Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ederson ba zai buga wasan ƙarshe na Premier League na FA Cup ba
Mai tsaron ragar Manchester City Ederson ba zai buga wasan ƙarshe na Premier League da FA Cup ba saboda rauni a saman idonsa.
Golan mai shekara 30 bai ji daɗi ba lokacin da aka cire shi a wasan Man City da Tottenhma ana minti na 69 bayan sun yi karo da ɗan wasan Tottenham Cristian Romero.
A ranar Lahadi City za ta karɓi baƙuncin West Ham, inda idan suka yi nasara - ko kuma suka tashi da sakamako iri ɗaya da Arsenal - za su ɗauki kofin karo na huɗu a jere.
Sai kuma ranar 25 ga watan Mayu City za ta gwabza da Manchester United a wasan ƙarshe na FA a filin wasa na Wembley.
Stefan Ortega, wanda ya hana ƙwallaye da dama shiga ragar City, shi ne zai tsare raga a wasannin biyu a madadin Ederson ɗan ƙasar Brazil.
Ortega ya buga wasa a dukkan zagayen gasar FA Cup da Carabao a kakar wasa biyu da suka wuce, kuma da alama shi ne zai buga wasan na Wembley ko da a ce Ederson ya warke.