Juyin mulki 8 da aka yi a Najeriya

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Rahotannin da ke nuna cewa ana binciken wasu manyan sojoji su 16 dangane da zargin juyin mulki na ci gaba da jan hankalin ƴan Najeriya a soshiyal midiya.
Hedikwatar tsaro ta Najeriya dai tuni ta fitar da sanarwa inda ta musanta faruwar juyin mulki a Najeriyar.
Hedikwatar ta kuma faɗi cewa "binciken da ake yi da ya shafi manyan sojoji 16 wani abu ne da aka saba yi lokaci zuwa lokaci a cikin gida domin tabbatar da ɗa'a da ƙwarewar aiki a tsakanin sojojin."
To sai dai da alama ƴan Najeriya ba su gamsu da bayanan hedikwatar tsaron ta bayar ba.
BBC ta yi nazari dangane da juyin mulki daban-daban fiye da 8 da Najeriyar ta fuskanta daga 1960 zuwa 1999 da mutanen da aka zarga da kitsawa.
Chukwuma Kaduna Nzeogwu - Janairu 1966

Asalin hoton, Nigeria Archive
Patrick Chukwuma wanda aka fi sani da Kaduna Nzeogwu ya kasance Manjo kuma shi ne mutumin da ya kitsa juyin mulki na farko da aka yi a Najeriya a ranar 15 ga watan Janairun 1966, shekaru shida bayan samun ƴancin kan ƙasar.
Sakamakon juyin mulkin ne ya yi sanadiyyar mutuwar Firaiministan Najeriya na farko, Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa da firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.
Kuma bayan juyin mulkin ne sai Manjo Aguinyi Ironsi ya zama shugaban ƙasa inda ya kwashe watanni shida kafin shi ma a yi masa juyin mulki wanda Murtala Ramat Muhamamd ya jagoranta.
Daga baya an kama Manjo Nzeogwu inda aka ajiye shi a gidan yarin Kirikiri a Legas kafin daga bisani a mayar da shi gidan yarin Aba, inda ya zauna a can har zuwa lokacin fara yaƙin Biafra a 1967.
A watan Maris na 1967 ne kwamandan sojojin Biafra na lokacin, Odumegwu Ojukwu ya saki Nzeogwu, sai an kashe shi a yaƙin na basasa a ranar 29 ga watan Yulin 1967 a Nsukka da ke jihar Enugu.
Murtala Ramat Muhammed - Yuli 1966
Sakamakon fahimtar da ƴan arewacin Najeriya suka yi cewa ƴan kudu maso gabashin Najeriya ne suka kitsa juyin mulkin da ya yi sanadiyyar mutuwar manyan arewa, sai Lafatanar Kanal Murtala Ramat Muhammad ya jagoranci wani juyin mulkin na ramuwar gayya watanni shida bayan na farkon.
Murtala Muhammad wanda a lokacin yake muƙaddashin Laftanar Kanar a lokacin shi ne a gaba-gaba.
Kuma bayan an samu nasarar juyin mulkin ne Yakubu Gawon ya zama shugaban mulkin sojin Najeriya.
Sai dai saɓanin abin da ya samu Nzeogwu Kaduna na hukunci bai samu Murtala ba inda ya ci gaba da zama a aikinsa har ma daga baya shi kansa ya zama shugaban Najeriya.
To sai dai an kashe shi a wani yunƙurin juyin mulkin a ranar 13 ga watan Fabrairun 1976 wanda Bukar Suka Dimka ya jagoranta.
Joseph Nanven Garba - Yuli 1975

