Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kasafin kuɗin Tinubu zai iya farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya?
- Marubuci, Rabiatu Kabir Runka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa kasafin kuɗi na 2025 da ya gabatar a gaban majalisar dokokin ƙasar ranar Laraba da "Farfaɗowa: Tabbatar da Zaman Lafiya, da Gina Rayuwa".
Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 47.9, wanda ya na shekarar da ta gabata da kashi 36.8 cikin 100. Shi ne na biyu da Tinubu ya yi tun bayan rantsar da shi a watan Mayun 2023.
An dai ɗora kasafin kuɗin na 2025 na Najeriya ne a kan dala 75 a kan kowacce gangar ɗanyen mai guda kuma ana sa ran Najeriyar za ta samar da gangar ɗanyen man fiye da miliyan biyu duk rana a shekarar mai kamawa.
Shugaba Bola Tinubu ya shaida wa majalisun dokokin cewa "muna fatan samun naira tiriliyan 34.82 ta hanyar kuɗin shiga domin zuba wa a kasafin".
Sai dai kuma ya ce kasafin na da giɓin naira tiriliyan 13.08 wato kashi 3.08 cikin 100 na jimillar kasafin, yayin da ake hasashen gwamnatin za ta ciyo bashin tiriliyan 13 a cikin gida da waje domin cike giɓin.
Ɓangarorin da suka samun kaso mai yawa
Tsaro - naira tiriliyan 4.91
More rayuwa - naira tiriliyan 4.06
Lafiya - naira tiriliyannaira tiriliyan 3.52
Ilimi - naira tiriliyan 3.52
'Da kamar wuya'
A cikin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya ce tattalin arziƙin Najeriya ya samu haɓaka da kashi 3.46 cikin 100 a kaso na uku cikin huɗu na shekarar 2024, fiye da 2.54 a irin wannan lokacin a 2023.
Ya ƙara da cewa asusun Najeriya na ƙasar waje yanzu ya kai kusan dala biliyan 42, "wanda ya samar da kariya daga duk wata komaɗar tattalin arziƙi da ka iya tasowa".
Sai dai masana tattalin arziƙi a Najeriya na ganin babu wani tabbas ko kasafin kudin zai iya farfado da tatattalin arziƙin ƙasar kamar yadda gwamnatin ta Tinubu ke so 'yan ƙasa su amince.
"Kasancewar tattalin arziƙin Najeriya na cikin rashin lafiya, yana kuma samun koma-baya a kowane lokaci," in ji Dr Murtala Abdullahi Ƙwara masanin tatattalin arziƙi na Jami'ar Umaru Musa Ƴar'adua da ke jihar Katsina.
Ya ƙara da cewa da wuya kasafin kudin na 2025 ya iya farfado da tattalin arziƙin Najeriya. "Idan aka kalli alƙalumman da ake da su a ƙasa za a iya cewa da kamar wuya.
"Wasu alƙaluman da aka sanya cikinsa abu, da yawansu ba haka suke ba a harkar tatattalin arziƙi ta zahiri. Farashin dala da kuma yadda ake sayar da mai a yanzu da kuma adadin man da ake iya haƙowa a yanzu, duka hasashe ne kawai."
Dr. Ƙwara ya ce hasashen da aka yi cikin kasafin kuɗi kan canjin dalar Amurka kan N1,400, "zai yi wahala a iya samun haka saboda idan aka yi la'akari da farashin da yanzu dalar take kai, kuma ba ta fara yin ƙasa ba duk da cewa an kusa shiga shekarar".
Ko me zai faru idan aka kasa cim ma hasashen da aka yi?
"Abin da zai faru shi ne, za a iya rasa damar aiwatar da kasafin kuɗin, wato duk abin da aka ce za a yi da kasafin kuɗin ba za a yi ba har sai an sake nemo hanyar da za a cike giɓin, ko da ta hanyar ciwo bashi ne," cewar Dr. Ƙwara.
Masanin ya ce Najeriya ta jima cikin ƙangin bashi. Amma ya ce ba kowane bashi ne yake zama illa ba, yana mai cewa ya danganta da yadda aka yi amfanin da kudin da aka ciyo bashin.
To mece ce matsalar Najeriya game da bashin?
"Matsalar Najeriya ita ce, ba a yin abin da ya dace da kudin da ake amsowa idan aka yi la'akari da ƙididdigar da ake da ita. Misali, me ya sa za ka ciwo bashi saboda saya wa ƴan majalisa motoci ko kuma wasu abubuwa?"