Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da kuke bukatar sani a kan Ranar Hausa ta Duniya
Ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara ce ake bukukuwan Ranar Hausa ta Duniya.
Taken bikin na bana shi ne "Zaman Lafiya da Ƙaunar Juna".
Wannan ranar dai ta samo asali ne a shekarar 2015 inda ma'aikacin Sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Aliyu Jari da wasu abokansa na shafukan sada zumunta suka ayyana ranar a matsayin ranar da masu magana da harshen Hausa za su hadu su tattauna ci gaba da kalubalen da harshen ke fuskanta a karni na 21.
A kowace shekara idan ranar ta zagayo ma'abota shafukan sada zumunta na yin amfani da tambarin #RanarHausa domin tattaunawa da yin muhawara. Daga bisani kuma a shekarar 2018 aka fara gudanar da bukuwa na zahiri a gidan ɗan Hausa da wasu ƙasashe a fadin duniya kamar Ghana.
End of Ƙarin Labaran da za ku so karantawa
Nasarorin da aka samu
Wadanda suka ƙirƙiro wannan ranar sun ce sun yi haka ne domin tuna wa da al'ummar Hausa game da muhimmancin harshen da yadda za a ciyar da shi gaba.
Sannan kuma ranar ta kasance a matsayin wata rana da ake ƙalubalantar al'ummar Hausawa domin fiddo da sabbin bincike da nazarce-nazarce domin haɓaka harshen na Hausa.
Babbar nasarar da za a ce Ranar Hausa ta Duniya ta haifar ita ce haɗa kan al'ummar Hausawan duniya a duk inda suke. A shekarar da ta gabata, an gudanar da bikin Ranar Hausa a ƙasashe 17, cikinsu har da Faransa da Saudiyya.
Hausawa na haɗuwa a wannan rana domin sada zumunci da kuma tattaunawa a kan yadda za su taimaka wa juna.
Girman Harshen Hausa
Masana harshe da dama na yi wa harshen Hausa kallon wani harshe mai yaɗuwa a fadin duniya, inda yanzu haka nazarce-nazarce ke nuna cewa Hausa ne harshe na 11 a fadin duniya wajen masu amfani da harshen kuma na ɗaya a Afirka ta yamma.
Sai dai akwai jayayya tsakanin manazarta kan girman Hausa a nahiyar Afirka, inda wasu ke ganin harshen Swahili da ake yi a kasashe da dama na yankin Afirka maso gabas ya ɗara na Hausa wanda ake yi a yankin Afirka ta yamma da Afirka ta tsakiya da ma kusurwar Afirka.
Sai dai nazarce-nazarce sun nuna harshen Hausa yana gaba da na Swahili ta fannin yawan masu yin yaren inda shi kuma Swahili ke gaba wajen yawan ƙasashen da ake yin yaren.
Tuni dai manyan kafafe irinsu Facebook da Google suke amfani da harshen Hausa inda tuni manhajar amfani ta Android da IOS suka shigar da shi cikin harsunan da suke amfani da su.
Ko a baya-bayan nan sai da hukumar Lafiya ta Duniya ta sanya Hausa a cikin harsuna guda uku da ta zaba domin yaki da annobar korona a Afirka.
Ana fatan harshen Hausa zai samu karɓuwa nan ba da jimawa ba cikin harsunan amfani na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar haɗa kan ƙasashen Afirka ta AU da ma Kungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ECOWAS.
Iyaka dai har yanzu ana bukatar bincike sosai da nazari a kan harshen Hausa ta hanyar sabbin ƙirkire-ƙirkire na zamani domin ɗaga martabar harshen.