Manyan abubuwan da aka fi tattaunawa gabanin zaɓen gwamnan Anambra

Hotunan Chukwuma Soludo da Nicholas Ukachukwu da Jude Ezenwafor da George Moghalu

Asalin hoton, Soludo/Ukachukwu/Ezenwafor/Moghalu/Facebook

    • Marubuci, Chukwunaeme Obiejesi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

An shirya gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Anambra a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Gwamnan yanzu, Chukwuma Soludo wanda tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ne zai fafata da 'yan takara 15 domin neman mulkin jihar karo na biyu.

Jihar Anambra na da matuƙar muhimmanci a Najeriya saboda tana daga cikin jihohin da ke haɗa kudu maso gabas da sauran sassan ƙasar.

Saboda haka mutane da yawa na sa ido sosai kan abin da ke faruwa a jihar.

Yayin da ranar zaɓe ke ƙaratowa, BBC za ta bayyana a wannan labarin muhimman abubuwan da za su iya shafar zaben da abin da ya kamata ku sani.

Jarabawar farko ga sabon shugaban INEC

Farfesa Joash Amupitan

Asalin hoton, Joseph Ayo Babalola University

Bayanan hoto, Wanan ne zaɓe na farko da za a gudanar a ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban Inec Joash Amupitan

Wannan zaben zai zama babbar jarabawa ko aiki na farko ga sabon shugaban shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Joash Amupitan. saboda shi ne zaɓe na farko da za a gudanar gudanar a ƙarƙashin jagorancinsa.

Amupitan, wanda Farfesa ne a fannin Shari'a kuma Babban Lauya na Najeriya (SAN), ya karbi ragamar aiki daga farfesa Mahmood Yakubu, wanda lokacin shugabancinsa aka samu wasu matsaloli kamar "matsalar na'ura" da ta kusan kawo tangarɗa a babban zaben ƙasa na 2023.

A jawabin da ya gabatar a lokacin tantance shi a Majalisar Dattijai, Amupitan ya yi alƙawarin cewa shugabancinsa zai karfafa gaskiya da adalci a zaɓukan Najeriya.

Duk ido na kan shi yanzu, musamman a wannan zaɓen na Anambra, don a ga ko zai cika alkawuransa.

Ƴan takara 16

Hukumar INEC ta amince da 'yan takara 16 da suka haɗa da mata 2 da maza 14 da za su fafata, ciki har da gwamnan jihar, Chukwuma Soludo, wanda ke neman mulkin jihar karo na biyu.

Wasu daga cikin 'yan takarar sun tsaya takara a zaɓen da ya gabata, kuma suna fatan a wannan karon za su yi nasara.

Sunayen 'yan takara da jam'iyyunsu sun haɗa:

  • Onyeeze Chidi Charles – Jam'iyyar A
  • Nweke Ezechukwu Japhet – Jam'iyyar AA
  • Ifemeludike Chioma Grace – Jam'iyyar AAC
  • Nwosu Chima John – Jam'iyyar ADC
  • Nicholas Ukachukwu – Jam'iyar APC
  • Soludo Charles Chukwuma – Jam'iyyar APGA
  • Otti Cyprain Echezona – Jam'iyyar APM
  • Nweke Chrispopher Chukwudubem – Jam'iyar APP
  • Okeke Chika Jerry – Jam'iyyar BP
  • Moghalu George Nnadubem - Jam'iyyar LP
  • Onyejegbu Geoffrey – Jam'iyyar NNPP
  • Ndidi Christy Olieh – Jam'iyyar NRM
  • Ezenwafor Jude – Jam'iyyar PDP
  • Chukwurah Vincent – Jam'iyyar SDP
  • Chukwuma Paul Chukwuka – Jam'iyyar YPP
  • Ugwoji Uchenna Martin – Jam'iyyar ZLP

Jami’an tsaro fiye da 50,000

Rundunar 'Yansanda ta Najeriya ta ce za ta tura jami’ai 45,000 domin tabbatar da tsaro a lokacin zaɓen.

"Dukkan ƙungiyoyin sa kai da sauran hukumomin jihohi ba za su samu damar taka rawa a wannan zabe ba," in ji Abayomi Shogunle, shugaban sashen shiryawa da Kula da zaɓe na INEC.

Shogunle ya bayyana hakan ne a wani taro na musamman da INEC ta shirya tare da jami'an tsaro domin shirya wa zaɓen Anambra.

Ya ce aikin 'yansanda a jihar zai fara tun daga farkon watan Nuwamba domin tabbatar da cewa duk wanda zai yi yunkurin kawo tashin hankali za a dakile shi, a kama, sannan a gurfanar da shi.

