Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mata ke zuwa asibitocin bayan fage don zubar da ciki a Kenya
- Marubuci, Daga Zoe Flood, Linda Ngari & Tamasin Ford
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye, Nairobi & London
Harshen damo game da dokokin zubar da ciki a Kenya na tilasta wa dubban mata komawa asibitocin bayan fage. Sashen binciken kwakwaf na BBC ya gudanar da binciken yadda labaran karya da tsangwama suka dabaibaye zubar da ciki.
Edith tana kwance a kan gadon da aka lulluɓe da tsohuwar jarida a wani asibitin bayan fage a Nairobi.
Wani abu na rike da kafafunta yayin da wani likita sanye da farar riga ke shirin saka wani magani a cikin mahaifarta. A ɗaya gefe kuma, akwai wani jan bokiti ɗauke da magani a ƙasa.
Mahaifiyar ‘ya’ya uku wadda aka canza sunanta domin kare mutuncinta, tana da cikin wata huɗu kuma tana shirin zubar da shi.
"Dole ne na kawo karshen sa saboda na koma bakin aiki, kuma ina da wani karamin jariri," kamar yadda ta shaida wa BBC Africa Eye daga baya.
Zubar da ciki lamari ne mai sarkakiya a Kenya.
Dokar hukunta laifuka, wadda ta samo asali tun lokacin mulkin mallaka, ta haramta zubar da ciki, hukunta wanda ya zubar da cikin da kuma wanda ya ba da kayan da ake buƙata.
Sai dai, kundin tsarin mulki na 2010, haɗi da manyan dokoki, ya ba da damar zubar da ciki idan “rayuwa ko lafiyar uwa na cikin haɗari” ko kuma lokacin da ciki ya samo asali daga fyaɗe ko lalata.
Edith ta gano cewa tana ɗauke da cutar kanjamau shekaru kaɗan da suka wuce. Abokin zamanta ya bar ta daga baya, bayan ya ki a yi masa gwaji.
Wani lauya ya shaida wa BBC cewa samun yaro yayin da mace ke ɗauke da kwayar cutar HIV na nufin "lalacewar lafiyar jikinta na cikin hadari". Wannan, da wasu dalilai, na nufin cewa Edith ta cancanci zubar da ciki bisa tsari na doka.
Amma ta ji cewa asibitin bayan fage shi ne zaɓinta ɗaya tilo.
Likitoci kaɗan ne da ke aikin zubar da ciki bisa tsarin doka ke fitowa bainar jama'a suna magana game da batun.
Kame-kamen da aka yi a tsawon shekaru ya sanya lamarin ya zama "haɗari ga ma'aikatan kiwon lafiya", a cewar Farfesa Joachim Osur, ƙwararre a fannin kiwon lafiyar haihuwa da jima'i a Jami'ar Amref International da ke Nairobi. Ya danganta yadda ake fahimtar doka.
“Ya danganta da yadda alkali ya fassara halascin tsarin da wani ya yi, zai iya bi ta ko wace hanya,” in ji shi.
A shekarar 2004, an kama Dokta John Nyamu tare da ma’aikatan jinya biyu bisa laifin kashe ‘yan tayi biyu, laifin da hukuncinsa ke ɗauke da kisa.
An tsare shi a gidan yarin Kamiti Maximum Security da ke Nairobi na tsawon watanni 12 kafin a same shi da laifi.
Kwakwazon da kafofin watsa labaru a Kenyasuka yi game da shari'arsa ya kai ga kafa Ƙungiyar Lafiya ta Haihuwa da Haƙƙin da kuma haƙƙin.
Ƙungiyar ce ta jagoranci muhawarar da ta taimaka wajen rubuta kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 2010, wanda a karon farko a tarihin ƙasar ya samar da wata hanya ta zubar da ciki ta doka, ko da kuwa tana da iyaka.
Duk da haka, Dr Nyamu, wanda a yanzu ya ke zubar da ciki da ke kan doka da kuma aminci, ya yi imanin cewa harshen damo kan zubar da ciki yana da wuya ga mata su samu damar yin haka, ko da lokacin da ya kamata a bar su musamman a wuraren kiwon lafiyar jama'a.
"Zubar da cikin da ba shi da aminci ya zama ruwan dare a Kenya," in ji shi, yana mai cewa mata matalauta ne suka fi shan wahala saboda ba a samun aminci a asibitocin gwamnati saboda rashin tabbas da rashin ka'idoji. Zubar da ciki marasa aminci da suke nema na iya haifar da matsalolin lafiya.
Dr Nyamu ya ƙara da cewa: "Waɗanda ke samun matsaloli bayan zubar da ciki, yawancinsu matasa ne…. Matan sun fara ne da kansu, ko kuma suna yin hakan ne da taimakon wanda bai samu horo ba," in ji Dr Nyamu.
A cewar ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta duniya, da Cibiyar kare hakkin haihuwa, kusan mata da 'yan mata bakwai ne ke mutuwa kowace rana a Kenya saboda rashin amun zubar da ciki mai aminci. Wasu dubbai kuma suna kwance a asibiti.
