Da gaske 'yanbindiga sun ƙwace sansanin sojan Najeriya a jihar Neja?

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an gwamnati a jihar Neja da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa 'yanbindiga sun mamaye wani sansanin sojan ƙasar da ke jihar.
Bayanai sun nuna cewa ana amfani da sansanin Nagwamatse ne da ke yankin Kontagora wajen bai wa sojojin Najeriya horon yaƙi, kuma yana ɗaya daga ckin mafiya girma a ƙasar.
Bayanin mamayar ya ɓulla ne bayan ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kontagora ta biyu, Abdullahi Isa, ya gabatar da ƙudirin neman a ayyana dokar taɓaci kan matsalar tsaro a yankin da yake wakilta.
Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta batun, tana mai cewa "labarin ƙanzon kurege ne". Ta ƙara da cewa "an ƙirƙiri labarin ne kawai don a haddasa faragaba a zukatan mazauna yankin".
Yayin gabatar da ƙudurin, ɗanmajalisar ya nemi a bar manoma mazauna yankin da sansanin yake su dinga noma a cikinsa, wanda a cewarsa zai rage ayyukan ‘yanbidiga a yankin.
Neja na cikin jihohin arewacin Najeriya da suka fi fama da hare-haren 'yanfashin daji da ke kai hare-hare da sace mutane domin neman kuɗin fansa. Bugu da ƙari, mayaƙa masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram na iko da wasu ƙauyuka a jihar.
A makon da ya gabata ma hukumomin Najeriya sun zargi 'yanbindigar da lalata layin wutar lantarki a yankin Shiroro na jihar ta Neja, abin da ya jefa kusan dukkan arewacin Najeriya cikin duhu tsawon kwana 10 - ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Bayanan da BBC ta tattara
Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa 'yanbindigar sun ƙwace iko da sansanin kamar yadda majiyoyi suka tabbatar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗanmajalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Tapa kuma mataimakin shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dokokin jihar Neja, Sani Idris, ya tabbatar wa BBC cewa majalisar ta tattauna ƙudirin har ma ta yi masa kwaskwarima.
"Majalisa ta yi wa ƙudirin gyara, inda ta ce a yi magana da gwamnatin jihar Neja domin ta saka baki wajen neman sojoji su ƙara ƙaimi domin korar 'yanbindigar daga dajin Kontagora," in ji shi.
Wata majiya da ba ta amince a bayyana sunanta ba daga rundunar sojin Najeriyar ta faɗa wa BBC cewa tuni rundunar ta umarci ƙarin dakaru daga maƙwabtan yankuna su kai ɗauki domin ƙwato sansanin.
"Ɓarayin sun je da yawa ne, sun fi mutum 500, kuma hanya ba ta da kyau ballantana a kai musu ɗauki da wuri," a cewar majiyar. "Amma yanzu an kore su bayan jirgin helikwafta ya je wurin. Sun gudu, sun koma ta hanyar da aka lalata layin lantarki."
Sansanin da ake kira Nagwamatse Training Camp, yana da girma sosai, inda ya fara daga ƙaramar hukumar Kontagora zuwa Mariga.
"Sansanin ya kwashi daji mai girma sosai. Girman dajin na Kontagora ya sa ana zaton 'yanbindigar na da sansanoninsu a cikinsa, kuma abin da ya sa majalisa ta nemi a bar manoma su dinga yin noma a ciki kenan ko hakan zai taimaka wajen rage zirga-zirgar 'yanbindigar," kamar yadda Sani Idris ya bayyana.
Ɗaya daga cikin abin da ɗanmajalisar ya nema a ƙudirin nasa shi ne a ayyana dokar taɓaci a yankin.
Ƙaramar hukumar Mariga na daga cikin wuraren da 'yanbindigar suka fi addaba, kamar yadda Sani Idris ya bayyana.
"Saboda tana da dazukan da suka yi iyaka da jihohin Zamfara, da Kebbi. Shi ya sa majalisa take fargaba game da lamarin," a cewarsa.
Bincike ya nuna makiyaya ne ke yawo a wurin ba 'yanfashi ba - Sojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta musanta labarin ne cikin wata sanarwa da Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta ce: "Labarin ƙwace sansanin... da kuma na cewa an fatattaki mazauna ƙauyuka 23 ba wai na ƙarya ba ne kawai, mai cutarwa ne saboda an yaɗa shi ne kawai don a jefa fargaba a zukatan mazauna yankin Kontagora da Mariga.
"Bincike na tsanaki da sashen tattara bayanan sirrinmu ya gudanar ya tabbatar da cewa mutanen da aka gani a yankin makiyaya ne da ke neman wurin kiwo."
Ta ƙara da cewa "babu wata mummunar aniya da aka gani tare da su".











