Me dokokin Najeriya suka ce game da satar jin wayar wani?

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Har yanzu ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a Najeriya game da iƙirarin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, mallam Nasir El-Rufai na satar jin wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai El-Rufai cikin wata hira da gidan talbijin na Arise ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu ne ya bayar da umarnin kama shi a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Abuja bayan komawa ƙasar da ƙasashen waje.

Da mai gabatar da shirin ya tambaye shi hujjarsa sai ya ce daga satar jin wayar Ribadun ne aka tabbatar da hakan.

''Sun ɗauka su kaɗai ne suke satar jin wayar mutane, to mu ma muna da masu yi mana aikin satar jin wayarsu, kuma muna yi'', a cewar El-Rufai.

Wannan batu dai ya ɗauki hankali ƴanƙasar da dama, inda masana ke bayyana muhawara kan lamarin.

Mallam Nuhu Ribadu ne babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, wanda ɗaya daga cikin muhimman muƙamai ne a fannin tsaron ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta kai El-Rufai kotu kan lamarin

Bayan yamutsa hazo da kalaman na El-Rufai suka yi, musamman a ranakun ƙarshen mako, a ranar Litinin gwamnatin Najeriya ta shigar da shi ƙara a gaban kutun tarayya bisa zargin sa da satar jin wayar Ribadun.

A cikin ƙarar da gwamnatin ta shigar, ta ce "Kai, Mallam Nasiru El-Rufai, ka amince a hirar da ka yi cewa kai da abokan aikinka kun naɗi wayar Nuhu Ribadu ba tare da saninsa ba".

Wannan ya saɓa da sashe na 12 (1) na dokar daƙile laifukan Intanet ta 2024.

A tuhuma ta biyu kuma gwamnatin tarayya na zargin Nasir El-Rufai da sanin wasu da ke naɗar wayar mutane ba bisa ƙa'ida ba amma bai kai ƙarar su ga hukumomin tsaro ba.

Takardar ƙarar ta ce "wannan ya saɓa wa sashe na 27 (b) na dokar hanawa da daƙile laifukan Intanet, wanda hakan laifi ne ƙarƙashin dokokin Najeriya.

Me dokar daƙile laifukan Intanet ta ce?

Dangane tanadin da dokokin Najeriya suka yi kan satar jin wayar mutane ba tare da saninsu ba, BBC ta tuntuɓi Barista Abba Hikima Fagge wani lauya mai zaman kansa a ƙasar, wanda ƙwararren masanin dokokin ƙasar ne.

Lauyan ya kuma ce a ƙarƙashin dokokin Najeriya laifi ne satar jin wayar wani.

Masanin dokokin Najeriya ya ce dokoki da dama ne suka haramta satar jin wayar mutane.

  • Kundin tsarin mulki

Abba Hikima ya ce da farko dai batun satar jin wayar wani ba tare da saninsa ba, kundin tsarin mulkin ƙasar ne ya zo da haramcinsa ƙarƙashin sashe na 37.

''Kuma a cikin sassan 12 da suka yi magana game da kare ƴancin ɗan'adam a cikin kundin tsarin mulkin ƙasar, kusan kowane da aka yi magana a kansa an yi togaciya, amma sashe na 37 ba shi da wannan togaciyar'', in ji shi.

Lauyan ya ce abin da sashe na 37 ya ce shi ne ''an haramta sauraron wayar mutane ba tare da saninsu ba ko karanta saƙonnin da aka tura ta cikin wayarsu''.

  • Dokar daƙile laifukan Intanet ta 2024

Masanin dokokin Najeriyar ya ce dokar daƙile laifukan intanet da aka sabunta a 2024, wato Cybercrime Act 2024.

''Ita wanna doka sashenta na 12 ya ce haramun ne mutum ya yi satar jin hirar mutane da suka yi ta waya'', in ji shi.

Haka kuma Abba Hikima ya ce sashe na 27 na wannan doka ya yi tanadin cewa yin mu'amala da wanda yake satar jin wayar mutane ma laifi ne.

''Ba ma kai ka saurara ba, a’a, yin mua'amala da mutumin da yake satar jin wayar mutane, matuƙar ka san yana yi to laifi ne'', in ji shi.

  • Dokar NCC ta 2003

Haka kuma lauyan ya ce a ƙarƙashin dokar hukumar sadarwar ƙasar wato, NCC 2003 Act, nan ma laifi ne satar sauraron jin wayar mutane.

''A ƙarƙashin wannan doka ma laifi ne ka yi satar jin wayar mutane'', in ji lauyan.

Wane hukunci doka ta tanatar wa wanda ya yi laifin?

Barista Abba Hikima ya ce ƙarƙashin dokokin Cybercrimes Act, akwai hukunce-hukunce masu tsauri da wanda aka samu da aikata laifin.

Ya kuma ce hukuncin ya danganta da abin da mutum zai yi da hirar da ya saurara.