Ƙasarmu ta fuskanci tashin hankali - Shugaba Talon na Benin

Asalin hoton, BTV
Bayan shafe sa'o'i ba tare da an ji ɗuriyarsa ba, shugaban ƙasar Benin Patrice Talon ya bayyana a kafar talabijin inda ya yi wa al'ummar ƙasar jawabi, tare da bayyana cewa an daƙile yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi a ƙasar.
Ya ce "yanzu an shawo kan lamarin baki ɗaya" bayan yunƙurin da masu juyin mulki suka yi tun da farko.
"Ina so na yaba wa jajricewar da sojojinmu da jagororinsu suka nuna, waɗanda suka... ci gaba da zama masu biyayya ga ƙasa," in ji Patrice Talon wanda ya bayyana a kafar talabijin ba tare da alamar tashin hankali ba.
"Gaba ɗayanmu mun tsaya tsayin daka, muka sake karɓo yankunanmu sannan muka kakkaɓe wuraren da masu cin amana suka ja daga.
"Wannan jajircewa ta ba mu damar yin galaba a kan waɗannan mutane, sannan muka kare ƙasarmu daga faɗawa cikin annoba," kamar yadda Shugaba Talon ya bayyana.
Gwamnati ta ce ta daƙile yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka so su yi, awanni bayan wasu gungun sojoji sun bayyana cewa sun karɓe iko da ƙasar.
Fashe-fashe da harbe-harbe
Ya zuwa yammaci an ji ƙaran harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa a Cotonou, babban birnin ƙasar.
Ana kyautata zaton cewa fashewar ta samo asali ne daga wasu hare-hare ta sama.
Gabanin fashe-fashen bayanai sun nuna wasu jirage guda uku sun shiga Benin daga Najeriya mai maƙwabtaka.
Tuni jiragen suka koma Najeriya, inda biyu suka sauka a birnin Legas yayin da ɗaya daga ciki ya nufi jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.

Asalin hoton, BTV
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da rana, ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin ɗin ƙasar domin sanar da cewa yunƙurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi bai yi nasara ba.
Wani rukunin sojojin ƙasar ƙarƙashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ya sanar da hamɓare Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da tsarin mulki a kafar talabijin ɗin.
"Da safiyar Lahadi, 7 ga watan Disamban 2025, wasu tsurarin sojoji sun yi yunƙurin ƙwace mulki domin tayar da fitina a ƙasa da kuma ma'aikatu," a cewar Minista Alassane Seidou.
"Ganin wannan lamari, sai rundunar sojan Benin, kamar yadda suka sha rantsuwa, suka ci gaba da mara wa ƙasarsu baya. Matakin da suka ɗauka ya ba su damar shawo kan lamarin kuma suka daƙile yunƙurin."
A cewar sanarwar da suka karanta a kafar talabijin ɗin, sojojin sun ce Kanar Pascal ne zai jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin abin da suka kira Kwamatin Soja na Sake Gina Ƙasa.
Sun kuma sanar da dakatar da kundin tsarin mulkin ƙasar, da rusa gwamnati, da rusa jam'iyyun siyasa.
Wani saƙo daga ofishin jakandancin Faransa a Benin ya bayyana cewa an ji ƙarar harbe-harbe a kusa da gidan Shugaban Talon a Cotonou, yayin da sojoji ke iƙirarin juyin mulki.
Tun da farko wasu jami'ai na kusa da shugaban sun ce yana nan ƙalau, kuma sojojin ba su samu goyon bayan rundunar sojan ƙasar ba. Amma babu tabbas game da abin da ke faruwa yanzu haka.
Sun kuma ce yanzu komai ya lafa ta yadda sojojin ƙasar ne ke kula da tsaron Cotonou babban birnin da ma ƙasar baki ɗaya. An toshe tituna yayin da sojoji ke karakaina a wurare da dama.
"An shawo kan lamarin. Mafi yawan rundunar soja na goya wa shugaban baya - kuma muna ƙara shawo kan al'amuran," kamar yadda Ministan harkokin Waje Shegun Adjadi Bakari ya faɗa wa kamfanin labarai na Reuters.
Wata majiya a fadar shugaban ƙasar ta faɗa wa kamfanin labarai na AFP: "Wani ƙaramin rukunin sojoji ne da suka kama iko da gidan talabijin ɗin kaɗai. Birnin da ƙasar na hannun gwamnati baki ɗaya."
Ana kallon Benin da ke Afirka ta Yamma a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka mafiya kyawun tsarin dimokuraɗiyya, wadda ke da ta fi arzikin auduga a nahiyar amma kuma cikin mafiya talauci a duniya.
A watan Afrilun shekara mai zuwa ne Shugaba Talon zai sauka daga mulki inda zai kammala wa'adin mulki na biyu, kuma a lokacin ne za a yi sabon zaɓe.










