Su waye 'yan takarar Republican da ba sa tare da Trump?

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da aka ɗauki haramar tunkarar zaɓen shugaban ƙasar Amurka na 2024 bayan gama zaɓukan rabin wa’adi – ‘yan takara da yawa suna jiran lokaci ne kawai.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da shirinsa na yin takara, tare da rantsuwar “sake gina Amurka da ɗaukakata”.

Amma ya fi shahara ga masu zaɓe a jam’iyyar Republican, rashin kataɓus da ya yi a zaɓen rabin wa’adi, ya sanya ba shi da wani kwarjinin samun takarar kai tsaye.

Tsohon shugaban ƙasar, zai cika shekara 78 nan da shekara biyu da yiwuwar ya fuskanci ƙalubale daga masu neman matsayin a jam’iyyarsu ta Republican ciki harda waɗanda a baya suka goyi bayansa.

Nikki Haley

Nikki Haley ta sanar da shirinta na neman shugabancin Amurka a tsakiyar watan Fabirairu, ta kuma zama ‘yar takarar Republican ta farko da ta bayyana shirin fafatawa da Mista Trump.

Yayin da ake mata kallon daya daga cikin matasan jam’iyyar Repblican masu tasowa, Nikki Haley ta zama tana ɓoye matsayinta a ‘yan shekarun nan.

An haifeta a South Carolina a gidan Sikh ɗan cirani na ƙabilar Punjabi ta yankin Indiya, Ta kasance gwamna mafi ƙarancin shekaru a Amurka a 2009.

Ta ja hankalin mutanen ƙasar a 2015 bayan ta yi kira a cire tutar Confederate daga majalisar South Carolina.

Duk da cewa ta ce ita ba ta “goyon bayan” Trump a 2016, daga baya ta amince da bayyana sunansa a matsayin wakilin Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, wa’adinta ya yi fice lokacin da ta fice daga taron kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya lokacin da wakilin Falasɗinawa yake bayani.

Rick Scott

Asalin hoton, Getty Images

Rick Scott

Gwamnan Florida Ron DenSantis ya yi aiki tuƙuru wajen koyon Trump, kuma ana masa kallon wani ɗan takara mai ƙarfi da zai iya maye gurbin Trum a matakin farko.

Ya takara rawar da ta kamata wajen sake takara a zaɓen tsakiyar wa’adi da sama da ƙuri’u miliyan 1.5, tazara mafi girma da ya taba samu cikin sama da shekara 40.

A shekara 44, matashin da ya karanta lauya har yanzu sabuwar fuska ne a siyasar Amurka.

Ya taɓa aiki da sojin ruwan Amurka, yana cikin waɗanda suka je Iraqi. Kuma an ɗan san shi a majalisar wakilan Amurka daga 2013 zuwa 2018.

Ya yi watsi da takunkumin fuska da kuma tilasata rigakafin korona, ya sanya hannu kan dokar ƙin amincewa da zanga-zangar wariyar launin fata, ya koma goyi bayan kada a riƙa koyar da ilimin LGBT a makarantun firaimare.

A lokacin da yake kan shugabanci ‘yan Republican sun zaɓi jam’iyyar Demokrat da yawa a jihar karon farko cikin tarihi.

Mike Pence

Asalin hoton, Getty Images

Mike Pence

Na tsawon shekaru huɗu da ya shafe tare da Trump, ya kasance mai biyayya a gare shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, har sai da aka zo zanga-zangar 2021 wadda aka shiga majalisa tukunna ta raba kansu.

Ɗa ga sanan mutumin nan da ya yi yaƙin Korea, Mike Pence ya fara siyasarsa ne a matsayin ɗan ra’ayin riƙau a tattaunawar da yake yi a wani shirin radiyo da yake jagoranta.

An zaɓe shi a majalisa ne a 2000 kuma ya zauna har 2013, yana kiran kansa “ɗan ra’ayin riƙau’’.

Ya yi gwamna a Indiana daga 2013 zuwa 2017. A lokacinsa ya rage yawan harajin da ake biya, ya kuma sanya hannu kan dokar taƙaita zubar da ciki da kuma ‘yancin addinai.

Mista Pence mai shekara 36 ya tuba ya koma ɗan ɗarikar evengelica, kuma hakan ya taimaka yadda mabiya ɗariƙar suka zaɓi Trump a 2016.

Liz Cheney

Asalin hoton, Getty Images

Liz Cheney

‘Yar tsohon mataimakin shugaban ƙasar Dick Cheney ta taɓa zama wata fitacciyar tauraruwa a jam’iyyar Republican, ta zama mai matsayi na uku a majalisar ƙasar a 2019 zuwa 2021.

