Gareth Bale ya yi retiya daga kwallon kafa

Kyaftin dan Wales Gareth Bale ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekara 33. Dan wasan wanda ya taka rawar gani ta sanar da haka ne a shafukan sada zumunta.
Shi ne dan wasan da fi rike mukamin kyaftin ga kasarsa a wasannin 111 kuma ya sanar da haka ne a shafukan sada zumunta.
Bale, wanda ya lashe gasar zakarun Turai sau biyar tare da Real Madrid, za a iya cewa shi ne dan wasan kwallon kafa daya fi shahara daga yankin Wales.
"Bayan na yi nazari sosai, ina son na sanar da yin murabus nan take daga wasan kwallon kafa a wata kungiya da kuma kasa da kasa," In ji Bale .
"Ina farin ciki matuka da na cimma burinna na buga wasan da nake kauna ."
Bale wanda haifaffen Cardiff ne ya taka leda a Southampton da Tottenham Hotspur da kuma Real Madrid kafin ya koma kungiyar Los Angeles FC ta Amurka
Shi ne ya kasance gwanin kasarsa yayin da suka kai ga gasar cin kofin nahiyar Turai a 2016 da 2020 kafin ya jagoranci Wales a gasar cin kofin duniya a Qatar a 2022 a karon farko tun bayan 1958











