Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a riƙa cin tarar direbobin da ba su sanya kwandon shara a mota
Hukumar kula da muhalli ta Uganda ta ce za ta fara sanya tara ga direbobi daga watan Afrilu mai zuwa, ga duk wanda aka kama babu kwandon shara a motarsa.
Duk wanda aka kama za a ci tararsa kuɗin ƙasar shilling miliyan shida, kwatankwacin dalar Amurka $1,630, kamar yadda dokar da aka sanar ranar Laraba ta yi bayani.
Direbobin da suka ƙi biyan tarar za a gabatar da su gaban kotu ko kuma a tura su gidan yari, kuma kotu ce za ta faɗi yawan tarar, kamar yadda hukumar ta bayyana a sanarwarta.
A yanzu wajibi ne ga duk wata mota da ke ɗaukar fasinjoji su yi doguwar tafiya, ta sanya kwandon zuba shara a cikinta.
Amma faɗaɗa dokar da aka yi kan masu amfani da motocinsu na kansu ya janyo hayaniya a Uganda, yayin da wasu da yawa ke tambaya kan wane irin kwando za a yi amfani da shi.
"Matuƙar kana amfani da abin da ba zai iya riƙe dattin da ka ke amfani da shi ba a mota, to lallai za a ci tararka. Ba a yarda a yi amfani da ledoji ba a motar," in ji kakakin hukumar Naomi Karekaho.
Ta ce hukumar za ta bayyana me take nufi da abin zuba sharar idan za ta faɗi sauye-sauyenta a nan gaba.
"A duka dokokin da muka bayyana na kiyaye muhammli wannanta fi tsaya wa mutane a rai. Wataƙila saboda an ce mutane su sa kwandon shara a mota," ya ƙara da cewa.