kisan kare dangi. Ya bayyana yadda mayaƙa 'yan sa-kai suka yi amfani da ƙeta wajen keta mutuncin waɗanda suka kuɓuta cikin lamari na ban takaici.
Eid Haddad ya fada min yadda ya yi ta fama da alamomin larurar dimautar rayuwa na tsawon lokaci, abin da kuma ke da alaka da rayuwar da ya taso a cikinta tun yana yaro.
"Iyayena - ina jin sun kuma yi fama da larurar ɗimautar rayuwa saboda sun ga ɗumbin abubuwa tun suna ƙananan yara. Kuma ka yi tunani mahaifina, sai da ta kai dakarun sojin Birtaniya sun kama shi don su titsiye shi," kamar yadda ya ce, yana bayanin cewa sojojin Birtaniya sun ware mata da mazan da jami'an tsaro suka tsare a lokacin aika-aikar ƙauyen al-Bassa cikin 1938.
Mahaifinsa, sannan yana cike da ƙuruciya, ya fi ɗaukar kamannin mata, a cewar Eid Haddad, wanda wani mutum ya sanya shi ɓad da kama ta hanyar yin shiga tamkar 'yar budurwa.
"To, da haka suka rufe shi, aka rufe masa kai da ɗan kwali aka ba shi tufafi. Da haka, suka kuɓutar da shi daga fuskantar azabtarwa," in ji shi.
Gwamnatin Birtaniya ba ta taɓa amsa cewa ta tafka aika-aika a ƙauyen al-Bassa ba, wanda aka yi imani an kashe fiye da mutum 30.
Daga Turai, Eid Haddad ya bayyana yadda bai iya sake komawa mahaifarsa ba.
Ya ce: "ji nake yi kamar wani babban sashen jikina ne ya ɓata. Ina jin rayuwata tamkar wani tsibiri a tsakiyar teku, wanda gaba ɗaya komai baƙo ne a gare ni."