Saudiyya: An bai wa sojojin damar 'harbe' waɗanda suka ƙi tashi daga filayen birnin da ake ginawa

    • Marubuci, Daga Merlyn Thomas & Lara El Gibaly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify da BBC Eye Investigations

Hukumomin Saudiyya sun ba da izinin yin amfani da karfi don kakkaɓe filaye domin wani garin da ake gina birni mai dausayi wanda kamfanoni da dama na ƙasashen yammacin duniya ke ginawa, kamar yadda wani tsohon jami’in leken asiri ya shaida wa BBC.

Kanal Rabih Alenezi ya ce an umarce shi da ya kori mutanen ƙauye daga wata ƙabila don ba da hanyar a kafa The Line, wani bangare na aikin samar da birnin dausayi na Neom.

Daga bisani an harbe ɗaya daga cikinsu har ya nuna rashin amincewa da umarnin.

Gwamnatin Saudiyya da shugaban Neom ba su ce komai ba game da rahoton.

Neom, wani dausayi ne da Saudiyya za ta kashe dalar Amurka biliyan 500 wajen ginawa a wani bangare na burinta zuwa 2030 don faɗaɗa tattalin arzikinta daga man fetur.

Aikin farko na birnin mai dausayi, an yi maganarsa a matsayin birnin da mota ba ta shiga, mai faɗin mita 200 da tsawon kilomita 170 - duk da cewa kilomita 2.4 na aikin ake sa ran za a kammala nan da 2030.

Kamfanoni da dama, galibinsu daga Burtaniya, na cikin masu aikin kwangilar gina Neom.

Filin da ake gina Neom, Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ya bayyana shi a matsayin filin Allah.

Amma an kwashe fiye da mutum dubu shida domin aikin, a cewar gwamnati sannan ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta ALQST da ke da mazauni a Birtaniya, ta ƙiyasta adadin ya zarce haka.

BBC ta yi nazari kan hotunan sararin samaniya na uku daga cikin ƙauyukan da aka rushe - alKhuraybah, Sharma da Gayal. An rushe gidaje da makarantu da asibitoci daga taswirar.

Kanar Alenezi, wanda ya je neman mafaka a Birtaniya bara, ya ce umarnin share wajen da aka nemi ya samar da al-Khuraybah ne, mai nisan kilomita 4.5 a gabashin birnin mai dausayi na The Line.

Ƙauyukan galibinsu cike suke da ƴan ƙabilar Huwaitat, da suka mamaye yankin Tabuk a arewa maso yammacin ƙasar tsawon shekaru.

Ya ce umarnin na Afrilun 2020 ya nuna cewa Huwaitat ya ƙunshi "ƴan tawaye masu yawa" da "duk wani da ya ci gaba da adawa da korar" ya kamata a kashe shi, don haka sai ta ba da lasisin amfani da ƙarfi kan duk wanda ya tsaya a gida."

Ya kaucewa ƙudirin bisa dalilai na lafiya, ya faɗa wa BBC, amma duk da haka ba a fasa ba.

Abdul Rahim al-Huwaiti ya ƙi barin kwamitin rajistar filaye ya ƙiyasta darajar filin, kuma hukumomin Saudiyya sun harbe shi, kwana ɗaya bayan nan, a lokacin aikin korar mutanen.

A baya, ya wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta saboda ƙin yadda a kori mutane.

BBC ba ta iya tabbatar da kalaman Kanar Alenezi game da amfani da ƙarfi ba.

Amma wata majiya da ta fahimci aikin sashen kula da bayanan sirrin Saudiyya ta faɗa mana bayanan kanar ɗin - game da yadda aka bayar da umarnin korar mutanen da kuma abin da aka ce - ya yi daidai da abin da suka sani game da irin waɗannan ayyukan.

Sun kuma ce matsayin kanar ɗin zai fi dacewa wajen jagorantar aikin.

Aƙalla ƙarin ƙauyuka 47 aka tsare bayan da suka ƙi yarda su tashi, galibinsu an gurfanar da su kan tuhume-tuhumen da ke da nasaba da ta'addanci, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da ALQST.

Cikinsu, 40 na tsare, biyar kuma na fuskantar hukuncin kisa, a cewar ALQST.

An kama da dama a cikinsu saboda kawai sun yi jimamin mutuwar al-Huwaiti a shafukan sada zumunta, in ji ƙungiyar.

Hukumomin Saudiyya sun ce waɗanda aka buƙaci su fice domin a gina birnin mai dausayi an biya su diyya. Amma kuɗin da aka biya ba su kai yadda aka yi alƙawari ba, a cewar ALQST.

A cewar kanar Alenezi, "[Neom] shi ne abin da Mohammed Bin Salman ya mayar da hankali. Shi ya sa ya nuna ba sani ba sabo wajen tafiyar da batun Hauwaitat."