A wani asibitin da ke aiki bisa ka'ida ba a wajen birnin Nairobi, mutumin da ke kula da shi ya bai wa mata damar zubar da ciki a kan shilling na Kenya 2,500.
“Muna da ‘yan matan da har yanzu suke zuwa makaranta, muna samun wasu da ake yi musu fyaɗe.
"Kuna samun wanda bai shirya ba, kuma suna so su dakatar da shi. Muna taimakawa saboda sun zo neman taimako. Suna buƙatar wannan taimakon daga gare mu," in ji shi.
Yana karɓar ƙarin kuɗi don yin aiki amintacce na zubar bar da ƴan tayin.
Idan mace ba za ta da halin biya, yana biyan wani don jefa ƴan tayin a cikin kogin.
Masu fafutukar yaƙi da zubar da ciki da ƙungiyoyin addini da ke da alaka da su a Kenya, waɗanda da yawa daga cikinsu ke samun goyon bayan ƙungiyar yaƙi da zubar da ciki a Amurka, sun dage cewa dokar ta fito karara: zubar da ciki haramun ne.
Charles Kanjama, shugaban wata ƙungiyar kiristoci a ƙasar Kenya, yana tofa albarkacin bakinsa akai akai game da zubar da ciki tare da shirya taruka a Nairobi.
"A gare mu, ba ma tunanin akwai wani saɓani. Muna tunanin [kundin laifuka da kundin tsarin mulki] sun daidaita. Ba na goyon bayan gyara dokokinmu don cire laifin zubar da ciki," in ji shi.
A shekarar 2012, gwamnati ta wallafa ka'idoji ga ma'aikatan lafiya game da zubar da ciki na doka. Shekara guda bayan haka aka janye su, kuma an dakatar da horar da kula da zubar da ciki lafiya.
Har yanzu dai lamarin na nan kuma ƙungiyar Mista Kanjama tana son ta ci gaba da kasancewa a haka.
"Matsayinmu shi ne, ko zubar da ciki na da aminci ko kuma akasin haka, na farko yaro yakan mutu, don haka akwai haɗari ga yaro kullum. Kuma na biyu, ba za ka iya horar da mutane su yi wani abu da ya saɓa wa doka a ƙasar ba."
Akwai mutane da yawa a Kenya waɗanda ba su yarda batun zubar da ciki ba.
Yar majalisa Esther Passaris ba kawai ta yi magana game da zubar da ciki ba amma tana matsawa don inganta lafiyar jima'i da ilimin tsarin iyali ma.
“Tsarin mulkinmu ya ba da damar zubar da ciki ne kawai a lokacin da aka ga lafiyar mahaifiyar za ta shiga haɗari.
"Ina tsammanin lokaci ya yi da za mu fahimci nauyin wahala na rashin samun damar yin amfani da tsarin iyali, rashin karfafawa mace don ta san cewa ba dole ba ne ta zama kamar injin samar da jarirai."
Ms Passaris ta ce yayin da kundin tsarin mulki na shekarar 2010 ya halasta zubar da ciki a wasu yanayi, ta yi nuni da cewa akwai fargabar hakan zai iya hana mata samun ayyukan kiwon lafiya, musamman ga waɗanda suka fito daga al'ummomi marasa galihu.
Ta ce "Masu kuɗi suna da damar kai 'ya'yansu asibitoci masu kyau kuma su samu zubar da cikin lafiya, shiru, ba tare da wani ya sani ko magana a kai ba. Amma talaka sai ya sha wuya," in ji ta.
A watan Maris ɗin shekarar 2022, wata babbar kotun ƙasar Kenya ta tabbatar da zubar da ciki a matsayin wani muhimmin hakki a karkashin tsarin mulkin ƙasar, ta kuma yanke hukuncin cewa kama mutane da ake yi ba ya kan ka'ida, amma hakan bai yi wani tasiri ba wajen kawar da fargabar wasu mata, kamar Edith.
Can a asibitin da Edith ta je domin zubar da ciki, mutumin wanda ya ce yana da kwarewa ta zama likita kuma yana zubar da ciki sau 150 a wata, ya kammala saka magani a cikin mahaifarta domin zubar da cikin.
"Yana ɗaukar sa'a huɗu zuwa biyar kafin maganin ya fara aiki. Sai dai daga baya, idan abu ya yi nisa, za ta shiga irin yanayin da mata ke shiga idan suka zo haihuwa," in ji shi.
Edith ta tara kusan shilling 4,000 na kuɗin ƙasar ta Kenya domin zubar da ciki. Kuɗin ba su kai ba, amma asibitin ya amince ya zubar mata shi da sharaɗin cewa za ta ƙara kuɗin daga baya.
Mako ɗaya bayan zub da cikin, Edith ta sake tattaunawa da BBC, inda ta kwatanta yadda lamarin zubar da ciki a ɓoye yake.
"Na kasance ni kaɗai kuma cikin raɗaɗi, zaune cikin asibitin. Ina mamakin abin da ke faruwa, idan haihuwa zan yi. Ina tunani: 'Ba na son mutuwa a cikin wannan gida ni kaɗai.'
"Za a yi maka aikin cikin raɗaɗi. Kana son yara amma duba da irin rayuwar da kake ciki, ya zama dole ka zubar da cikin."