Potter na ganawa da West Ham kan maye gurbin Lopetegui

Harry Potter

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

An bayar da rahoton cewar Graham Potter na tattaunawa da mahukuntan West Ham United, domin maye gurbin Julen Lopetegui.

Potter, tsohon kociyan Brighton, mai shekara 49 bai da wata ƙungiyar da yake horarwa tun bayan da Chelsea ta kore shi a Afirilun 2023.

Ƙungiyar Stamford Bridge ta raba gari da Potter, bayan wasa 31 da ya ja ragama a yarjejeniyar kaka biyar da ya rabbata hannu daga baya aka soke ta.

Tun da aka fara kakar bana, Lopetegui ke fuskantar kalubale wanda ya maye gurbin David Moyes.

An yi tsammani ɗan kasar Sifaniya zai kai West Ham kololuwa a fannin tamaula, amma sai yake cin karo da cikas, duk da miliyoyin ƙudi da aka bashi ya sayo sabbin ƴan ƙwallo.

Lopetegui ya kara shiga matsi, sakamakon ƙwallaye da yawa da Liverpool da Manchester City suka zura a ragar West Ham.

West Ham ta kashe kusan £130million wajen sayen ƴan wasa tara, amma duk da haka tana ta 14 a kasan teburin Premier League, bayan kammala wasan mako na 20.

Cikin waɗanda ta saya a bana har da Niclas Fullkrug daga Borussia Dortmund kan £27million, wanda kawo yanzu ƙwallo biyu ya ci.

Haka kuma ta dauki masu tsare baya daga Nice, Jean-Clair Todibo da ke wasan aro da kuma Maximilian Kilman kan £40million

West Ham za ta fafata da Aston Villa a FA Cup ranar Juma'a daga nan ta buga wasan hamayya da Fulham da kuma Crystal Palace a Premier League.