Wani tsohon babban jami'i na katafaren aikin ya faɗa wa BBC cewa ya samu labarin kisan Abdul Rahim al-Huwaiti, ƴan makonni kafin barin ƙasarsa ta asali - Amurka domin karɓar aikin a 2020.

Andy Wirth ya ce ya sha tambayar manyansa game da korar, amma bai gamsu da amsoshin ba.

"Kawai yana nuna abu mai muni da aka aikata a kan waɗannan mutanen...," ya bayyana.

Ya bar aikin ƙasa da shekara ɗaya bayan fara shi, bai yadda da hukumar ba.

Wani babban jami'i a kamfanin da ke tace gishiri daga teku da ya janye daga aikin dala miliyan 100 domin gina birnin mai dausayi a 2022, shi ma na cikin sarƙaƙiya.

"Zai yi kyau ga mutanen da ke da masaniyar kimiyya da ke zaune a yankin amma ya batun sauran? in ji Malcolm Aw, shugaban kamfanin Solar Water.

Ya kamata a kalli al'ummar garin da daraja, ya ƙara da cewa, ganin yadda suka fi fahimtar yankin.

"Ku nemi shawarar ingantawa da samarwa ba tare da korarsu ba."

Mutanen ƙauyukan da aka ɗaiɗaita ba su ce komai ba, suna tsoron magana da kafafen yaɗa labaran ƙasashen waje ka iya ƙara jefa ƴan uwansu da ke tsare cikin haɗari.

Amma mun yi magana da waɗanda aka kora domin aikin tabbatar da burin Saudiyya a shekarar 2030 wato Saudi Vision 2030.

Fiye da mutum miliyan ɗaya ne suka ɗaiɗaita sanadin aikin Jeddah Central a wani birni da ke yammacin Saudiyya - da suka haɗa da gidan wasannin daɓe da raye-raye da wurin wasanni da na kasuwanci da gidaje.

Nader Hijazi [ba sunansa na gaskiya ba] ya tashi a Aziziyah - ɗaya daga cikin yankuna 63 da ke maƙwabtaka da rusau ya shafa.

An ƙona gidan mahaifinsa a 2021 da aka ba shi umarnin tashi ƙasa da wata ɗaya.

Hijazi ya ce hotunan da ya gani na tsohon yankinsu na da firgitarwa, inda ya ce sun yi kama da filin daga.

"Suna ƙaddamar da yaƙi kan mutane, yaƙi a kan asalinsu."

Masu fafutuka daga Saudiyya sun faɗa wa BBC cewa an kama mutum biyu a shekarar da ta gabata kan hannu da rusau ɗin da aka yi a Jeddah - ɗaya saboda ƙin yadda da korar, ɗayan kuma saboda wallafa hotunan rusau ɗin a shafukan sada zumunta.

Sannan wani ɗan uwan wanda aka tsare a babban gidan gyaran hali na Dhahban ya ce sun ji bayani daga ƙarin mutum 15 da ke tsare a can - saboda zargin su da shirya liyafar bankwana a ɗaya daga cikin yankunan da aka tsara za a rushe.

Wuyar samun mutanen da ke tsare a gidan gyaran halin na Saudiyya na nufin, ba mu iya tantance hakan ba.

ALQST ya yi nazari kan mutum 35 da aka kora daga yankunan Jeddah. Cikinsu, babu wanda ya ce ya karɓi diyya ko kuma ya samu isasshen lokacin tashi bisa tsarin doka, kuma fiye da rabinsu sun ce an tilasta masu fita daga gidajensu cikin barazanar ɗauri.

Kanar Alenezi a yanzu yana zama a Birtaniya amma har yanzu yana fargabar tabbacin tsaronsa.

Ya ce wani jami'in asiri ya faɗa masa cewa za a yi masa tayin dala miliyan biyar idan ya halarci taro a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Landan tare da ministan cikin gida na Saudiyya. Ya yi watsi da gayyatar.

Mun yi wa gwamnatin Saudiyya tambaya kan wannan zargi amma ba su ce komai ba.

Hare-haren da ake kai wa masu sukar gwamnatin Saudiyya da ke zaune a ƙasashen waje ba wani abin tarihi ba ne - babban abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi, da wasu jami'an Saudiyya suka kashe a ofishin jakadancin ƙasar na Istanbul a 2018.

Wani rahoto abin allawadai ya yanke cewa Mohamed Bin Salman ya ba da umarnin kisan. Yarima mai jiran gadon ya musanta hannu a lamarin.

Sai dai Kanar Alenezi bai yi da-na-sani kan matakinsa na yin burus da umarni game da gina babban birnin na Saudiya ba.

"Mohamed Bin Salman ba zai bari wani abu ya hana gina Neom ba...Na fara damuwa game da abin da za a iya nema na yi wa mutanena."

Wanda ya bayar da gudummawa Erwan Rivault.