Amurka da Jamus na shirin aika wa Ukraine tankokin ƴaƙi

.

Asalin hoton, Reuters

Bayan watanni na nuna rashin kulawa, an ruwaito cewa Amurka da Jamus na shirin aika wa Ukraine tankokin ƴaƙi, a wani abu da Kyiv take fatan zai kawo sauyi a faɗa da take yi da Rasha.

Ana sa ran gwamnatin Shugaba Joe Biden na Amurka za ta sanar da shirinta na aika tankokin yaƙi guda 30 ƙirar 30 M1 Abrams. Shi ma shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yanke shawarar aika tankoki 14 masu suna Leopard 2.

An ruwaito cewa zai yi jawabi gaban majalisar dokoki da safiyar ranar Laraba. Jakadan Rasha a Amurka ya ce labarin wani yunkuri ne na ɓata ran ƙasar.

Mai magana da faɗar Kremlin ya ce yunkurin da Jamus ke yi na aika tankokin yaki ba zai amfane su ba haka kuma zai dagula harkokin dangantaka tsakanin ƙasar da Rasha.

Jami'an Ukraine sun ce suna cikin buƙatar agajin gaggawa na manyan makamai, inda suka ce ƙarin makaman yaƙi za su taimaka wa Kyiv sake kwace ikon yankunanta da ke hannun Rasha.

Sai dai kafin yanzu, Amurka da Jamus sun tsaya kan matsayarsu duk da irin sukar cikin gida da kuma waje da ake musu na yunkurin aika wa Ukraine tankokin yaki.

Washington ta ce tana aikin horarwa da kuma gyara tankokin yakin masu fasahar zamani na Abram.

'Yan ƙasar Jamus sun jure tsawon watanni na kace-nace kan harkokin siyasa a daidai lokacin da ake nuna damuwar cewa aikewa da tankokin yaƙi zai ƙara dagula rikici sannan hakan zai sa kungiyar Nato ta zamo mamba ta kai-tsaye a yaƙin da ake yi da Rasha.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafafen ƴaɗa labarai a Amurka sun ruwaito cewa gwamnatin ƙasar za ta yi sanarwa kan aika tankokin yaƙin Abram zuwa Ukraine a ranar Laraba, inda wani jami’i da ba a bayyana sunan shi ba ya ce tankokin za su kai akalla 30.

Sai dai, ba a bayyana takaimamen lokacin aika su ba, inda tankokin yakin na Amurka za su iya kai watanni kafin isa filin daga.

An ruwaito cewa hukumomi a Jamus sun nace cewa za su iya aika tankokin ne kawai na Leopard 2 zuwa Ukraine, idan Amurka ma ta yadda ta tura nata.

"Idan Jamus ta ci gaba da cewa ba za ta tura tankokin yaki ba har sai Amurka ta aika nata, to za mu tura tankokin Abram,’’a cewar sanata Chris Coons na jam’iyyar Democrat wadda kuma makusancin shugaba Biden ne.

Tuni Birtaniya ta ce za ta aikawa Ukraine tankokin yaƙi na Challenger 2.

Polan na ɗaya daga cikin ƙasashen Turai 16 kuma mamba a kungiyar Nato da ta mallaki tankokin yaƙin Jamus ƙirar Leopard guda 2 – tana matsawa na ganin an aika su zuwa Ukraine, sai dai, fitar da su na buƙatar amincewar Berlin.

Ukraine ta ce zai yi wuya ta iya samun tankoki yaƙi na zamani guda 300 da ta ce tana buƙata domin samun nasara a yaƙin.

Sai dai, idan ƙasashen yamma guda shida suka ba ta tankoki guda 14 kowannen su, to hakan zai iya kai tankokin zuwa 100 – wanda kuma zai iya kawo sauyi a faɗa da take yi da Rasha.

Ana ganin tankokin yaƙin ƙasashen yamma – wanda suka kunshi Challenger 2 na Birtaniya da Leopard 2 na Jamus da kuma Abrams na Amurka – a matsayin na gaba masu karko fiye da na takwarorinsu na lokacin mulkin Soviet kamar ubiquitous T-72.

Tankokin za su taimaka wajen ƙare yankunan Ukraine.

Sai dai tankokin yaƙi na zamani na ƙasashen yamma ba za su iya kare komai ba saboda an ga hakan a karan kansu.

A makonnin baya-bayan nan, an samu sauyi a kan irin manyan makamai da ƙasashen yamma ke samarwa – wanda ya haɗa da motoci masu sulke da motocin atilari da kuma harsasai.

Idan aka haɗa wannan duka, akwai irin makamai da ya kamata a samar waɗanda za su iya kawo nakasu ga Rasha da kuma sake kwace ikon yankuna da ke hannunta.

Idan aka horar da dakarun Ukraine sannan aka samar da makamai a kan lokaci, hakan zai iya su kare kansu daga duk wata barazana. Wani abu da dakarun suka rasa shi ne makaman yaki na sama.

Ukraine na ta yin ƙira ga ƙasashen yamma da su samar mata da jiragen yaƙi na zamani tun soma yaƙin. Zuwa yanzu, babu wani jirgi da aka aika mata.

Duk da cewa babu wani martani a hukumance daga gwamnatin Jamus, amma Marie Agnes Strack-Zimmermann na jam’iyyar FDP masu ra’ayin kawo sauyi, wacce ke jagorantar kwamitin tsaro na majalisar dokokin ƙasar, ta yi maraba da rahotannin.

"Matakin yana da wahala, an ɗauki lokaci mai tsawo, amma a ƙarshe ba a kaucewa hakan ba, inda ta ce hakan zai kawowa ‘yan Ukraine mafita.’’

.

Ƙawayen ƙasashe, sun nuna damuwa kan yadda Jamus ta nuna halin ko-in-kula kan buƙatar aika wa Ukraine motocin yaƙi a baya-bayan nan.

Tun da farko, ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius, ya ce Berlin ta bai wa wasu ƙasashe damar horar da 'yan Ukraine wajen yadda za su yi amfani da tankokin yakin Leopard 2, sai dai, bata aike da nata tankokin ba.

Shugaban ma'aikata na faɗar shugaban ƙasar Ukraine, Andriy Yermak, a ranar Talata ya yi kira ga ƙasashen yamma da su bai wa Kyiv ɗaruruwan tankokin yaƙi domin tarwasa Rasha.

"Tankokin yaki na da muhimmanci ga Ukraine don komawa kan iyakokinta na 1991,'' in ji Andriy , a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Telegram.

Jakadan Rasha a Washington, Anatoly Antonov, ya rubuta a shafinsa na Telegram cewa: "Idan Amurka ta yanke shawarar aike da tankokin yaƙi, kare matakin da ce-ce-ku-ce kan 'makama kariya' ba zai yi aiki ba.

"Wannan zai ƙara harzuka gwmanatin Rasha.''