‘Karancin albashi ya sa wasu ma'aikatan asibiti na tsanar aikinsu’

    • Marubuci, Halima Umar Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Digital Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja

Wani ƙaramin ma’aikacin lafiya a Najeriya ya koka kan yadda rashin isasshen albashi ke karya gwiwar ma’aikata irinsa, na rashin son zuwa wajen aiki a wasu lokutan, duk kuwa da irin ɗimbin marasa lafiyan da ke buƙatar taimako.

Mutumin, ya aiko da labarinsa ne daga jihar Katsina a Najeriya, a cikin jerin labaran da BBC Hausa take samu daga ƴan ƙasar, bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023.

Ma’aikacin lafiyar wanda muka ɓoye cikakken sunansa saboda tsaro, ya ce a lokuta da dama “ina da sha'awar zuwa wurin aiki to amma babu yadda na iya sai dai na haƙura, saboda albashin ba ya isa cefane, balle har na rage na abin hawa,” kamar yadda Nura ya faɗa.

Ɓangaren lafiyar na cikin halin taɓarɓarewa a faɗin Najeriya musamman a shekarun baya-bayan nan, duk da irin yadda gwamnati ke shan alwashin inganta shi.

Matsalolin da suke jawo rushewar ɓangaren lafiyar kamar yadda ma’aikacin ya nuna, sun haɗa da ƙarancin albashi da sauran alawus-alawus da kuma rashin isassu da ingantattun kayan aiki.

Wannan lamari ya sanya ƙananan ma’aikata suke ɗaukar matakin ƙaurace wa zuwa aikin, su kuwa ƙwararrun likitoci barin ƙasar suke yi suna neman aiki a ƙasashen waje.

Wasu bayanai da jaridar Punch ta wallafa a watan Oktoban da ya gabata sun nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 30 ga watan Satumban 2022, kusan likitoci 1,307 ne suka bar ƙasar zuwa Birtaniya.

Hakan, kamar yadda masana suka bayyana, guduwar ƙwararru domin neman ingantacciyar rayuwa, ba ƙaramar illa za ta ci gaba da yi wa fannin lafiyar ƙasar ba.

Aikin wucin-gadi tsawon shekara 10

Nura ya yi karatunsa ne a Makarantar Koyon Fasahar Lafiya a jihar Katsina, inda ya samu satifiket na zama jami’in lafiyar muhalli a 2010.

Tun daga wancan lokacin aka ɗauke shi aiki na wucin-gadi a wata ƙaramar cibiyar lafiya, inda ake biyan shi naira 10,000 duk wata.

Ma’aikacin ya ce ainihin aikinsa na yin riga-kafi ne na cututtuka, amma daga baya saboda ƙarancin ƙwararru sai da ta kai yana haɗawa da sauran ayyuka da ƙwararrun ma’aikatan jinya ko likitoci ne ya kamata su yi.

“Saboda ƙarancin ma’aikata muna taimakawa ta wasu fannonin, kamar yin allura da ƙarin ruwa da duba marasa lafiya da bayar da magunguna,” in ji shi.

Sai dai ya koka da cewa duk da tsawon lokacin da suka ɗauka suna wannan aiki har yanzu ba a tabbatar da su a matsayin cikakkun ma’aikata ba sannan ba a taɓa ƙara masu albashi ba, a kan naira dubu goman da ake ba su.

“Tun shekarar 2012 aka ɗauke mu wannan aiki na wucin-gadi, mu da yawa, amma har yau ɗin nan babu wani sauyi. Kuma a hakan har aikin kwana muke yi tamkar cikakkun ma’aikata.”

Ma’aikacin yana aiki ne a ƙarƙashin gwamnatin jiha amma kuma a asusun ƙaramar hukuma ake biyan shi.

“A yanzu, da ni da ire-irena wannan dubu goman ko kashi 30 cikin 100 na cefanen gidana ba ta isa, kuma a haka hukumomin da muke wa aiki suke so mu ci gaba da gudanar da aiki yadda muka saba.

“Lokuta da dama ina da sha’awar zuwa wurin aiki to amma babu yadda na iya sai dai na haƙura saboda rashin abin da zan yi cefane har in rage na abin hawa,” ya faɗa cikin alhini. 

A baya ma’aikata irin su Nura masu wannan ƙorafi har zanga-zanga sun taɓa yi, amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba.

Ya koka kan yadda sai lokacin zaɓe ya zo sai ƴan siyasa su yi ta yi masu daɗin baki, a karɓi bayanansu da zimmar za a duba matsalarsu, “amma da zarar an kammala zaɓe sai a manta da mu,” ya faɗa.

Ana kukan targaɗe

Ba rashin isasshen albashi ga ma’aikata ne kawai matsalar fannin lafiya ba, akwai rashin isassu da kuma ingantattun kayan aiki.

Kamar yadda wannan ma’aikaci ya shaida wa BBC, sa’a ɗaya da aka ci ita ce ta yadda ƙungiyoyin ƙasashen waje masu zaman kansu ke yin matuƙar ƙoƙari wajen samar da kayan aiki da magunguna.

Dama a 2020 an bayyana tsarin kiwon lafiyar Najeriya a matsayin na 142 cikin kasashen duniya 195, a wurin inganci.

Idan aka waiwaya baya, a shekarar 2001, Najeriya tana daga cikin ƙasashen Afirka da ta yi alkawarin ƙara kuɗin da take warewa a fannin lafiya da kashi 15 cikin 100 na kasafin kuɗinta.

Amma shekara 21 ke nan ƙasar ta gaza cimma wannan ƙuduri. A shekarar 2012 ne kawai aka ware kashi 6 cikin 100.

Idan kuma aka duba yawan kuɗaɗen da ƙasashen Afirka ke kashewa a ɓangaren lafiya cikin jimillar kasafinsu, to Najeriya na can ƙasa a jerin, domin ita ce ta 38.

Sannan ya koka a kan yadda a yanzu matsalar rashin tsaron da ke addabar wasu jihohin ƙasar, ciki har da inda yake aiki, wato Katsina, take shafar su da saka masu tsoron zuwa wajen aiki.

“Musamman ma dai mu da muke asibitocin da ke yankunan karkara, inda da a can ne ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka wajen kai hare-haren da ke sa rayuwarmu cikin haɗari.

“Hakan ya sa da yawan ma’aikata irina ba sa zuwa wajen aiki akai-akai musamman ganin albashin bai taka kara ya karya ba ga shi ba mu da tabbacin tsaron rayukanmu da na marasa lafiyan.

“A yanzu haka asibitoci da yawa ma babu ma’aikatan domin haka ko marasa lafiya sun je ba lallai su samu kowa ba” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Ma’aikacin, wanda ya ce ya yi karatu ne domin taimakon al’ummarsa, a yanzu wannan yanayi yana karya masa gwiwa ƙwarai.

“Ba mu da zaɓi sai barin wannan fanni idan abu ya ci tura, duk da muna son taimakon al’umma.”