Asalin hoton, Photo12/Universal Images Group via Getty Images
A ranar 29 ga watan Yulin 1975 ne wata tawagar wasu ƙananan sojoji suka kitsa wani yunƙurin juyin mulki da ba a samu asarar rai ba.
Joseph Nanven Garba shi ne sojan da ya fito ya sanar da juyin mulkin a gidan Rediyo kuma ya sanar da Murtala Ramat Muhammad a matsayin sabon shugaban ƙasa da Olusegun Obasanjo a matsayin mataimaki, abin da ya sa ƴan Najeriya suka yi tsammanin shi ne jagoran masu juyin mulkin.
Juyin mulkin ya faru ne lokacin Yakubu Gawon ya tafi taron ƙungiyar tarayyar Afirka ta OAU a Uganda
Masu juyin mulkin sun ce sun haɓɓare Gawon saboda jan ƙafar da ya yi wajen komawa mulkin dimokraɗiyya.
Ƙarin sunayen sojojin da suka yi amo a juyin mulkin sun haɗa da Theophilus Danjuma da Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida da kuma Sani Abacha.
Bukar Suka Dimka - 1976
A ranar 13 ga watan Fabrairun 1975 aka samu wasu yaran sojoji da suka kira kansu "masu son kawo sauyi" suka yi yunƙurin haɓɓarar da gwamnati.
Jagoransu shi ne Laftanar Kanal Bukar Dimka wanda ya tsare motar da Murtala Muhammad yake ciki a kan hanya kuma ya kashe shi.
Dimka a sanarwar da ya yi a gidan rediyo ya zargi Murtala Muhammad da rashawa da cin hanci da rashin iya samar da mafita da kuma rauni a gudanawa.
To sai dai sojoji da dama ba su bari juyin mulkin ya yi tasiri ba inda tun daga gidan rediyon da ya yi jawabi aka fara tasa shi a gaba.
Makonni uku bayan al'amarin kuma jami'an tsaro suka kama shi a Abakaliki da ke jihar Ebonyi a kudu masu gabashin ƙasar.
Kuma daga ƙarshe an kotun soji ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar harbe su tare da wasu abokan juyin mulkin nasa guda shida.
A ranar 15 ga watan Mayun 1976 ne aka kashe su gabaɗaya su bakwai.
Juyin mulkin 1983
Shi wannan juyin mulkin na 1983 wanda ya tumɓuke Alhaji Shehu Shagari ba shi da jagora na kai tsaye da za a iya kama sunansa.
Sai dai kuma mutumin da ya zama shugaban ƙasa bayan nan shi ne Muhammadu Buhari.
Sauran mutanen da sunayensu suka yi amo sun haɗa da Kanal Tunde Ogbeha da Birgediya Ibrahim Baƙo waɗanda su ne suka shiga fadar shugaban ƙasa suka kama Alhaji Shehu Shagari, abin da ya janyo musayar wuta da dakarun fadar shugaban ƙasa har ya yi sanadiyyar mutuwar Baƙo.
Muhammadu Buhari wanda daga baya ya zama zaɓaɓɓen shugaban Najeriya a 2015 ya ce babu hannunsa a juyin mulki duk da cewa wasu sun ce yana da masaniya.
Ibrahim Babangida - 1985

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Kamar abin da ya faru a juyin mulkin 1975, juyin mulkin na ranar 27 ga watan Agustan 1985 bai janyo zubar da jini ba.
Ibrahim Badamasi Babangida wanda shi ne ya jagoranci juyin mulkin shi ne shugaban ma'aikatan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a lokacin.
Kuma Babangida ya kasance a matsayin shugaban ƙasa tun daga 1983 har zuwa 1993, duk da cewa an yi wani yunƙurin juyin mulki a 1990 wanda Gideon Orkar ya jagoranta.
Gideon Gwaza Orkar - 1990
Manjo Gideon Orkar shi ne sojan da ya jagoranci juyin mulkin 1990 da manufar hamɓarar da Ibrahim Babangida a ranar 22 ga watan Afrilu.
Orkar dai ya samu narar mamaye hedikwatar sojoji da Dodon Barak inda shugaban ƙasa ke zaune to amma Shugaban ƙasar ya kuɓuta daga harin sojojin.
Sakamakon rashin nasarar juyin mulkin, aka tsare Orkar da wasu sojoji masu yawa ciki har da fararen hula, inda aka yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbewa a ranar 27 ga watan Yulin 1990.
Sani Abacha - 1993

Asalin hoton, Nigeria High Commission
Shi ma wani juyin mulkin ne da bai haddasa zubar da jini ba wanda wasu ke kira "na cikin gida" kuma ya faru ne a ranar 17 ga wtan Nuwamban 1993.
Sani Abacha wanda a lokacin Manjo Janar ne a rundunar sojin Najeriya kuma ministan tsaro, shi ne ya turo Chief Ernest Shonekan wanda Ibrahim Babangida ya ɗora lokacin da zai bar mulki sakamakon matsin lamba.
Abacha ya yi mulki tun daga wannan lokaci har zuwa ranar 8 ga watan Yunin 1998, lokacin da ya rasu.
Bayan mutuwar Abacha ne kuma sai Janar Abdussalam Alhaji Abubakar ya zama shugaban ƙasa na ɗan wani taƙaitaccen lokaci kafin ya miƙa mulki ga Cif Olusegun Obasanjo a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 1999.






