Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda tabar wiwi da dafin macizai suka kara wa yakin neman zaben Kenya armashi
George Wajackoyah, wanda a baya ya kasance wani karamin yaro da ke gararamba a titi, kana mai hakar kabari a Birtaniya, ya zama wani mai tagomashi a fagen siyasa ta hanyar shiga takarar shugabancin kasar Kenya, da yin alkawarin mayar da kasar babbar mai fitar da tabar wiwi, da dafin maciji, da kuma ‘ya'yan marainan kura, duk kuwa da cewa mutane da dama na dasa ayar tambaya kan yiwuwar shirin nasa.
Shehin malamin, mai shekaru 63, wanda ya yi karatu a fannin Shari’a, ya kasance mutumin da ya fita daban a cikin ‘yan takarar shugaban kasa hudu a zaben ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa.
Kuri’un jin ra’ayoyin jama’a sun saka dan takarar jam’iyar Roots Party a matsayin na uku mafi rashin tagomashi – na baya bayan da aka fitar a ranar 11 ga watan Yuli, ya samu kashi 4 bisa dari kacal na kuri’ar.
Amma masu sharhi sun bayyana cewa yana kokari ganin cewa wannan shi ne karonsa na farko na fafatawa a zabe, kana ‘yan takara biyu na kan gaba-gaba za su shiga damuwa game da bar masa ko da kuri’a kwaya daya kamar yadda kuri’un jin ra’ayoyin suka yi hasashe kan zazzafar takara, inda suka saka gogaggen jagoran adawa Raila Odinga a kashi 43 bisa dari, kana Mataimakin Shugaban kasa William Ruto a kashi 39 bisa dari.
A lokacin gangamin yakin neman zaben, Farfesa Wajackoyah kan sanya tufafin masu wasan motsa jiki, da riga mai gajeren hannu da dankwali a maimakon cikakkiyar shiga ta kwat – don nuna cewa ba ya cikin gwamnatin Kenya da yake zargi da cin hanci da rashawa.
Yakan kuma nuna alamu da ‘yan yatsunsa kamar yana shan tabar wiwi, kana yakan nishadantar da taron jama’a a lokacin da yake yin rawar wakokin nan na reggae.
Farfesa Wajackoyah ya bayyana cewa idan ya yi nasara a zaben zai kafa dokokin yi wa noman tabar wiwi kwaskwarima ta hanyar amfani da ita a fannin masana’antu a harhada magunguna, don taimakawa wajen shawo kan manyan matsalolin kasar Kenya – rashin aikin yi da kuma kangin basussukan da kasar ta fada.
Ya yi ikirarin cewa zai samar wa kasar ta Kenya kudi fiye da shilling tiriliyan tara (kwatankwacin dala biliyan saba’in da shifa) a ko wace shekara, kana gwamnati ba za ta "sake cin bashin ko kwandala ba."
"Kasashen Yamma sun halatta bhang [tabar wiwi]; me zai sa mu ba za mu yi haka ba?," in ji shi.
Duk da cewa bai kare ikirarinsa da cikakken bincike ba, dokar amfani da tabar wiwi don masana’antu da sarrafa magunguna wani babban bangare ne na yakin neman zabensa.
Shafin intanet na cibiyar bincike ta Africa Check ya bayyana tsarinsa a matsayin marar kan gado.
Duk da haka, hakan ya sa ya zama abin tattaunawa a shafukan sada zumunta, kana ya bai wa matasa da dama wadanda rashin aikin yi shafa sha’awa.
Muddin aka aiwatar da aniyar Farfesa Wajackoyah, hakan zai sa kasar ta Kenya ta shiga cikin jerin sauran kasashen Afirka – da suka hada da Lesotho, da Afirka ta Kudu, da Zambia da kuma Zimbabwe – da ke shirin shiga kasuwar tabar wiwi ta duniya, wanda kamar da yadda wata kididdiga ta nuna ana sa ran darajar za ta kai dala biliyan tama’in.
Farfesa Wajackoyah ya bayyana cewa bai taba zukar tabar wiwi ba, amma zai kasance mutum na farko da zai yi hakan don nuna murna muddin kasar Kenya da halatta ta.
"Babu wani laifi a shan ta muddin aka halatta, kana hukumomin sa ido suka amince da a rika shan ta,’’ a cewarsa.
Farfesa Wajackoyah na kallon kiwon maciji a matsayin karin wani babban tushen bunkasa tattalin arzikin kasar Kenya.
Ya ce dafin macikin, wanda yake ikirarin "ya fi zinari tsada’’, za a iya tatsarsa don hada maganin kashe dafin macijin don amfani a asibitoci, a yayin da za a iya fitar da naman macijin zuwa kasashe irin su China, inda ake daukarsa a matsayin abinci mai dadi.