Haka kuma, Ahmed Audi, babban kwamandan hukumar tsaro da kula da lafiyar jama'a ta NSCDC, ya ce za su tura ma'aikatan hukumar 10,250 domin samar da tsaro a lokacin zaɓen.

Tsaro da tattalin arziki su ne manyan batutuwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana kimiyyar siyasa sun ce, babban abin da za a fi tattaunawa a wannan zaɓen shi ne lamuran tsaro da tattalin arzikin jihar Anambra.

Jihar ta sha fama da tashe-tashen hankula a 'yan shekarun nan sakamakon ayyukan wasu 'yan bindiga da ba a san su wane ne ba.

An samu rahotannin satar mutane domin karbar kuɗin fansa da kashe-kashen al'umma da kashe-kashe domin tsaface-taafacen samun kuɗi da sauran laifukan tayar da hankalin al’umma.

A lokacin yakin neman zaɓen gwamna na 2021, 'yan bindiga sun sace Obiora Agbasimelo, dan takarar jam'iyyar LP kuma har yanzu babu wanda ya san halin da yake ciki.

Haka kuma, ƙasa da shekara guda bayan zaɓen, a watan Satumba 2022, 'yan bindiga sun kai hari kan Ifeanyi Ubah, wanda ya tsaya takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar YPP inda suka kashe jami'an tsaronsa na 'yan sanda. shi kuma abin da ya ceci rayuwarsa a lokacin shi ne harsashe ba ya huda motarsa.

A farkon wannan shekarar, gwamnatin jihar ta ƙirƙiro wata sabuwar rundunar tsaro da ta kira 'Agunechemba' sannan ta ƙaddamar da "Operation Udogachi" domin yaƙi da rashin tsaro da ya addabi jihar.

"Gaba ɗaya tsarin tsaro a Jihar Anambra kamar ba ya aiki. Mutanenmu da ke kasuwanci a waje ba za su iya komawa gida ba, kuma hakan na shafar tattalin arziƙin jihar," in ji George Muoghalu, ɗan takarar LP a wata hira da BBC Pidgin.

Jami'an 'yansandan Najeriya sun ce za su tura 'yan sanda 45,000 domin tabbatar da tsaro a lokacin zaben, yayin da Hukumar NSCDC za ta tura ma'aikatanta 10,250.

A ɓangaren tattalin arziki, lamarin zaman gida duk ranar Litinin a jihar musamman a birnin kasuwanci na Onitsha, har yanzu babbar damuwa ce.

An saka wannan umarnin zaman gidan ne saboda ƙungiyar IPOB, wadda ke fafutukar kafa jamhuriyar Biyafara mai cin gashin kanta daga kudu maso gabashin Najeriya.

An fara aiwatar da umarnin tun a watan Agustan 2021 don nuna adawa da kama shugaban ƙungiyar Nnamdi Kanu da gwamnati ta yi a Kenya sannan aka mayar da shi zuwa Najeriya domin gurfanar da shi a kotu.

Duk da cewa IPOB ta soke umarnin zaman gida, da yawa daga cikin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke biyayya ga Kanu na ci gaba da tilasta wa mutane, dalilin da ya sa mutane suke jin tsoro su fito a ranakun Litinin.

Gwamna Soludo ya yi ƙoƙarin tilasta wa mutane su buɗe shagunansu a ranakun Litinin kuma ya yi barazanar rufe shagunan duk wanda ya ki bin umarnin, amma tsoro ya hana mutane su saɓa wa umarnin zaman gida.

Wannan matsala ta janyo asarar kuɗaɗe da yawa ga Jihar Anambra da yankin kudu maso gabas, kuma ta shafi matsayin Onitsha a matsayin babbar cibiyar kasuwanci a Najeriya.

Mutumin da zai lashe wannan zaɓe zai fuskanci babban aiki domin sauya wannan yanayi.

Tarihin zaɓen jihar Anambra tun daga shekarar 1999

Jihar Anambra na da matsayi na musamman a harkar zaɓe a Najeriya saboda ita ce jiha ta farko da ta fara gudanar da zaɓukan da ake yi ba tare da sauran zabukan kasa baki daya ba tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999.

Abun ya fara ne lokacin da Kotun ƙoli ta ayyana Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a shekarar 2003, shekaru uku bayan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta riga ta bayyana Chris Ngige na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma aka rantsar da shi.

Obi ya kai ƙara kotu inda kotu ta yanke hukunci cewa lokacin mulkinsa na shekaru hudu zai fara ne daga ranar da aka rantsar da shi a matsayin gwamna.

Tun daga wannan lokaci, jihohi da dama da suka samu irin wannan lamarin suka fara samun jadawalin zaɓe daban da lokacin zabukan gama gari da Najeriya ke gudanarwa.