Kwararriya ce kan harkokin kuɗi da kuma na jam’a tana da ra’ayin tsoma baki kan harkokin kasashen waje, a 2017 ta lashe kujerar da mahaifinta ya taɓa riƙewa.

Ta rasa goyon bayan ‘yan Republican bayan ta riƙa sukar Trump tare da kaɗa ƙuri’ar tsige shi daga matsayinsa sakamakon zanga-zangar 6 ga watan Janairu.

Mis Cheney mai shekara 56, ta zama ɗaya daga cikin ‘yan Republican biyu kacal da suke cikin kwamitin da suke bincike kan zanga-zangar da aka yi a ka shiga ginin majalisa. Ita ce mataimakiyar da ta jagoranci zaman tuhumar Trump.

Wannan aiki ya sanya ta rasa matsayinta a watan Agusta, yayin da shugaban ya goyi bayan ɗan adawar da ya hamɓarar da ita da kusan kashi 40 na kuri’u yayin takara.

Mike Pompeo

Asalin hoton, Getty Images

Mike Pompeo

A matsayinsa na ɗan majalisa daga Kansan, Mike Pompeo ya fitar da sanarwa a 2016 kan cewa Trump zai zama “shugaba ɗan kama karya da zai riƙa watsi da kundin tsarin mulkinmu”.

Tsohon soji ne da ya kammala kwalejin ba da horo ta soji ta West Point military, kuma ya kammala da sakamako da ya fi na kowa, ya yi zaman majalisa tsakanin shekarun 2011 zuwa 2017.

Ya kammala karatun lauyansa a Harvard daga nan ya zama darakta CIA da kuma sakataren cikin gida lokacin Trump.

Ya taka muhimmiyar rawa kan manufofin Amurka ga ƙasashen waje, ciki har da manufar Amurka ta shekaru kan Isra’ila.

Glenn Youngkin

Asalin hoton, Getty Images

Glenn Youngkin

Glenn Youngkin ya ji daɗi lokacin da ya lashe zaɓen gwamna a Virginia a 2021. Sabon ɗan siyasa ne da ya shafe shekara 25 yana aiki da kamfanin Carlyle Group, ya yi nasara kan ɗan takarar Dimokrat wanda ke cikin siyasa tun shekarun 1980.

A wata jiha da ta karkata ga jam’iyyar Dimokrat a baya-bayan nan, Mr Youngkin ya yi kakkausar suka ga siyasar maƙalewa jam’iyya ɗaya yana cewa hakan mummunar aƙida ce a siyasance, kuma ya fara yaƙin zaɓe da manufar kawo ƙarshen wannan aƙida.

Ɗan shekara 55 ɗin ya riƙa tsintar kansa cikin manyan rikici da suka shafi lamuran mutane daga ranarsa ta farko a ofishi, daga watsi da dokar korona ba tare da hana koyar da wasu maudu’ai masu alaƙa da launin fata.

Rick Scott

Asalin hoton, Getty Images

Rick Scott

Rick Scott, ɗan shekara 70 ɗan majalisa ne daga jihar Florida, an ba shi aikin taimakawa ‘yan takarar Republican domin sake nasara a kujerar Sanata a zaɓen tsakiyar wa’adi.

Ya gaza cimma wannan buri, amma a yayin zaɓe ya taka muhimmiyar rawar gani ta hanyar goyon bayan duk wani ɗantaraka da ke faɗin kasar da kuɗi – yana bayyana kansa a matsayin babban magoyin baya.

Tsohon gwamnan Florida sau biyu, a yanzu yana shan matsi daga ‘yan Dimokrat bayan neman a rage girman gwamnatin tarayyar ƙasar.

Wasu da za su iya neman takarar

Tim Scott: Ɗan shekara 57 ya fito ne daga South Carolina, shi ne ɗan Afrika da Amurka na farko da ya zana a zauren majalisun ƙasar biyu kuma shi ne baƙar fata na farko da ya zama Sanata a jam’iyyar Republican tun 1979.

Ted Cruz: Sanata ne daga Texas yana kuma da shekara 52 ya nuna kansa a zaɓen fitar da gwani na Republican a 2016, kafin daga baya ya yi na biyun daga Trump.

Larry Hogan: Wanda ya warke daga kansar fata, mai shekara 66 ya yi gwamnan Maryland a 2015 – jihar da Dimokrat ta mamaye.

Greg Abbott: Gwamnan Texas na farko da ya yi amfani da keken guragu, Mista Abbott mai shakara 65 ya rike ra’ayin riƙau tun zaɓarsa da aka yi 2014.

Kristi Noem: Gwamna mace ta farko daga South Dakot mai shekara 51, an santa ne a ƙasar lokacin adawarta da kullen korona kuma ta ƙagu ta taka rawa a tattaunawar kasa.