"Za mu iya samun biliyoyi daloli a ko wace shekara da zai sa tattalin arzikinmu dorewa,’’ Farfesa Wajackoyah ya bayyana, ba tare da fitar da wata shaida da za ta tabbatar da alkaluman ba.
Ya kuma ce kasar Kenya za ta iya fitar da ‘ya'yan marainan kuraye, da ake amfani da su wajen hada magunguna a kasar China, yana mai cewa hakan zai samar da kudin shiga fiye da na tabar wiwi.
Kungiyoyin kare namun daji da likitocin dabbobi na kasar Kenya sun mayar da martani cikin bacin rai.
"An haramta kasuwancin ‘ya'yan marainan kauraye da kuma macizai kana kuma barazana ce ga rayuwar namun daji,’’ a cewar kungiyar likitocin dabbobi a wata sanarwa.
Ta kara da cewa shirin "karin wata annobar ce" saboda zai iya haifar da yaduwar kwayoyin cuta na bairos, da bacteriya da sauran kwayoyin cututtuka daga kurayen a macizai zuwa dan adam.
Duk da yin tur da ake masa kan abin da masu suka ke kira neman suna, Farfesa magoya bayan Wajackoyah na matukar kaunarsa kan yadda yake jure wa duk wasu kalubalen rayuwa wajen shiga takarar shugaban kasa.
Ya girma a kauyen yammacin Kenya kana bayan da iyayensa suka rabu, ya koma zama a titin Nairobi babban birnin kasar.
Wasu masu ibada a wurin bauta na Hare Krishna, da ke ciyar da mutanen da ba su da wurin zama ne suka ceci rayuwarsa.
Farfesa Wajackoyah ya zauna a wurin bautar kana ya zama limamin Hare Krishna.
An dauki dawainiyarsa wajen kammala karatunsa na sakandare kana daga bisani ya shiga aikin dan-sanda a kasar Kenya, ya kuma kai ga matakai daban-daban don kai wa ga matakin shiga rundunar tsaron farin kaya.
Farfesa Wajackoyah ya bayyana cewa ya fada babbar matsala bayan da ya dauki wasu bayan sirri game da daya daga cikin manyan kashe-kashe a kasar Kenya, na Ministan Harkokin wajen kasar Robert Ouko a shekarar 1990.
Ya kuma ce an cafke shi aka gana masa azaba, kuma bayan sako shi ne ya tsere daga kasar Kenya tare da taimakon ofishin huddar jakadancin Amurka a birnin Nairobi.
Bayan tserewa daga kasar Kenya, Farfesa Wajackoyah ya samu hanyar shiga kasar Birtaniya inda ya rika yin kananan ayyuka kana ya nemi karo karatu a Jami’ar Soas ta birnin London, da Jami’ar Warwick da Jami’ar Wolverhampton.
A yayin da yake karatu a Wolverhampton ya kuma yi aiki a matsayin mai gadi, da mai hakar kabari da kuma wankan gawa don samun kudin shiga.
Aikin ya sa shi samun "natsuwa da hankali’’, ya shaida wa jaridar Daily Nation.
Ya kuma ce hada karatu da aiki ya sa shi samun maaki na uku a karatun auya. Ba a dauki wannan a matsayin cin jarrabawa ma kyau ba.
Ya shiga gangamin yakin neman zabe a Birtaniya don yin mtasin lambar kawo sauyi a kasashe daban-daban na duniya – kana ya yi aiki tare da tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings, wanda ya karbi ragamar mulki a wani juyin mulki a shekarar 1981, kuma ya yi mulki har ya zuwa shekarar 2000.
Daga bisani ne Farfesa Wajackoyah ya koma Amurka, inda ya hadu da matarsa bakar fatar Amurka. Kuma sun an bayar da rahoton cewa sun haifi ‘yaya uku.
Ya kuma yi karatun a jami’oi da dama na murka, da suka hada da digirin digigir daga jami’ar shafin intanet ta Walden.
Farfesa Wajackoyah ya dawo kasar Kenya a shekarar 2010, inda ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa.
A sauran alkawuransa na yakin neman zabe masu cike da kace-nace, Farfesa Wajackoyah ya bayyana cewa zai inganta yanayin aikin gwamnati ta hanyar bullo da yin aiki sau hudu a ko wane mao, don bai wa Musulmai damar yin ibada a ranakun Jumma’a, da mabiya daikar addinin Kirista ta Adventists a ranakun Asabar, da kuma sauran mabiya addinin Kirista a ranakun Lahadi.
Farfesa Wajackoyah ya kuma yi alkawarin dawo da dokar hukuncin kisa, kana ya ce duk wadanda aka yankewa hukunci kan aikata laifin cin hanci da rashawa za su fuskanci zabin hukuncin kisa ta hanyar harbewa ko kuma rataya "bayan cin ugali [wani nau’in abincin gargajiya da ake yi da masara a kasar Kenya]".