Faransa ta maye gurbin Nkunku da Kolo a Gasar Kofin Duniya a Qatar

Asalin hoton, Getty Images
Faransa ta maye gurbin Christoper Nkunku da mai taka leda a Eintracht Frankfurt, Randal Kolo Muani a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar.
Nkunku mai wasa a RB Leipzig ya ji rauni a lokacin atisaye ranar Talata tare da tawagar, wanda zai yi jinya har bayan kammala babbar Gasar tamaula ta duniya..
Kolo Muani ya ci kwallo takwas a wasa 23 a Frankfurt a kakar nan a Bundesliga.
Dan kwallon mai shekara 23 ya yi wa tawagar Faransa wasa biyu a karawa da Australia da Denmark a Nations League a watan Satumba.
Nkunku ya zama na baya-bayan nan daga tawagar Faransa da ba zai buga Gasar Kofin Duniya ba, bayan Paul Pogba da N'Golo Kante da kuma Presnel Kimpembe.
Har yanzu dan wasan Manchester United, Raphael Varane bai murmure ba, wanda Faransa ta je da shi Qatar.
Tawagar da Didier Deschamps ke jan ragama za ta sauka a Qatar ranar Laraba.'
Za ta fara wasa ranar 22 ga watan Nuwamba da Australia a rukuni na hudu da ya hada da Denmark da kuma Tunisia.
Faransa ce mai rike da kofin da ta lashe a Rasha a 2018.










