An sanar da Liz Truss a matsayin sabuwar Firaiministar Birtaniya

An sanar da Elizabeth Truss a matsayin Firaiministar Birtaniya.

An yi takarar neman kujerar ne tsakaninta da Rishi Sunak.

Kafin ta zama Firaiminista, ta kasance ministar harkokin wajen Birtaniya.

Ta jagoranci 'yayan jam'iyyar a gangamin kada kuri'ar neman maye gurbin Boris Johnson, wanda aka tilasta wa murabus sakamakon tarin badakala. Sai dai mutum daya wanda ke hamayya da ita shi ne Rishi Sunak.

A halin yanzu dai za ta ci gaba da jagorantar harkokin Birtaniya bayan murabus ɗin da Boris Johnson ya yi a watan Yuli.

Ana kuma sa ran sabuwar firaiministar wadda za ta gaji Boris Johnson za ta goyi bayan ƙayyade farashin makamashi a Birtaniya wanda ke ta ƙaruwa a faɗin Turai sakamakon yaƙi Ukraine.

Tuni wasu daga cikin shugabannin duniya suka soma murna da wanan sabon ci gaba da Ms Truss ta samu

Ita ce mace ta uku da ta zama firaiminista a Birtaniya bayan Margaret Thatcher da kuma Theresa May

Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen na daga cikin waɗanda suka taya ta murna inda ta ce tana sa ran aiki tare da ita.

Shi ma wanda ya gabace ta Boris Johnson wanda shi ne tsohon firaiministan ƙasar ya yi mata murna inda ya ce tana da shirye-shiryen shawo kan matsalolin da ke addabar ƙasar.

Dominic Raab, wanda shi ne mataimakin firaiminista da kuma sakataren shari'a, ya ce ba ya sa ran zai yi aiki a gwamnatin Liz.

Amma ya sha alwashin bayar da duk wata gudunmawa iya ƙarfinsa amma a cewarsa, ba ya sa ran za a ba shi wani muƙami.

Sharhi daga Chris Mason, editian harkokin siyasa na BBC

Abubuwa za su sauya. Sauyin zai faru, Boris Johnson na daga cikin ministocin da suka yi aiki.

Sai dai Liz Truss za ta gaji irin matsalolin da Mista Johnson ke fuskanta.

Za ta yi mulki a lokacin da miliyoyin mutane ke fuskantar ƙalubale.

Za kuma ta yi mulki a lokacin da ake yaƙi a Turai da kuma ƙoƙarin farfaɗowa daga annobar korona.

Haka kuma za ta jagoranci jam'iyyar da ta shafe shekara 12 tana mulki.